← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 37

Sashe 5

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdulillah" ya faɗa a nutse lokaci ɗaya yana karɓar hannayen masu miƙo masa suna gaisawa cikin mutunci. Be daɗe a soron ba ya miƙe zuwa ɗakinsa da ana shiga tsakar gidan yake. Kai tsaye toilet ɗin da ke cikin ɗakin ya faɗa yayi wanka, ya ɗauki wajen minti 20 sannan ya fito ya sake shiryawa cikin manyan kaya, sosai kyawunsa ya sake fitowa musamman da ruwan da be gama bushewa ba na jikinsa ya sake kwantar da kwantaccen sajen da ke zagaye akan kyakkyawar fuskarsa, ɗaya daga cikin abin da ke sake ƙawata fuskarsa kenan. Se da ya gama shiryawar sannan ya koma ya zauna akan madaidaicin gadonsa ya ɗauki littafan da ya shigo da su ya shiga dubawa yana ware waɗanda ze fara yiwa ajinsu Twins wanda yanzu su ne babban aji. Sallamar Ummeey cikin ɗakin nasa ne ya sanya shi ɗaga manyan idanunsa ya kalli bakin ƙofar. Murmushin da ban taɓa gani akan fuskarsa ba ya wanzu, se a lokacin na sake fahimtar lallai murmushi ma wani abun ne, dan kuwa wani shahararren kyau Gwanin ya ƙara yi, kai ba zaka taɓa ɗauka shi ne a waje ba a yanzu da yayi wannan murmushin.

"Sannu da zuwa Ummeey" ya faɗa yana miƙewa daga inda yake.

"Yawwah sannu ka dae Affan.. Ka ci abinci?" Ta haɗe tayi maganar lokaci ɗaya. Girgiza kai yayi yace

"A'ah Ummeey zan dai ci tukunna" Itama girgiza kan tayi dama ta san halin Affan ɗin, shi ba damuwarsa ba ce ya yini be ci abinci ba, se dai idan ita ta tilasta shi, hakan ne ya sa idan dai ta fita unguwa toh tana dawowa zancen abincin take fara masa dan ta san da wuya idan ya ci.

"Ajiye littafan nan, yanzu zan kawo maka." Bata jira yace komai ba ta wuce Kitchen. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, a ransa yana sake godewa Allah da irin wannan uwa da ya ba shi, dan haka se ya koma kawai ya zauna har Ummeeyn ta dawo hannunta ɗauke da abincin ta ajje masa. Babu musu ya ɗauka ya soma ci ko dan faranta ran Ummeeyn. Se ma ta zauna tana masa fifita shi kuma yana cin abincin.

... A harabar gidan driver ɗin da ya saba kaisu makaranta ya saukesu. Dukkansu suna sanye ne cikin Uniform na makarantar boko me kyau, kalarsa nutsatstsiya ce sam babu hayaniya, ga kuma yanayin yadda ɗinkin da aka musu yake me kyau, wanda aka yi shi cike da ƙwarewa. A gajiye dukaninsu suka shige cikin ɗakin nasu da sallama, yayin da Little ya faɗa ɗakin a guje yana kiran Ammi. Ammi da fitowarta daga kitchen kenan ta amsa sallamar tasu lokaci ɗaya tana riƙe Little da ya rungumeta.

"Ammi mun dawo." Ya faɗa bayan shi ma ya rungume Ammin.

"Sannunku da dawowa yaran kirki" tayi maganar tana ɗago shi suka ƙaraso zuwa cikin parlourn. A tare Twins suka zube akan kujera sannan kusan a tare suka ce

"Washh!" Se da Ammi ta zauna sannan tace

"Da alama kun gaji?" Yamutsa fuska Didi tayi tace

"Wallahi kuwa Ammi"

"Toh maza ku tashi ku watsa ruwa, ku zo ku samu ku ci abinci." Ta ƙarasa maganar tana kallan malalaciya Lulu da har ta kwanta akan kujerar ɗakin. Se dai da yake ta ji maganar Ammin ya sanyata miƙewa ta bi bayan Didi suka wuce ɗakinsu.

.. Parlour ne madaidaci wanda adon da aka masa ya dace da zubinsa, ya matuƙar ƙawatu da kayan da ke cikinsa. Daga kan kujera wata matashiyar budurwa ce da aƙalla za ta yi 20years, zaune cikin riga da wando wanda ta ɗaga shi zuwa ƙasan gwuiwarta. Hannunta ɗauke da waya tana dannawa yayin da kunnenta ke saƙale da bluetooth, da alama waƙa take ji dan kuwa lokaci lokaci ta kan tsaya ta ɗan jinjina kanta sannan ta cigaba da danna wayar. Ba wata kyakkyawa bace se dai ba za a kira ta da mummuna ba, dan kuwa tana da kyawunta daidai misali. Kanta babu ɗan kwali se zallar gashinta da ba shi da wani yawa da ta ƙulle shi a saman kanta.

"Jadwa!" Maganar da naji daga gefe itace ta sanyani juyawa dan ganin wadda tayi ta. Babbar mace ce wadda aƙalla ta bawa 40 baya, ko kuma 40 ɗin ciff, se dai idan har kace daga yanayin shigarta zaka faɗi shekarunta toh se dai ka ce ba tafi ashirin da wani abu ba. Dan kuwa wani riga da wando falazo ne a jikinta, yayin da ta saka wata hula a kanta wadda ta zameta har wajen rabin kanta a waje yake. Hannunta ɗauke da waya ta ƙaraso cikin ɗakin ta saka hannu ta cire bluetooth ɗin kunnen Jadwa guda ɗaya. Se ta juyo da sauri, ganin Maminta ne ya sanya ta faɗin

"Ohh Mami! Kin saka nayi loosing." Ta faɗa tana yamutsa fuska. Neman waje Mamin tayi tana faɗin

"Kin ƙure uban volume, idan kin gama ji se ki tashi ki yi sallah." Se da ta sake yamutsa fuska kafin tace

"Tohm" ta cigaba da danna wayarta. Se kuma ta juyo ta kalli Mamin da take danna waya tana ɗan tauna chewing gum ɗin da ke bakinta.

