Sashe 18
Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna cikin wadannan bayanan ne suka jiyo wurin ya kaure da karar jiniya ta motocin jami'an tsaro. Nan da nan mutanen suka fara darewa da kansu suna bada hanya ga jerin gwanon motocin suna wucewa. A filin suka yi farking sannan suka fara dirowa kamar tsinukka suna bin sahu, ko-wannensu dauke da zungureriyar bindiga da hular kwano. Fuskokin nan nasu babu ko annuri. Haka suka yi leshi suka zagaye motar da Alhaji Habib yake cikinta. Acp Sauwam ne a kan gaba cikin gagarumar shiga irinta ma'aikacin da ya shiryawa fita filin daga. Da gudu wani dan sandan ciki ya zo ya bude masa kofar. Cikin mutumcin nan nashi da nuna kamala ya fito daga motar fuskarsa dauke da murmushi. Nan da nan jama'ar dake wajen suka dauki ihu da sowa suna daga mishi hannayensu alamar suna bayansa. Da murmushin nan yake daga musu hannu yana jinjina kai. 'Yan jarudu ko suka yo masa caaa! Da tambayoyi. Ji kake suna "Ranka ya dade me zaka ce game da wannan zargin da ake maka? Dan Allah Alhaji kace wani abu mana. Mutane suna son ji daga gareka". Kowa da irin tambayar da yake jefa masa, sai dai tuni jami'an tsaro suka killace shi ta hanyar saka shi tsakiya suka zagayeshi. Wasu a gaba wasu a baya suna ture mutane suna buda hanya. Bai amsa tambaya ko daya ba har suka shigar da shi cikin kotun. A can ma basu daga suka barshi ba, layi daya aka ware duk na masu bashi tsaro ne, kujerarsa na tsakiya.
Basu jima da shiga ba aka sanar da isowar alkali. Mutane kam ko rabi basu sami shiga ba kotun ta cika. Ganin hayaniyar na wajen ta yi yawa yasa aka yi gaggawar samun mafita ta hanyar jona camera da babban majigi dake make a gaban kotun ta waje, yadda duk wanda yake waje zai iya ganin komai da ake gabatarwa a ciki. Sai da aka tabbatar kotu ta sami nutsuwa sannan aka bude karamar kofar, bayan kowa ya mike tsaye ne alkali ya fito ya zauna a mazauninsa. Sannan kowa ya koma ya zauna. Saida aka fara da gabatar da karar sannan aka gabatar da masu laifin su biyu. Shiru kotun ta yi a lokacin da kan alkalin yake kasa yana gabatar da 'yan rubuce-rubuce a kan wata farar takarda. Sai da ya kammala rubutun sannan ya dago ya bukaci lauyoyin dake dakin su gabatar da kansu. Daya bayan daya lauyoyin Alhaji Habib guda biyar suka gabatar da kansu, sannan daga bisani barrister Bashir Bayo. Ya mike ya gabatar da kansa a matsayin lauya mai kare masu laifin. Al'amarin da ya bawa kowa dake wajen mamaki musamman masu laifin da basu san sun dauka ko wani ya daukar musu lauya ba. Amma saboda jin yace zai kare su ya saka basu musa ba suka yi shiru. Ragowar lauyoyin Alhaji Habib kuwa tuni suka fara kus-kus-kus domin duka sun san Barrister BB kamar yadda ake gaya masa. Lauya ne mai kafiya da dagewa kan abinda yasa gaba. Baya shakka ko tsoron case ko na waye, domin shi din lauya ne mai zaman kansa kuma korarre. Wanda zai iya fafatawa da kowane lauya a fadin duniya. Bayan gajeren rubutun da alkalin ya yi kan bayanan gabatar da kai na lauyoyi ya dago ya fara da tambayar masu laifi a kan waccan maganar da suka fada a zama na farko.
"Kuka ce saka ku aka yi ku kashe mai laifi Fadwa ko?". Dukkansu suka amsa da "eh". "Wa ya saka ku?". Kai tsaye suka kara mai-maita abinda suka fada a baya. "Alhaji Habib Shugaba". Shugaba da yake gogagge ne ya zuba musu ido, yana kada kai cike da alamar mamaki kamar bai taba ganinsu ba. Alkalin ya koma yin rubutu sannan ya dago yace "kotu na bukatar ganin Alhaji Habib a gabanta yanzu".
A tsanake babban mutumin ya mike jami'an tsaro suka rufa masa baya. Cikin takun nan nasa na kasaita da amsa sunansa. Ya isa gaban munbarin tsayuwar ya tsaya yana fuskantar al'umar dake cike da kotun. Kutu ta kaure da maganganun mutanen dake daga mishi hannu. Alkali ya buga gudumarsa domin dawo da nutsuwar kotu. Ai ko duk suka yi tsit! Ya kalli Alhaji Habib yace "Alhaji Habib ko zaka gabatarwa kotu da kanka?".
