← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shari'a ta yi zafi, shaidannu sun bayyana cewa duk abinda Fadwa ta fada karya ne. Burinta daya, shi ne ta batawa taddijon suna. A cikin shedannunsu kuwa hadda ragowar 'yan matan nan da aka dauke su tare da Fadwa. An zo da su kasar, sun kuma bada shaida kan cewa tun da suka tafi su kam karatu suke. Ga takardunsu nan na ko-wane mataki. Sannan suka bayyana Fadwa a matsayin wadda ta gudu daga inda aka ajiye su, ta tare a wani club ta fara rawa da wokoki. A can ta koyi shaye-shayen miyagun kwayoyi ta kuma kware a fannin karuwanci. Suka ce lokacin da aka fara nemanta kuma sai labari ya zo daga gun da take zaune wai ta mutu.

Domin kwantarwa iyayen rikonta da hankali yasa ba a gaya musu cikakkiyar gaskiyar halinda ta jefa kanta a ciki ba. Wannan shi ne abinda suka sani game da ita.

Duba ga ire-iren wadan-nan shaidannun ne aka yi watsi da karar, tare da wanke wanda ake zargi. A karshe kotu ta daure Fadwa na shekaru uku a gidan kaso, bisa laifin batawa babban mutum kamar Alh. Habib suna.

Wannan shi ne rashin adalcin da ya fara fusata Fadwa, ya fara sauya tunaninta. Ta fara nazari a kan neman mafita. A rayuwarta ta gidan kaso kuwa ta kara samun wayewar rayuwa a cikin masu manyan laifuka. Mata ne daga Jihohi dabam-daban. Wasu laifukansu na kisan kai ne, wasu kuma na ta'addanci a ciki ma har da 'yan fashi da makami. Sune suka kara tunzura ta, suka hure mata kunne kan ta yi duk yadda zata yi wajen ganin ta tona asirin Alh. Habib.

Fadwa ta yarda, ta kuma karbi shawarwarin da abokanin zamanta na gidan kaso suke bata. A haka rayuwarta ta yi ta tafiya a can. Yayin da bakin ciki da kunci suka cika gidan marayu. Har zuwa lokacin da aka yankewa Fadwa ya kare ta fito daga gidan kaso. Zuwa lokacin ciwon Ummynta ya kara tsananta har ta kai bata iya tashi. Saboda bakin cikin da take ciki na halin da Fadwa ta shiga.

Jikin kowa a gidan ya yi sanyi. Sun ja'janta mata, a karshe suka ce ta fita hanyar Alh. Habib ta maida hankali ga gyaran ragowar rayuwar da ta rage mata. Sun tsoratar da ita game da abinda zai iya yi mata idan ta ci gaba da neman tona asirinsa.

Ranar bacci gagarar idonta ya yi. Ga tsananin ciwon Ummy ga bala'in matsin da zuciyarta take mata kan kar ta yarda ta bar maganar nan, ta ci gaba da bibiyarta, har lokacin da zata yi dacen yin nasara a kansa.

Da dai tunanukan suka hadu suka yi mata yawa sai ta saka kuka. A lokacin tana zaune gaban Ummynta wadda take tunanin ta dade da yin bacci. Cikin kukan ta fara magana "yanzu shikenan muna ji muna gani zai ci gaba da bautar da rayuwar 'ya yan bayin Allah marasa karfi? Iyayen da suke samun abinda zasu ci dakyar. Su ciyar da 'ya yansu, su kuma tarbiyantar da su. Su tattare duk abinda suke da shi su basu ilmi. Duk wannan kokarin suna yin shi ne dan buri da fatan ganin yaran nasu sun zama na gari. Su sami ingantacciyar rayuwa. Amma a karshe sune ake maida 'ya yansu karuwai. Ababen kasuwanci? Tir! Ya Allah dubi halin da Ummynna take ciki, duk saboda bakin cikin gurbatacciyar rayuwar da aka jefa ni a ciki. Yanzu haka iyaye zasu kare a wannan kuncin? Allah ka amshi raina, ni dai ba zan iya rayuwa ina kallon wannan azzalumin mutum da ire-irensa a cikin kasata ba tare da na dauki wani mataki a kansu ba. Ba zan iya ba."

