← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin ya kasa mikewa daga kan kujerar ne ya tuna masa a daure yake. Ya zubawa sarkar da ta daure shi da ita ido, yayin da bakin ciki ya mamaye zuciyarsa. Ya sake dago da jajayen idonsa ya kalleta yana cewa "banza karamar tsagera. Wannan daurin da kika min ya tabbatar min kina jin tsorona ne, in ba haka ba ki kwance ni ki tsaya a gabana mana. Wallahi kisan da zan miki shi zai zama kisa mafi muni da aka taba yi a cikin duniyar nan". Ya saka aya yana ciccika kamar wani mayunwacin Zaki. Fadwa ranta ya yi masifar baci, ita ma a take launin idonta ya canza. Jikinta har bari yake ta fara magana "lallai kai jahili ne. Kallon me kake min ne? Ka dauka 'yar gwa-gwarmaya kamar ko-wace mace take? To bari a kwance ka din ka yi abinda zaka iya". Ta fice daga dakin a matukar fusace ta nufi nata dakin a ranta cewa take lallai yau ko bata kashe wannan yaron ba sai ta hada masa jini da majina. Ba jimawa ta fito tana huci hannunta rike da daurin makkulansu.

Ab'ha dake zaune a falo yana kallon shige da ficenta ya miki ya rufa mata baya, saboda ganin yanayinta. Da isarta dakin kai tsaye ta isa gaban kujerar tana kokarin kwance shi.

Tsabar yadda ya kagu ya kashe ta, tun kan ta gama kwance hannunsa daya ya yi amfani da kansa ya buga a nata. Ji kake gum! Dai-dai da shigowar Ab'ha kenan. Ta tsaida abinda take ta dago ta wanke kuncinshi da wani rikitaccen mari, wanda ya sa idanunsa suka fara gani bibbiyu. "Banza mai karamin tunani, ka bari na kwance ka mana. In yaso sai ka fito da dukkan karfin da kake da shi ka kashe ni".

Ta koma dukawa da nufin ci gaba da kwance shin.

Ab'ha ne ya yi wuf ya rike hannunta tare da mikar da ita tsaye. "Me kike shirin aikatawa haka Fadwa? Ta ya kike tunanin hada karfinki da na namiji? Wannan kuskure ne karki soma pls". Wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare mata a makogwaro, wai me maza suka dauki mata ne? Bata san lokacin da ta kai wa Ab'ha wani mugun naushi a fuska ba. Ya yi baya taga-taga ya fadi kasa. Daga lokacin ya daina ganinta sai maganganun da take cikin fushi, da yake ji sama-sama. "Ina namijin yake? Wannan ne namijin? Me kake tunanin samu a jikin da aka gina shi da haramun? Dole in ganar da wannan kuskurensa. Dole ya san ni din ba kamar ko-wace mace bace, burin ramuwa bai bar ni sakankancewa na san dadin jikina ba". Ta juya ta ci gaba da kwance shi.

Baffa ya zuba mata ido yadda take zuba masifa. Bangaren zuciyarsa na kokarin yabon yadda fadan ya yi mata kyau. Bangare mafi rinjaye kuwa Allah Allah yake tagama kwance shi ya yi mata kisan gilla. Hakika yau zai kawar da abinda ya hana mahaifinsa da duka familynsa sukuni da walwala, abinda ya jefa rayukansu a cikin bakin ciki.

Sai da ta gama kwance shi sannan ta ja da baya ta yi wani irin juyi, lokaci daya rigar nan dake jikinta ta nadi-diye. Ta sa hannu ta daure ta a inda ta taru. Ta daure gashin kanta waje daya ta zuba masa ido tana cewa. "To me kake jira? Bismillah man zo ka kashe Fadwa". Baffa ya yi saurin kauda yabon yadda ta kara kyawu a zuciyarsa. Tsana da kiyayyarta suka mamaye a lokacin da ya tuna video da ta dauka na yadda ake lalata rayuwar gudar kanwarsu Anisa, wadda a sanadinta har yau basu san inda take ba. Ya yi wani rin karaji ya nufe ta da gudu zuciyarsa dauke da mugun nufi. Haka itama ta tare shi cike da burin jiyar da shi asalin karfinta. Nan fa aka kaure da fada babu ji babu gani. Ba wanda yake rike da wani makami a cikinsu, sai dai ko-wannensu na kokarin nuna asalin karfi da kuma kwarewarsa. Burin ko-wanne ya illata abokin fadansa.

