← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Assalamu alaikum masoyana, masoya wannan labarin na 'YAR GWA-GWARMAYA. Babu shakka na san kun nuna so da kauna kuma kun jira. Ku sani ba dan ciwo ba da babu abinda zai tsayar da ni. Da wannan shafin nake muku albishir cewa na dawo bakin fama. Da iznin Allah zaku ci gaba da samun labarin kullum, kamar yadda aka saba. Na riga na gamsu cewa abinda kuke nuna min shi ne asalin abinda ake kira kauna. Ku sani, ku kara sani, nima nan ina kaunar ku duka. Allah ya bar zumunci ya yi karko amin.*

_Nasmat ta gode!_

```Page 18```

Shiru ya yi, yana nazarin maganarta, kafin daga bisani tunani ya zo masa da mafita. "Umaima." Ya kira sunanta a dan gajarce. "Kin sani sarai cewa ba zan iya zuwa ko turo wani daga bangarena ya taimake ku ba saboda gudun zargi. Amma ki jira yanzu zan turo muku lambar jami'an tsaro, ku neme su, su zasu zo duk inda kuke su dauko ku a saukake". Yana gama maganar ya kashe wayar, sannan ya tura mata test mai dauke da number Asp Sauwam.

Ba bata lokaci ta kira lambar. Shima dai a galabaice ta yi mishi bayanin halin da suke ciki. Nan da nan kuwa ya tashi ma'aikatansu ya tura su inda ya gano a can suke ta hanyar yin (tracking) din number da ta kira shi da ita.

Shugaba ya kasa zaune ya kasa tsaye. Sai kai komo yake yana jiran jin yadda zata kaya. A haka dansa Faisal ya same shi. "Kai lafiya ka fado min daki ba ko sallama?". Ya tambaya yana kallon yanayinsa. Shi kuwa cikin rudu da tashin hankalin da yake ciki yace "Dady ka taimake mu. Momy ce ba lafiya, gata can kamar zata mutu". Ya waro ido da alamar al'ajabi. Bai koma cewa komai ba ya nufi dakinta da sauri-sauri, gudu-gudu. Faisal din ya rufa masa baya yana sharar kwalla.

Halin da ya same ta ciki ya yi matukar razana shi, bata iya magana, ga wani jijjiga da jikinta ke yi. Sam bata san waye a kanta ba. A take ya ajiye mamakinsa gefe Faisal ya taimaka masa suka kinkime ta zuwa mota. Driver ya ja su suka nufi asibiti.

*Police station*
Linda da Zainab, da sauran 'yan matan nan ne durkushe a gaban Dpo bayan da jami'an 'yan sandan suka ceto su a cikin wani babban jeji. Bayan ya gama rubutu a file din dake gabansa ya dago ya kalle su. "Wacce ta yi garkuwa da ku tace ku ajiyar shugaba Habib ne, shin ya wannan zargin yake?". Wata mai suna Aysha ta amsa "karya take yallabai, mu bamu da wata alaka da shi". Ya jijjiga kai. "To yanzu ina ragowarku suke, a wane hali kuka baro su?". "Suna can hannunta yallabai, kuma a gaskiya suna cikin wahala. Mu kanmu yin Allah ne kawai ya tsiratar da mu".

"Shikenan duka zaku koma muhalkanku, hukuma kuma zata ci gaba da bincike domin gano inda ragowar suke. Zaku iya tafiya." Suka yi masa godiya suka fita.

Hankalin Shugaba ya rabu kashi-kashi. Ga matarsa kwance a asibiti bata san inda kanta yake ba, ga zuciyarsa ta kasa hakura da tunanin halin da 'yarsa Anisa da Baffa suke ciki. Ga kiraye-kirayen turawa a bangare daya, wadan-da dayawa a cikinsu ya karbi kudadensu ne kan cewa zai turo musu yara. Duk ya furgice ya yi wani zuru-zuru da shi.

A lokacin ya sami sakon Umaima cewa sun koma gida su takwas da suka gudo, ragowarsu kuwa suna hannun 'yar gwa-gwarmaya. Yana goge sakon likitan dake kula da ita ya fito ya kira nurse suka koma ciki da sauri. Faisal kam banda kuka ba abinda yake. Jimawa kadan likitan ya fito yana sanar musu ta sami bacci. Ya kuma bukaci ganin Alhajin a ofishinsa. Bayan sun je ne yake sanar masa damuwa ce silar ciwon matarsa. Hakan bai bashi mamaki ko yasa yayi wani tunani ba saboda sanin halin damuwar da dukkaninsu suke ciki na batan 'ya yansu. Addu'ar samun sauki suka yi mata shi da likitan, sannan ya yi masa sallama ya fita.

Daga asibitin ya wuce gida ya yi wanka ya canza kaya, sannan ya dan sami nutsuwa ya kira wayar gidan da 'yan matanshi suke dan raba musu aiki.

Amina ce ta daga wayar, wayar da take kan recording. Ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa. Kana yace "ki gayawa Aysha ta shirya yau da yamma zata tafi Mexico, Umaima kuma da sassafe zata wuce Rasha. Zainab ta tafi Dubai, ke kuma Canada. Sauran su jira zuwan kasuwa. Zan turo wa ko-waccen ku lambar wanda zata hadu da shi. Ku kasance cikin shiri bamu da lokaci sai kirana suke". Ta amsa da "to". Suka ajiye wayoyin. Ta isar da sakonsa ga duk wadanda ya abmbata. Nan da nan suka hau shiri cike da murnar samun dama.

Dukkaninsu sun sani wannan shi ne aikin karuwancinsu na karshe dan tsaida shaidu da manyan hujjoji kamar yadda suka tsara da Auntynsu Fadwa.

To fa 🤔

*Nasmat* ✍

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