"Mami wa za ki kira ne haka?"

"Ammin twins!" Se ta juyo sosai tace

"Mami me ya faru?" Ta faɗa daidai lokacin da Mamin ta kai wayar kunnenta sannan ta amsa mata da

"Ki jira ki ji!" Babu musu kuwa ta gyara zama tana kallan Mamin. A ɗaya ɓangaren kuwa Ammi na zaune kan kujera, Didi na kusa da ita tana koyawa Little home_work. Wayar Ammin da tayi ƙara ne ya sanya Lulu da tafi kusa da ita ɗauka ta miƙawa Ammin ba tare da ta kalli me kiran ba. Karɓa Ammi tayi ta ɗaga wayar, suka gaisa da Mamin sannan ta ɗora da

"Ina Twins su ke?" Murmushi Ammi tayi kana ta amsa da

"Ga su a kusa da ni" Kamar Mamin na kusa da Ammi tace

"Na san wannan maƙalalliyar uwar miskilanci tafi kowa kusa da ke a yanzu haka" Kamar kuwa ta sani hakan ne, kuma da yake sun ji abin da ta faɗa ɗin se Didi ta ɗora kanta akan kafaɗar Ammi tana tura baki da murmushi akan fuskarta. Hannu Ammi ta saka ta shafa kan Didi sannan tace

"Aikam dai.."

"Ina Lulu?" Ta sake tambaya. Da sauri Lulu ta taso daga inda take dan dama babu ƙarya suna ɗasawa da Auntynta su. Karɓar wayar tayi daga hannun Ammi suka gaisa sannan Mami ta ɗora da

"Yaushe zaki zo?" Kallan Ammi tayi sannan tace

"Idan an yi hutu!"

"A'ah babu wani hutu, ki zo kawai tunda idan kika zo ɗin zaki dinga zuwa makarantar anan ɗin ma, Uhmm?"

"Toh Mami" Daga haka ta miƙawa Ammi wayar, suka sake magana sannan suka yi sallama. Abba da ya shigo kafin su yi sallama yace

"Sadiya ce?"

"Ehh.." Kafin Ammin ta gama faɗar abin da tayi niyya Lulu tace

"Abba zan je gidan Mami pls.." se da ya nemi waye ya zauna yana riƙe da hannun Little sannan yace

"Makarantar fa?"

"Abba ai za a dinga kaini a can ɗin ma" Kallan Ammi Abba yayi dan jin abin da zata faɗa, se dai ba tace komai ba hakan ne ya sanya shi faɗin

"Ita ce ta nemi ki je ne?" Ɗan shagwaɓe fuskarta tayi sannan tace

"Ehh Abba"

"Ki shirya, gobe idan Allah ya kai mu se na saukeki acan ɗin." Cikin jin daɗi tace

"Toh Abba." Ta faɗa a ranta tana tuna yanayin rayuwar gidan Aunty Sadiyan, da take babu takura, komai ka ga damar yi daidai ne, ta san idan ta je can ɗin babu me tilasta mata yin abin da bata ga dama ba, hatta da karatun ma idan bata yi niyyar yi ba ta san Mamin ba zata takura ta da se tayi ba, shi yasa take matuƙar ƙaunar rayuwar gidan Mamin. Kallan Didi tayi da har lokacin kanta ke ɗore akan cinyar Ammi tace

"Didi wankin kan."

"Ba za a yi ba" Didi ta faɗa tana galla mata harara. Rau rau tayi da idanunta tana kallan Didin, ta san ko me zata yi Didin ba zata bi ta su tafi tare ba, dan ita ɗin miskila ce irin ta sosai ɗin nan, ba kasafai ta fiya son shiga cikin mutane ba idan ba dole ba, shi yasa kullum tana gida kusa da Amminta. Se dai kuma ta wani ɓangaren zata ɗan ji daɗi, dan kuwa idan har Didin ta bi ta suka tafi gidan Aunty Sadiyan tare, zata zame mata cikas, ta san ita ɗin me sakata tayi ne. Ɗan sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ba dan ta so zuwan Lulu gidan Aunty Sadiya ba, se dai komai lalacewar Aunty Sadiyan ita ɗin ƙanwar Abbansu ce, saboda haka ba zata iya kallansa tace masa Lulun ba zata je gidanta ba saboda yanayin tarbiyyarta sam be dace ba. Se dai koma me ake ciki ba zata bari Lulun ta wuce sati ɗaya bata dawo gida ba, dan haka kawai take ji hankalinta be kwanta ba tun da akayi maganar zuwan Lulu gidan nata..

Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.

https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_04

___Ba su daɗe a parlourn ba Didi ta miƙe tana kallan Ammi tace

"Ammi bari na je na kwanta, bacci nake ji." Kallanta Ammin tayi na tsawon sakanni kafin tace

"Tohm" Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta wuce ɗakin nasu. Da narkakkiyar fuskarta Lulu ta bita da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Ammi.

"Ammi haushina fa take ji." Ta faɗa tana tura baki. Girgiza kai Ammi tayi kana tace

"Ai dai kin san halinta dama." Tasowa Lulu tayi daga kan kujerar da take, ta dawo wadda Ammin ke kai. Ta kamo hannunta har lokacin fuskarta a narke tace
Chapter 5 · 0% Book details