← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 37

Sashe 11

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Magana ce a kan er uwar Afrah Muhammad Aji, na koreta daga ajina!" Numfashi Malam Ahmad ya sauke yana tuna Afaaf ɗin, tabbas ya san yarinyar ba ta ji, amma be taɓa tunanin har zata iya yiwa Gwani wani abun da ze sa har ya koreta ba. Ya riga ya san Gwanin ba ze yanke hukunci babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba, dan haka tambayarsa dalilin yin hakan ma kamar ba shi da wani amfani, dan haka yace

"Kayi haƙuri Malam Affan, kayi haƙuri. Wallahi ka san yarinyar muna fama da ita, ba dan ma muna da tsayayyun malamai ba. Duk da yarinya ce amma gani take kamar kanta ɗaya da kowa, amma In Sha Allah zamu san yanda za a yi a yiwa tufkar hanci." Furzar da iska Gwani yayi lokaci ɗaya yan ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗesu yace

"Ka yi haƙuri Malam Ahmad, amma se dai ko ni na zauna a ajin, ko kuma ita ta zauna ni na bar ajin.." Wajen second 30 Malam Ahmad ya soma faɗin

"Da ka duba al'amarin nan Malam Affan, ka yi haƙuri, ba wai dan ina sama da kai a cikin makarantar nan ba ne, dan ka san idan Addini ne kai ɗin number ɗaya ne. Ba komai ne ya sa nace kayi haƙuri ba se dan kai ɗin na daban ne, kai ɗin me iya zama da ɗalibai ne masu kowanne irin hali sannan ka chanja su cikin ƙanƙanin lokaci. Zaka iya zama da wannan ɗalibar Malam Affan, kamar kuma yadda nake fata ta chanja, ta koma kamar er uwatta. Se dai a wannan karon ba ze yiwu a barta haka ba, zata iya kasancewa mahaifinsu be san abin da take aikatawa ba, saboda mahaifinsu mutumin kirki ne na sosai. Dan haka zan saka a sanar da shi muna son ganinsa, idan ya so se ku yi magana da shi." A wannan karon shiru Gwani yayi sanda ya gama saurarar maganar Malam Ahmad ɗin sannan ya gyara zamansa a kan kujerar da yake kai..

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_07

"Shi kenan!" Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana miƙewa, ya miƙawa Malam Ahmad hannu suka sake gaisawa sannan ya fice daga Office ɗin.

A tare suka fito daga cikin makarantar, se dai Didi ba tace da Lulu ko uffan ba, wanda hakan ke alamta mata fushi take da ita. Ita kuma a yanda take jin zuciyarta dama yanzun ba za ta iya cewa komai ba. Idan kuwa tayi ƙoƙarin furta ko da kalma ɗaya ce to kuka ne ze ƙwace mata, and idan hakn ta kasance kuma ba zata taɓa yafewa kanta ba, hakan ne ya sanyata sake haɗe fuska waje ɗaya tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta riƙe kanta kukan be taho ba dan kada ta yarfa kanta.

"Se da safe." Didi ta faɗa ba tare da ta kalleta ba, daga haka tayi gaba hannunta riƙe da na Little. Binta da kallo Lulu tayi, mamakin yadda tayi fushin na sake kamata, bata taɓa tunanin akan Gwani Didin kan iya fushi da ita ba. Da dai ta ga alamar da gaske Didin take ta tafi kenan, se ta soma jan ƙafafunta kafin ma en ajin na su su gama fitowa tayi inda motar da zata ɗauketa ke tsaye. Daidai lokacin ya ɗago kai cike da sarewa, dan a yanzu kam be taɓa tunanin ze iya ganinta ba, ya gama fidda rai, bayan daɗewar da yayi a wajen ta sama da awanni. Se dai me? Yana ɗaga kai ya hangi Lulu na neman shiga motar. Cikin matuƙar farin ciki ya furta

"Alhamdulillah!" Yana tayar da motarsa. Babu daɗewa driver ya ja motar da Lulu ke ciki ya soma tafiya, cikin ƙwarewa shi ma ya soma binsa har zuwa sanda suka isa gidan Mami. A bakin gate ɗin ya tsaya yana kallan gidan, ba dan akwai abin da ze yi yanzu ba, da tun yanzun ze fara zuwa wajen nata, se dai kuma ance gaggawa aikin sheɗan ne, dan haka gwara ya bari zuwa goben se ya zo. Hakan ne ya sanya shi tashin motarsa ya bar layin cike da farin cikin samun gidansu Lulun. Ko jakarta Lulu bata iya ɗauka ba ta fice daga motar da gudu.

"Subhanallahi, daughter me ya faru?" Mami ta faɗa tana miƙewa tsaye, babu ɓata lokaci Lulu ta ƙaraso ta faɗa jikin Mami tana fashewa da kuka.

"Na shiga uku ni Sadiya, Lulu me aka miki ne? Waye ya taɓa min ke?" Se da tayi me isarta sannan ta buɗe baki ta soma korawa Mamin abin da ya faru tana jin kwata kwata babu daɗi.

"A gaban en ajin ya yagaki haka? Shi be san wacece ke ba? Be san kin fi ƙarfinsa ba shi ne ze miki haka? Toh makaranta ce kin dena zuwa daga yau, zan yi magana da Yayan." Mami ta faɗa a kufule. Cikin jin dadi Lulu tayi murmushi kafin tace

"Ko Mamina?"

"Ƙwarai kuwa ɗiyar albarka, ai kin fi ƙarfin wulaƙancin kowanne ɗa namiji ballantana kuma malamin islamiyya. Kada ki damu daga yau kin dena zuwa makarantar nan." Miƙewa tayi duk da yanda take jin zuciyarta na zafi amma sosai taji dama_dama da maganganun Mamin, ko babu komai sun sanyaya mata zuciya, hakan ne ya sanya ta wuce ɗaki.

