← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannunku 'yan uwa, kuyi hakuri fa, na tara ku nan amma ban samu muka hadu ba. Na san ba wadda ta san ni a cikinku. Sai dai na san zaku san sunana. Fadwa nake 'yar gwa-gwarmaya. Na kawo ku nan ne domin ganar da ku asalin batan da kuke kai. Ku mata ne, amma har yau baku san daraja da martabar da 'ya mace take da ita ba. Mafi yawan mata sun kare kansu da mutuncinsu. Amma saboda ire-irenku matan titi, ana yi musu kallon wulakanci. Irinku mata masu zaman kansu ku kuke karya darajar 'ya mace a idon duniya. Shin ku bakwa kishin jinsinku ne?". Ta takaita tana kallon fuskokinsu da suka yi la'asar. Ganin ba wadda ta yi magana yasa ta ci gaba.

Nan da kuke gani na, na tsinci kaina a kuncin rayuwar da ya nunka wanda ko-waccenku ta taba shiga. Na rasa mutuncina, alfaharina. A lokacin da yake daf da amfana ta. Ni marainiya ce, wadda ta taso da burin yin karatu mai zurfi don inganta rayuwarta. Hakan yasa na tilastawa kaina karatu, ba dare ba rana. Kwazona yasa makaranta da iyayen rikona suke alfahari da ni. Ni kuwa ina yin wannan fafutukar ne dan samawa kaina kima a idon duniya, na taso da burin gwadawa 'yan uwana marayu cewa babu maraya sai rago. Amma kafin cimma wannan burin Uban-gidanku ya ruguza rayuwata. Ya yiwa burukana kisan gilla. Kutsen da ya yi a cikin rayuwata da nufin taimako shi ya maida ni yadda kuka ganin nan. Shugaba Habib ba karamin makiyi bane ga mata. Ku sani gatan da yake yi muku ba so bane, ba kuma taimako bane, kasuwancinsa kawai yake ingantawa da ku. Yayin da ku kuma a kullum kuke dada nisanta kanku daga rahmar Allah. Kuke fama da bakar addu'ar matan kirki bisa bata musu suna da kuke. A kan karamin laifin da bai kai komai ba ku baro gidajen iyayenku. Ku bar duka danginku dan kuna jin da akwai abin kudi a jikinku. Kun manta wannan abin na dan lokaci ne? Kun manta kuruciya ke karuwanci?". Ta koma sararawa tana kallonsu.

Ba wadda ta yi magana jikinsu kuma ya yi sanyi sosai. Ta jijjiga kai tace "ni mai son ku ce, mai matukakar kaunar ku. A rayuwar da ta rage min bani da burin da ya wuce inga na samawa mata 'yanci. Burina a wayi gari babu karuwa a kasar hausa. Ya zamana duka matan duniya sun san matsayi da darajarsu. Ko-wane namiji ya wahala ya biya sadakinki kafin ya mallake ki. Wannan shi ne cikar kimar mace. Ba wai ta zama bola abin zuba sharar ko-wane fasiki ba Yanzu ku kalli nan". Ta danna musu play ga TV dake dakin wanda ta riga ta gama saita komai. Hoton video ya bayyana yadda aka keta haddin Anisa 'yar Shugaba. Duka sun gane ta, suka shiga kallon-kallo. Fadwa ta kashe TV ta koma fuskantarsu.

"Da gan-gan nasa aka yi mata haka. Domin shi ma ya ji yadda iyaye suke ji, a lokacin da yake dora musu 'yaya a kan turbar karuwanci. Saboda wannan da kuka gani kwanakinsa uku a asibiti bai san kansa ba. Kun san saboda meye? Saboda ita tashi ce, ya san darajarta, yana son mutuncinta. Ku kuma ya dauke ku dabbobi wadanda basu da iyayen da zasu cutu kan rayuwar da suke. Da yawa a cikinku nan bakin cikinku zai kashe iyayenku..." Tun bata karasa ba wata a cikinsu ta fashe da kuka.

Sannan ta taso daga inda take zaune ta nufo inda Fadwa take.