Ta kara tsananta kukanta...

Ummy wadda ke sauraren maganganun 'yar ta'ta, ta juyo da dakyar. Ta lalubi hannunta ta damke. Sannan ta kakaro kalmomin sunanta ta hada ta kira ta. Ta amsa murya na rawa, saboda tsabar kukan da take.

Ummyn tace "Fadwa ni kaina ban goyi da bayan hakan ta ci gaba da kasancewa ba...

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

```page 6```

Ta ci gaba da cewa.. " 'Yata ke nake jiyewa, bana so wani abu ya same ki. Amma tunda har kika yi wannan tunanin na tabbata zaki zama mai juriya, na san zaki ja'jirce. Na baki dama 'yata. Ki dakatar da Shugaba Habib da masu sana'a irin tasa in dai zaki iya. Ni kuma zan zamana mai sa miki albarka ko bayan raina. Fadwa kin fadi gaskiya iyayen irin wadan-nan yaran bakin ciki ne zai ci gaba da kashe su kamar yanda yake daf da kashe ni. Ba zan boye miki ba 'yata, bana ji wannan ciwon zai bar ni. Saboda haka na baki dukkanin goyon bayana. Ina goyon bayan manufarki, na kuma baki dama ki fara gwa-gwarmaya. Ki tunkari duk wani azzalumi ki toni asirinsa. Kar ki barsu, kar ki sassauta musu. Rike wannan..." Ta karashe maganar tana damka mata wata karamar laya a hannunta na dama. Tace "wannan layar ta bata ce. Gudummawa ta farko da zan baki, saboda na san wadan-nan maha'intan zasu fara farautar rayuwarki. A duk lokacin da kika matsu, aka rutsa ki. Sai ki matsa ta da bismillah. Da iznin Allah zaki bacewa ganinsu, zaki bayyana a duk inda kika yi ra'ayi. Sannan abu na gaba da zan gaya miki shi ne, ki tsarkake kanki da zuciyarki, ki yi watsi darayuwar da kika yi a England ki buda wata sabuwa a nan. Ki zama mai yawan ibada da kaiwa Allah kukanki. Ki dage da bincike a kan abinda kika sa gaba. Ina kaunarki Fadwa. Ina jinki kamar 'yar da na haifa a cikina.

Na gama magana da shugaban gidan nan, duk wasu kudade da na shafe shekaru ina tarawa, na aiki da ma na gudumawa da ake bamu, na mallaka miki su. Ki yi amfani da su wajen tafiyar da aikinki. Ina da wani karamin gida a mai-tama na san kin gane gidan da nake nufi. Shima na mallaka miki shi. Domin ya zama dole ki bar gidan nan, ki nisanta kanki da wadanda suka san ki.

Kar ki yarda da kowa sai kanki. Kar kuma ki nemi taimakon kowa sai na Allah. Ke ta daban ce, ni na rene ki. Na sani zuciyarki ta musamman ce. Zaki iya duk abinda kika sa a gaba. Ina miki fatan alkhairi 'yata. Zan zama mai alfahari da ke, idan kika zama *fitilar 'yan-cin mata.* Fadwa ta rungume Ummy cikin tsananin murna da farin cikin goyon bayan da ta samu daga gareta. Ta fara kwarara mata godiya da kyawawan adduo'i. Haka suka kasance har zuwa asuba. Inda ta tashi ta shiga bayi ta dauro alwala, ta fito ta tashi salla bayan da ta lura cewa Ummynta ta samu yin bacci.