Alhaji Habib ya gyara tsayuwa. "Da fari dai sunana Alhaji Habib Inuwa. Wanda aka fi sani da Shugaba a bakunan al'uma". alkalin ya koma kallonsa bayan ya rubuta bayaninsa yace "ko ka san wadancan mutanen kuma mene ne alakarka da su?". Sai da ya koma kallonsu a lokacin su kansu shi suke kallo. Sannan ya kau da kansa gefe yace "aa, ban san su ba ya mai shari'a". Alkalin ya koma rubutawa sannan ya kalli lauyoyin yace akwai wanda yake da tambaya ga Alhajin? A bangarensa suka ce aa. Amma bar.BB ya daga hannu alamar zai yi tambaya ga Shugaba. Kotu ta bashi damar yin hakan. Ya mike ya isa gaban Alhaji Habib ya kalle shi da guntun murmushi yace "ranka ya dade kace baka san wadannan mutanen ba?" Alhaji Habib ya amsa da "eh, ban san su ba". Yace "haka ne? To in baka san su ba me yasa zasu tsallake kowa dake jihar nan kai katsaye su ambaci sunanka a matsayin wanda ya basu aikin?". Alhaji Habib ya saki fuska a wayance yace "to lauya, ni a ganina wata manufarsu ce kawai ta kokarin ganin sun bata min suna". "Kenan kana zargin suma wani ne ya turo su domin ganin sun bata maka suna?". "Eh haka nake tsammani". "To yanzu kai wa kake zargi game da hakan?". Ya yi shiru alamar yana dan nazari. "A gaskiya ba zan ce ba, dan ban taba rike kowa da mugun nufi ba, balle in yi tunanin shi yake ramako a kaina". "To ko in haka ne me yasa kace kana zargin wani ya saka su?". Tambayar ta zo masa a ba zata, amma kasancewar sa kwararre wajen iya magana ya yi saurin juyeta "to ka san mai hannu cikin lamuran siyasa baya taba rasa 'yan adawa da magauta". Br.BB ya yi murmushi "amma Alhaji na ji ita wannan 'yar gwa-gwarmaya ta zargeka da cewa kana lalata rayuwar yara mata kana dora su bisa turbar karuwanci, sannan ka fara safararsu daga nan zuwa ko-wace kasa turawa na yin badala da su. Ya abin yake?". Nan da nan yanayin shugaba ya canza, ganin dubannin idanu ne a kansa yasa ya yi gaggawar nemo nutsuwarsa "wannan karya ce kawai mara tushe. Ba ni ba, hatta makiyina bana masa fatar kasancewa mai irin wannan dabi'ar". Kotu ta sake kaure da ihun masoyansa, suna fadin "sai Shugaba. Allah ya kare ka".
Bayan sun lafa da maganganun Bar.BB ya kalle shi da murmushi yace na gode Alhaji zaka iya komawa ka zauna". Ya fada a lokacin da yake taku zuwa gaban masu laifin nan. Alhaji Habib kuma ya sauka daga inda yake ya koma mazauninsa bayan kotu ta bashi iznin hakan. Bar.BB ya sami iznin tambayoyi ga masu laifin ya fara da tambayar su ayyukansu. Kamar ba zasu fada ba sai kuma suka yanke shawarar su fada kawai su tona asiri a nemo duka ragowarsu kar su wahala su kadai. Hali (maiki) ne ya fara magana. "A wannan al'amarin fa ba mu kadai bane. Muna da yawa, kuma muna da shugaba. Bamu da wani aiki da ya wuce ta'addanci shugaban namu shi ne yaron wancan Alhajin... Ya nuna Alhaji Habib. Sannan ya dora ...Shi yake kira a duk lokacin da yake bukatar mu yi masa wani aiki na ta'addanci kamar kisa ko tsorata wasu mutane dake neman bijire masa. A iya rayuwar shashancinmu bamu taba rika bindiga ba sai da muka fara aiki da shi. Shi ya saya mana makamai a kokarinsa na ganin mun kawar masa da ita wannan 'yar gwa-gwarmayar da yace ta addabi rayuwarsa. Wanda a kokrinmu na yin hakan ne aka kama mu." "Mene ne shaidarka game da hakan?". Bar.BB ya tambaye shi. Abokanen aikina sune shaidana. Zan iya fadawa jami'an tsaro inda suke domin su ma a kamo su a gurfanar da mu tare. Kirjin Alhaji Habib ya buga da sauri ya yi kasa da kansa. Bar.BB ya yi godiya ga alkali sannan ya koma ya zauna yana 'yan rubuce-rubuce kan takardar dake gabansa.
Saida alkalin ya gama rubutunsa sannan ya dago yana kallon jama'ar dake cikin kotun yace "bisa yadda zantuka suka gabata daga bakin masu laifi, sun kara tsunduma Alhaji Habib Inawa a cikin wannan shari'ar. A saboda haka kotu ta daga wannan shari'ar zuwa mako mai zuwa, tare da bawa jami'an tsaro iznin kamo ragowar masu laifin domin samun tabbatacciyar shaida a kan wanda ake zargi. Saboda haka... "Wannan Shari'ar ta rana daya ce ya mai girma mai Shari'a". Wata murya da ba a san mamallakiyarta ba ta katse alkalin da fadin haka a cikin wadanda ke zaune bisa jerin kujerun dake cikin kotun. Hakan ya ja hankalin alkali da lauyoyin tare da ilahirin mutanen dake kotun zuwa ga mai maganar. Mace ce zaune bisa kujera, fuskarta yane da karamin mayafi. Cikin 'yan dakiku ta sauwaka ma masu son ganinta ta hanyar mikewa ta tsayu a gaban kotun tare da bude fuskarta gaba daya. Fadwa ce! 'yar gwa-gwarmaya.
Tirkashi... Keep following.
*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________
```Page 25```