.. Ko sallamar da yayi a ciki_ciki yayi ta, Ammi da ke zaune kan kujera ta amsa sallamar tana kallansa. Se ta miƙe tana faɗin

"Sannu da zuwa"

"Yawwah, maza ɗauko min takaddun nan zan fita ne."

"Ikon Allah, sake fita kuma zaka yi?" Ammi ta tambaya, se dai ganin yanayinsa kamar a ɗan fushi ya sanyata faɗin

"Allah dai yasa lafiya!" Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace

"Ni dama na san kiran nan da aka min a makarantarsu yaran nan akwai wani abun, dan kuwa basu taɓa yi min haka ba. Ashe ban sani ba kara suke min, suna ta ɗaga min ƙafa ban sani ba. Ashe yarinyar nan tana can tana ƙoƙarin zubar min da mutunci da kimata wajen malamanta, bata duba girmansu, darajarsu da kuma kimarsu, tana yin abu kamar bamu bata tarbiyya ba?" Abba ya ƙare cikin fushi kamar Lulun na gabansa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!" Shi ne abin da Ammi ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna. Se dai kafin ta gama tunanin ballantana ta kai ga cewa komai ta jiyo muryar Abban na faɗin

"Zuwa zan yi na ɗakkota, ta dawo ta cigaba da zama a gidan nan, a gabana ina kallan abin da take yi hankalina ze fi kwanciya. Sannan kuma tun a can ɗin wallahi zan hukuntata tun da bata da kirki." Se a lokacin Ammi ta miƙe tana girgiza kai tace

"A'ah Abba kayi haƙuri don Allah, kome zaka yi mata ka bari ku dawo gida tukunna, sannan ka ɗan sassauta fushin nan naka kafin ka fita, ka san fushin ba shi da wani alfanu.." Sauke ajiyar zuciya Abba yayi yana faɗin

"In Sha Allah.."

A ɗaya ɓangaren kuwa su ukun ne zaune a parlour suna kallo a ƙatuwar TVn da ta ƙawata parlourn. Jadwa da ke zaune kujera ɗaya da Lulu ta juya ta kalli Mami sannan tace

"Mami wae yaushe Abbu ze dawo?"

"Baki na fiki koh?" Mamin ta faɗa tana jefa mata harara. Kafin Jadwan ta kai ga cewa komai se ga sallama daga bakin parlourn. Jin sallamar me gadinsu ne ya sanya Mami faɗin

"Shigo!" Duk kuwa da irin shigar da ke jikinsu hakan be sanyasu tashi sun ɗauki ko da mayafi ne sun rufe jikinsu ba ko dan kasancewarsa ba muharraminsu ba. Babu daɗewa kuwa se ga shi ya shigo cikin ɗakin. Ya durƙusa har ƙasa yana faɗin

"Hajiyoyi barkanku da wannan lokaci.."

"Barka dai" Jadwa da Mami suka amsa da hakan, yayin da Lulu hankalinta gaba ɗaya ke kan TV saboda ana haska wani favourite movie nata ne.

"Me ya faru?" Mami ta katse shi da faɗin hakan.

"Kun yi baƙo ne, yana ƙofar gida, yace yana buƙatar ganin wata daga cikin gidan nan, nafi tunanin irin baƙin nan naki ne hajjaju, shi yasa nace bari na zo na faɗa miki!"

"Yana tsaye a bakin gate kuma?" Mami ta faɗa tana kallansa. Se ya girgiza kai yace

"A'ah da yake a mota yake, toh har yanzun ma yana ciki.."

"Ohk, ka faɗa masa ya shigo, ka kai shi ɗakin baƙi, gani nan zuwa." Mami ta faɗa tana miƙewa. Babu musu ya miƙe yana faɗin

"Toh Hajiya." Ɗaki Mami shiga, babu daɗewa ta fito, kai tsaye ta wuce ɗakin baƙi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, hannunta ɗauke da wayarta, ba yau ne karon farko dama da take karɓar baƙi kala_kala ba, musamman akan aikinta, se dai yau ɗin bata san da zuwan wannan ɗin ba, abin da ya bata mamaki kenan. Sanye yake cikin shadda, ɗinkin babbar riga kamar ranar farko, yau ɗin ma sun amshe shi babu laifi, yana kame a cikin kujera. Amsa sallamar yayi sannan ya juyo yana kallan me shigowar. Kusan a tare suka faɗi sunan junansu kowannensu cike da mamakin ganin ɗan uwansa.

"Kaseem!" Mami ta sake faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.

"Kai ne a gidan nawa?" Ta tambaya tana neman waje ta zauna a kan kujera. Duk da yayi mamakin ganinta a gidan hakan be hana shi faɗin

"Wallahi kuwa ni ne Madam."

"Ikon Allah, toh ya kake? Ya aiki?" Ta tambaya. Nan dai suka gaisa cike da sabo sannan Mami tace bayan shuɗewar wasu sakanni ba tare da kowa yace komai ba

"Anya kuwa gaisawa da ni ka zo yi?" Murmushi Kaseem yayi yana ɗan gyaran murya sannan yace

"Madam ina ganin fa da alama kina dab da zama sirikata.." buɗe ido Mami tayi kafin tace

"Woww, da gaske?" Se da ya jinjina kai sannan yace yana murmushi

"Ƙwarae kuwa, dan kuwa a jiyan nan na ga ɗiyarki, na kuma ga nan gidan ta shigo, hakan ne ya sanyani biyo sawu." Cikin matuƙar farin ciki Mamin tace
Chapter 11 · 0% Book details