← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana cikin wannan halin ne wayarsa ta koma daukar ruri. Ya dagota yana kallon sunan mai kiran. A take 'yan hanjin cikinsa suka kada. Gumin da yake yi ya ninku. Ya tattara yawun bakinsa dakyar ya yi musu wata hadiya, ji kake "mukut". Tamkar wanda aka shaki wuyansa kafin ya hadiyi yawun. Ya shafi fuskarsa da tafin hannunsa sannan ya koma bude ido ya kalli sunan mai kiran dan tabbatarwa. Shakka babu Asp Sauwam ne mai kiran. Hannunsa ya shiga kyarma ya kasa daga wayar har ta yanke. Ba jimawa kiran ya sake shigowa, bai san ya aka yi ya dauki kiran ba. Sai kawai ya ji muryar Asp yana kiran sunansa ba ko sallama. "Shugaba kana ji na kuwa?". Da ace da wani a dakin to babu abinda zai hana shi jin kukan 'yan cikin Shugaba...

*Ku yi hakuri da wannan, na san ya yi kadan. Ina cikin uzuri ne shi yasa.*

Insha Allah gobe zan ci gaba. Kuma in muku da yawa 😜

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Domin ki kawa ta gari ASIYA ISAH (MAMAN NANA FIDDAUSI) Ubangiji ya raya mana baby rayuwa mai albarka. Sannan ya kara dankon so da kauna da Oga.*

```page 11```

Sannu a hankali yake tukin kamar wanda baya son tafiya. Duk da akwai tsaro sosai a lunguna da sakon garin hakan, hakan bai kawo musu cikas a tafiyar tasu ba. Har Allah yasa suka isa GRA. layi na uku, gida mai lamba ashirin da biyu. Dai-dai nan suka tsayar da motar suka fito. Gabansu gadi duka nufi gate din gidan kamar masu gida.

Da sauri ta jiyo ta kifta masa ido, alamar ya koma mota. Bai tsaya komai ba ya juya zuwa mazauninsa. Da zuwa ta kwan-kwasa gate din gidan bayan ta cire hular kanta ta baje gashin a gadon bayanta da gefe-gefen fuskarta. Ta gyara tsayuwa. Shiru ba amsa, sai da ta koma kwan-kwasawa a karo na biyu sannan tsumakakken buzun ya taso yana tambayar "wane ne a cikin daren nan?". Karamar kofar ya bude yana haska ta da fitila. Cikin gurbatacciyar hausarsa yake tambayarta "waye ne kai?". Ta sakar masa murmushi "sannu Audu. Ni ce Bintu kawar Shakira. Wani fati na zo dare ya yi min kusan nan, shi ne nace bari kawai in zo in kwana a nan."

Ya kara gyara tsayuwa yana nazarinta. Da ganin yanayin shigarta dai ya san duk sune da masu gidan. Sai dai yanayin tsaro sam ba a bashi damar barin wani ko wata ya shigo gidan bayan mazaunanshi ba. Yace "aa kayi hankuri, wallahi bai bari wani siga". Ta bata fuska "haba Abdu kar ka min haka mana, yanzu in ka hana ni ina zan je in kwana kenan?". Duk ya tabbatar ta san su tunda har sunansa take fadi. Amma fir ya hana ta shiga, saboda tsoro da gudun ya rasa aikinsa kamar yadda aka gindaya masa sharadin.

"Kai hankuri yarinya. Wallahi ba laifinmu, laifin masu gida ne". Ya ja baya yana shirin rufo kofar. Ganin zai bata musu aiki, Fadwa ta yi wuf ta shako wuyansa. Kafin ya yi wani yunkurin tuni ta rufe bakinsa da naushi, hade da hular nan tata. Hakan ne ya hana shi yin ihu duk kuwa da cewa ya ji zafin dukan. Ta kai shi gefe ta zaro wata siririyar igiya ta daure hannayensa ta baya ta koma kai masa wani naushin a fuska, wanda ya yi sanadin dakatawar numfashinsa. (Ya suma) ta jefar da shi gefe ta budewa Ab'ha gate din ya shigo da motar ya fito, suka nufi cikin gidan a tare.

Daya bayan daya suka fara bude kofofin da suka tarar suna shiga kafin daga bisani suka tsinci kansu a cikin gidan. Gida mai tarin dakuna da kofofi, dole suka shiga bin dakunan daya bayan daya. Duk inda suka shiga sai sun ci karo da 'yan mata uku ko hudu a gado daya suna sharar bacci. A ko wane daki Ab'ha ne yake fesa musu wani sinadarin saka bacci mai nauyi, sai su buge. Su kuma su ja su ratai-ratai su kai su mota. Haka suka dinga yi har Allah ya basu iko suka kwashe duka matan dake gidan-nan su goma sha bakwai.

Sannan suka tayar da motar suka tafi. A hanyar su ta komawa kam kamar an share babu kowa a kan titunan, kasancewar dare ya kara tsalawa.

Cikin sa'a da nasara suka isa gida, nan ma daya bayan daya suka jido su zuwa cikin babban dakin dake gidan, wanda ba komai a cikinsa sai Capet. Kamar matattu haka suka jere su, sai baccinsu suke a natse, sannan suka fice suka rufe dakin da kye. Ko-wannensu ya nufi dakinsa fuskokinsu dauke da farin cikin samun nasara.