```Page 19```

*Barka dai masoya makaranta wannan labarin. Ina yi wa kowa da kowa barka da wannan lokaci. Har yau dai hakuri nake bawa masoya kan tsaiko da ake ta samu ga wannan labarin. Wanda dukansu suna samuwa ne bisa manyan dalilai. Na farko na hadu da matsalar rashin lfy, bayan dawowana kuma sai matsalar waya. Wadannan abubuwan su ne suka yi mini katanga da ku da wannan labarin. Gabadayanku ina sonku kamar yadda kuke so na. Babu shakka masoya abin alfari ne ga ko-wane tauraro. Ina alfari da ku duka. Nasmat ta dawo, labarinku ma ya dawo ku mu je zuwa. 😎*

Washe gari dukkaninsu suna kasashen da aka bukaci su je. Aysha ce ta fara kammalawa a kwana dayan. Bayan ta gama maida rigarta ta kalli tsumakakken baturen da ya gama amfani da ita yake saka kaya tace cikin turancinta da bai gama kama bakinta ba "wai tafiya zaka yi, kudin aikina fa?". Busashshen baturen ya kalleta da mamaki yace cikin ingantaccen turanci "wannan wace irin magana kike kamar wata bakuwa? Kudinki kam tun kafin ki zo suka sauka a asusun mai gidanki Alaji Abib". Yadda suke kiransa kenan. Aysha ta wayance da cewa "Oh! Yi hakuri, na manta ne saboda uzuri na bukatar kudin da nake ciki". Baturen mai suna Michale ya daga kafada irin ko a jikinsa din nan ya fice yana mata sallama. Ta sauke numfashi tana mai kashe camera da ta kunna tana daukar maganganun da suke. Ta mike cike da murna tana hada kayanta dan komawa gida Najeriya.

*Ranar assabar a maitama*
Bayan ta gama motsa jiki ta fito da nufi komawa dakinta, sai ta tsinci kanta da son ganinshi da halin da yake ciki. Duk da Ab'ha ya sanar mata cewa guy din ya warke sumul. Kawai ta ji ne tana son ganinsa ne. A hankali ta nufi kofar dakin da yake cikin takunta na cikakkiyar mace mai ji da kanta. Ta mirda kofar bayan ta murza key, ta tura ta shiga. Baffa da idonsa suke kan kofar tun da ya ji ana taba key ya zubawa mai shigowar ido. Shi a zatonsa Ab'ha ne domin rabonsa da ganin Fadwa tun ranar da wannan tsautsayin ya gifta ta masa dukan kawo wuka. Amma Ab'ha kam kullum suna tare, shi yake kula da abincinsa. Sun saba da shi sosai fiye da kima.

Ita da shi duka ba wanda ya yi magana, sai dai dukkaninsu sun zurfafa ga kallon junansu cikin wani irin yanayi. Ita ce ta fara yin jarumtar kauda kanta ga barin kallonsa tana mai jin haushin zuciyarta kan yadda take yabawa da kebance kyan zubi da halittar Baffa a kan duk wani da namiji da ta taba gani a rayuwarta. Bata san shi ba sai a kan wannan abin na ubansa, amma zuciyarta tana nuna shi daban ne da ko-wane namiji. Take haushin kanta ya fara kamata, sai ta ga kamar yana ganin halin da take ciki. Da sauri ta juya da nufin barin dakin ba tare da tace komai ba. Har ta kama handle na kofa zata murda ta ji sautin muryarsa cikin sanyi da tausasawa yana cewa "dakata mana Fadwa, ba dan ni da nasabata ba ki tsaya ki saurare ni domin Allah". Cak! Ta ja ta tsaya, tare da dakatar da bude kofar da ta yi niyya. Babu wani kwakkwaran dalili kawai sai ta ji jikinta ya yi sanyi. Ko dan yanayin yadda ya fitar da maganar ne?.. Ci gaba da maganar da ya yi ne ya katse mata tunani. "Ki yi hakuri Fadwa. Hakika na sani idan kika kalle mu ta fuskar nasaba da tushe sam ba mu can-canci ki yi mana afwa ko rangwame ba. Amma ina so ki kawar da duk wadannan. Ki kallemu a matsayin al'uma, 'yaya marayu wadanda basu da uba a duniyar nan. Fadwa ki dubi Allah da darajar Annabinsa ki dawo mana da Anisa. Da can a baya ina miki kallon azzaluma mara imani wadda ake biya kudi tana cutar da mahaifina. Amma a yanzu da Allah yasa aka yi walkiya ta haska idona na ga komai Fadwa. Abokin aikinki ya gaya min komai ya kuma nuna min tsayayyin hujjojin da suka saka na yarda da ku, na ji bayanai dabam-daban a bakin 'yan matan nan da suke nan. Fadwa na gano mahaifina da halayyarsa su suka saka kike yin duk wani abu da kike. Har ga Allah ban ga laifinki ba, mutumin da aka zalumta kamar ke babu abinda ba zai iya yi ba. A yanzu na san waye mahaifina, na san cikakkiyar gurbatacciyar sana'arsa. Na tsane shi, na tsani halayyarsa. Bana fata ko burin a koma kiransa ubana, bana son ko-wace alaka ta koma hadani da shi na tsane shi." Ya matse idonsa da karfi wasu zafafan hawaye suka silalo zuciyarsa cike da nadama da dana sanin zamowa daya daga cikin 'yayan Alhaji Habib.
Chapter 13 · 0% Book details