Ta dade da kammala salla da adduo'inta, amma Ummy ko motsawa bata yi ba. Tunaninta ya bata ramakon bacci take yi, tun da jiya duk basu yi baccin ba. Karfe bakwai dai-dai ta yanke shawarar tashin ta dan ta yi salla a yadda take lallabawa tana yi kullum. Amma inaa. Abinda bata sani ba shi ne Ummynta ta dade da amsa kiran buwayi. Ta tafi inda ba a tafiya a dawo. Tayi bacci ne irin wanda ba a farkawa a doron kasa.

Allahu Akbar! Fadwa ta da'da shiga kunci, ta yi kuka kamar ranta zai fita. A karshe aka kai Ummy Amina gidanta na gaskiya. A lokacin ne Fadwa ta san maraici, a lokacin ta san zafin rabuwa da iyaye. Bayan lokaci mai tsayi ta aiwatar da duk abubuwan da Ummy ta bar mata wasiyyar ta yi. Ta karbi makudan kudaden ta loda su a account dinta. Ta hada su da nata. Sannan ta tattare ta bar gidan marayu ba tare da sanin kowa a gidan ba.

Kamar yadda Ummy ta bukata bata yarda ta sanarwa kowa shirinta ba. Kawai dai an wayi gari aka ga babu ita a gidan.

Hukumar gidan da marayun da suke gidan har zanga-zanga suka yi, saboda batan dabon da Fadwa ta yi. A tunaninsu Shugaba ne ya tura aka sace ta.

Ganin haka yasa ta aika musu wasika a rubuce, cewa su kwantar da hankalinsu bata hannun kowa. Kuma a inda take tana cikin koshin lafiya.

Daga wannan lokacin ne ta fara binciken sirri, da bibiyar duk wasu ayukka da Shugaba Habib yake aiwatarwa. Daga lokacin ta daura damarar *gwa-gwarmaya* da yakar azzaluman mutane irinsa a cikin kasarta.

Zuwa lokacin kuma al'amarin shugaban ya kara habaka. Ya ma daina dibar dalibai da 'ya yan talakawa, ya koma kan karuwan gari. Irin wadan-da suke samun matsalar Auren dole da iyayensu, su baro gidajensu. Da masu haduwa da kaddarar cikin banza, iyayen su kore su. Kasancewar zuwa lokacin sun yawaita sun cika ko-ina. Suna neman mafaka da abinda zasu ci su biya bukatunsu. Sai ya zamana aikin ya daina bashi wahala. Yarje-jeniya yake kullawa da su yana kai su kasashe suna karuwanci. Idan aka dawo sai ya basu dan ihsani a cikin abinda ya samu da su din.

A haka yake kara bude musu idon. An fara hawa jirgi ana harka da turawa. Sai suke jin kansu kamar wasu hamshakai.

Hakan yasa ya tara karuwai yarurruka dabam-daban. Ya rarraba su a wasu gidajensa na sirri. Sai dai wannan duk a cikin sirri ne. Amma ita Fadwa duka ta san komai game da shi.

Wannan shi ne tarihin rayuwar *'Yar gwa-gwarmaya Fadwa* da musabbabin 'yar tsamar dake tsakaninta da shugaba Habib. Mutumin da al'uma suke wa kallon Uba, adali, mai so da tausayin talakawa. Hakan yasa duk garin suka tsani *'yar gwa-gwarmaya* a ganinsu abinda aka fada game da ita gaskiya ne. Wato wasu'yan siyasa ne suke amfani da ita wajen ganin sun shafa masa bakin fenti. Lokacin da ayyukanta suka fara bayyana kuma, sai suka dawo yi mata kallon 'yar ta'adda.

*Ci gaban labari...*
Washe gari da safe Fadwa ta koma daura damarar shiga gari neman wata damar.

Kamar yanda a can ma Chaka (dan ta'addan Shugaba) da yaransa suka shirya tsab dan nemanta bisa umarnin Shugaba. A cikin garin Kano.
Chapter 4 · 0% Book details