Washe gari da safe, kamar ko wane lokaci haka ta fito ta shirya musu abin karyawa, Ab'ha bai tashi da wuri ba, saboda rashin sabo. Bayan sun kammala karin ne suka fara sabon shiri yadda zasu sato ragowar matan da suke a daya gidansa dake Maagana. Kamar dai wan-can haka shima suka tsara yadda aikin zai tafi.

Sannan ko-wannensu ya mike suka koma dakunansu dan kara samun hutu.

*02:30pm*
Labari ya gama baje ko-ina cewa "a daren jiya an sace wasu mata masu zaman kansu guda goma sha bakwai a cikin garin Kano". Tashin hankali! Lokacin da wannan mummunan labarin ya riski Shugaba, sam kasa tsayuwa da kafafunsa ya yi. Al'amarin da ya tashin hankalin uwargidansa Hajiya Laurat da yaranta duk da basu san takamai-man dalilin hakan ba. Kawai dai suna kallon labarun rana a tashar BBC ne suka ga ya fara kyarma daga tsaye yana neman faduwa.

Nan da nan su Baffa suka kinkime shi suka kai shi dakinsa, da hanzari aka kira likitansa Dr. Yakub. Ba jimawa ya bayyana a gidan, ya kuwa dukufa wajen ganin ya shawo kan matsalar domin Shugaba abu sai sama yake yi. Jiki na karkarwa. Likitan ya samu nasarar samo dai-daituwar numfashinsa. Sai dai yana cikin mawuyacin hali kamar yadda yace. Ya korawa iyalan nashi jawabin musabbabin ciwon na shi wato, damuwa. Domin kuwa jininsa ne ya hau. Irin mummunan hawan nan da ba a cika so ba. Wanda yake yi a lokaci daya. Ya kare da cewa "a irin haka ne in ba sa'a ba sai kuga mutum ya kamu da mutuwar barin jiki farat daya."

Hankulan yaran da matarsa suka kara tashi. Auta Anisa sai kuka take. Likitan yace "ba kuka zaku yi ba addu'ar samun sauki zaku yi masa. Insha Allah nan da dan wani lokaci zai tashi." Ya bukaci daya daga cikinsu ya biyo shi asibiti ya karbowa Alh. Magani. Auta ta mike tana share hawaye. Faisal yace "ki zauna kanwata barin je in karbo". Ta girgiza masa kai alamar aa ita zata je. Baffa ya share mata ragowar hawayen yace "to ku je". Likita ya fice ta rufa masa baya. Sauran kuwa sun kasa fita dakin uban na su. Sun yi cirko-cirko suna kallon yanayin fitar numfashinsa domin ya dan jima da yin bacci.

A asibitin Mai jama'a private hospital. Likita ya faka motarsa ya fito. Anisa ma ta faka tata ta fito ta bi bayansa zuwa ofishinsa. Jikinta kana-nan kaya ne riga da wando. Pink in colour. Rigar iya guiwa wandon kuma pencil ne sai siririn mayafin dake sakale a kafadarta, kamar ba 'yar musulmi ba. Likita ya tura aka kawo masa maganin ya bata tare da addu'ar Allah ya bawa mahaifinta lafiya. Ta amsa da "amin". Ta fita.

Ta shiga motarta ta tayar ta kama hanyar komawa gida. Ta dan yi nisa sosai har ta sauka daga babban titi, ta kama kebabbiyar hanyar unguwarsu. Sai ta ji muryar mutum a motar yana cewa "ki tsayar da motar nan". A razane ta taka birki a tsakiyar hanyar ko gefe bata iya sauka ba saboda tsorata da ta yi. An gode Allah hanyar ba ababen hawa. Ta juyo da sauri dan ganin mai magana a bayan motarta. Juyowarta ke da wuya aka fesa mata wani abu a fuska, daga nan kuma bata koma gane komai ba.

Wanda ya yi mata hakan din ya gaggauta fitowa daga baya ya zauna a mazaunin direba ita kuma ya tura ta a bari daya. Ya tashi motar ya yi ribas ya fice daga unguwar.

Ab'ha kenan. Tun shigowarta asibitin ya ci karo ita, a lokacin shi kuma ya zo siyen sinadarin nan mai saka nannauyan bacci da suke amfani da shi ne a asibitin. Ganin haka yasa ya siyi abin da gaggawa ya fito ya yi wa kansa masauki a motarta, kasancewar hankalinta a tashe bata tsaya kulle motar ba.

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

```page 12```

*Gidan Shugaba*
Abu wasa-wasa har dare babu Anisa babu labarinta. 'Yan uwa sai kiran wayarta suke bata tafiya. Hankula sun tashi saboda an kira lokita ya kuma tabbatar musu da cewa tun da suka je ya sallame ta ta tafi. Zuwa lokacin Shugaba ya farka amma babu kwarin jiki. Uwar ce ta gargadi yaran da kar su sanar da shi halin da ake ciki na batan'yarsa saboda ganin halin da yake ciki.

Hakan kuwa aka yi. Can tsakaninsu suke ta bulayin bin gidaje na 'yan uwa da abokaninta har karfe dayan dare ba wani labari mai kama da samunta. Sai suka juya akalar neman zuwa asibitoci da police station. Nan ma shiru a ranar Momy Baffa da Faisal ba wanda ya iya rumtsawa. Gaba daya layukanta a kashe sai kuna suke.
Chapter 7 · 0% Book details