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Godiya mai tarin albarka gareki MAMAN ISLAM na gode da yabo, da tarin adduo'inki gare ni. Fatana shi ne Allah ya bar zumunci da kaunar juna* ```Ki sani ina sane dake a cikin jerin masoyana, ana matukar tare``` 🤝

```Page 17```

Da zuwa ta zube a gabanta, tare da kama kafafuwanta ta soma magana cikin kukan... "Hakika Anti ke mace ce da kika san darajar mata. Da ace duka mata zamu yi koyi dake, da duniya ta tsarkaka, da masifun da muke ciki sun takaita, da bala'in da ake saukar mana ya ragu. Domin a yau a halin da muke ciki babu abinda aka mayarwa hankali kamar zinace-zinace. Wallahi Anti safarar nan ta mata da ake kar ki so ki ga yadda ake yi da su. Da yawa daga cikin mu ma ba ta inda Allah ya halatta ake amfani da mu ba. Kazantar ta girmama, babban tashin hankalin ma shi ne, ki ji, ko ki ga masu daukar nauyin matan suna tura su yin karuwancin. Da yawa a cikinsu manyan mutane ne, masu kima da daraja a idon al'uma. Wadanda ko sunansu aka kira a cikin masu laifin ba zaki yarda ba. A yau su ne suke bautar da 'yayan talakawa masu karamin karfi. Wadanda 'yayansu ke barin gidajensu a sanadin yin cikin shege, ko auren da basa so (auren dole). Da kuma masu samun wani sabanin daban tsakaninsu da iyaye. Wanda wannan kuskuren namu ne mu da iyayenmu. Wasu iyayen su suke korarsu suce sai sun bar gidan, wasu kuwa ba ma da sanin iyayenba suke lallabawa su baro gidajen saboda gudun auren wanda ba shi suke so ba.

Anti da haka rayuwar 'yaya mata take fara lalacewa, a farkon fitowarmu wahala muke sha sosai, domin ko abinda zamu ci wahala yake mana. A haka ne muke samun masu neman mu fasikanci, tun muna jin tsoron yi har mu fara. Sannu a hankli mu samu muhalli, kudi da ababen more rayuwa. A cikin haka ne muke haduwa da irin su shugaba. Wadanda ke kwadaita mana duniya da kyale-kyalinta. Sai muga ai da wanda muke a nan da wanda zamu yi a can duk karuwanci sunansa. Wannan ne yasa bama shayi ko shakkar amsa kiransu. Ya zamana har ma dadi muke ji idan aka zabe mu, domin kudaden da muke samu a can sai mu shekara a nan bamu same su ba.

Wannan ne yake sawa muke biyewa masu yin safara, da saninmu muke bada kanmu gare su. Amma a yau Allah ya kawo mana ke, babu shakka ke *fitilar 'yan-cin mata* ce. Kin haska ni, na kuma ga tarin kazanta da koma bayan da nake ciki. Anti Fadwa na bada kaina gareki, daga yau an daina amfani da ni wajen yada zina a doron kasa. Na yi niyyar tubarwa mai duka. Tare da neman gafararsa bisa laifukana na baya". Ta karashe maganar tana tsananta kukanta, tare da kankame kafafuwan Fadwa da take rungume da su. Kafin Fadwa ta ce wani abu, ta kusa da ita ta fara magana... "Babu shaka a maganar Zainab, iyayenmu ma suna da rawar da zasu taka, domin rage yaduwar karuwanci a kasarmu. Wannan rawar ko ita ce: su guji korar 'yayansu mata daga gidajensu don kaddara ta afka musu, ko don sun ki bin zabinsu ga aure. Idan aka samu haka hakika za'a rage masifu. Sannan kuma mu mata mu kiyaye, kurciya ta daina fizgarmu muna yin abinda muke so. Wlh mata muna cikin hatsari. Nima daga yau na tuba, ina bayanki. Ki ci gaba da haska muna hanya, yake wannan *fitilar*".

Ta miko hannayenta ga Fadwa. Fadwa ta amsa ta rike ta gam. Haka dai da guda-guda suka yi ta bada kansu gareta. Duka su goma sha bakwai din-nan babu wadda ta juya bawa. Allah ya yi musu rabo sun yarda har cikin ransu cewa karuwanci koma baya ne, kuma masifa ne ga rayukan mutane, har wadanda basu ji ba, basu gani ba. Domin ita masifa idan zata sauka ba kan iya masu laifin take tsayawa ba. (Shiyasa a kullum idan kaga laifi ba a so ka kauda kai dan kai baka aikatawa, an fi so ka tsaya ka yi iya kokarinka wajen ganin ka dakatar da shi. To ko da abin yafi karfinka ka riga ka samu ladar. To balle kuma ka yi nasarar dakushe shi. Allah yasa mu dace amin.)

Farin ciki mara misaltuwa ya kama Fadwa, har ta rasa bakin magana, sai wasu siraran hawaye dake bin kuncinta. Ta kalle su, kallo na jin dadi tace "alhamdulillahi dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, madaukaki. A yau ina cikin farin cikin mara misali, dalilin wannan goyon bayan naku. Domin da gudumawarku ne zamu samu dukkanin hujjojin da mahukunta suke bukata domin gurfanar da Shugaba a gaban kuliya. Ta ware hannayenta aiko duk suka yanyame ta, ko-wannensu na cike da farin ciki.

A wurin ta ware guda takwas daga cikinsu, wadanda tauraruwarsu ke haskawa, kuma su ne Shugaba yafi ji da su a kasuwar tashi ta sake su. Saboda ta san muddin ta sake su duka zai gano shirinta a kansa. Bayan ta gama shirya musu yadda zasu dauko mata sirrukansa irin na harkarsu, ta bawa ko-wacce daga cikinsu kayan aiki, sannan ta dora su a hanya.

*3:56pm*
Wayar Shugaba Habib ta fara ruri. Kishingide kawai yake yana saka da warwara. Tunanin 'yarsa Anisa da halin da take ciki ya addabe shi. Sai juyi yake yana neman abin yi. Hakan yasa bai yi wani jinkiri wurin daga wayar ba. Lambar Umaima ya gani. Daya daga cikin matan nan da Fadwa ta sace masa. Da sauri ya daga wayar yana kiran sunanta. Ta amsa da kyar ta fara magana cikin yanayin galabaita. "Shugaba ka taimake mu, gamu nan mun gudo daga hannun azzalumar nan, amma bamu san inda muke ba. Muna cikin wani hali dan Allah a kawo mana dauki".

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

_Alhamdulillah ala kulli halin_
Chapter 12 · 0% Book details