Naushi da yakuci suke kaiwa junansu ta hannu da kafa, kafin kace me Baffa ya fara jigata. Duk abinda ake dukansa daya bai sami taba Fadwa ba. Da kwarewarta take kare harinsa kuma ta dake shi. Tun yana taga-taga har ya kai ga faduwa, baki da hancinsa duka jini suke fitarwa. Ga wasu manyan gurare uku da ta kumbura masa a ka.

Sai a lokacin idon Ab'ha suka dawo da ganinsu dai-dai. Saboda mugun naushin da Fadwa ta masa. Ganin Baffa a kasa tana ball da shi yasa shi hanzarin mikewa. Wannan karon da rarrashi ya je mata.

"Dan Allah ki dakata Fadwa, hakan ai kashe shi zaki yi. Ya isa haka pls". Ya rike ta yana jijjigata. Bata ce da shi komai ba ta fizge jikinta ta fice daga dakin, ta bar shi da Baffa ranga-ranga.

Ab'ha ya tallafa masa ya mikar da shi ya maida kan kujerar da yake kai ya zaunar da shi. Ya yi laushi sosai har baya gane komai. Kansa ma ya kasa tsayuwa sai lilo yake kamar dan mashalo. Da gudu Ab'ha ya nufi dakin Fadwa. Ya tura kofar ya shiga yana kiran sunanta. A lokacin tana tsaye gaban karamar freezer dake dakin tana kora ruwan sanyi. Sai goge gumi take da wani karamin kyalle dake hannunta. Ta juyo ta zuba masa ido kawai. Shi kuwa cikin rawar murya yake mata bayani. "Guy din nan fa zai iya mutuwa, bai san inda kansa yake ba. Ga baki da hancinsa na zubda jini". Sam bata ji wani tausayinsa ba, amma sai ta ji sam bata so ya mutu ko dan saboda mahaifiyarsa. "Ka je ina zuwa". Iya abinda tace da shi kenan. Ta shige toilet dinta. Shi ko ya koma gurin Baffa da sauri.

Ta dauki mintuna goma kafin ta fito a hakan ma ta hanzarta saboda tausayin uwar yaron ba dan shi ko ubansa ba. Ta shigo dakin cikin wata sabuwar shigar. Hakan ya nuna wanka ta yi ta sauya kayanta zuwa wasu kana-nan kaya riga da wando pink colour. Da flat shoe su ma pink. Ta tattare gashin kanta ta daure shi guri daya bayan ta taje shi. Wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mata, wato a duk lokacin da ta sauya shiga sai mai kallonta ya ga tafi ta dazu kyau.

Karamin akwatin agaji ne a hannunta, ta zuba masa ido cikin wani yanayi. Ita kanta bata san ta illata shi hakan ba. A yadda yake kam babu mamaki zai iya mutuwa. Sai ta ji faduwar gaba ta riski zuciyarta, dan tun da take bata taba yin kisan kai ba. Ga tausayin halinda mahaifiyarsa zata shiga idan shima ta rasa shi. Sai ta ji tana tsoron ta zama wannan mugun sanadi. A dan tsorace tace da Ab'ha "na shiga uku Ab'ha, mahaifiyarsa ba zata yafe min ba in na kashe shi. Pls ka yi wani abu". Ganin ta bashi dama yasa ya dauko Baffa daga kan kujerar nan ya kwantar da shi bisa dogon bancin dake ajiye a tsakiyar dakin. Sannan ya dauko akwatin ya dire. Wani tunani ne ya zo wa Fadwa kasancewar bata da wani makiyi sama da Shugaba a kullum burinta ta saka shi bakin ciki.

"Dakata Ab'ha kar ka masa komai, ina zuwa". Ta fada tana mai ficewa daga dakin. Ab'ha ya bita da kallon mamaki al'amarinta ya fara bashi tsoro. Sai kace mai al'janu? Ya tambayi kansa. Bisa dole ya dakatar da aniyarsa yana kallon mawuyacin halin da Baffa yake ciki na rai ko mutuwa. Ba jimawa ta dawo da wayar hannunta ta dauki hotunan guy din guda biyu sannan ta yi murmushi. "Ka yi duk yadda zaka yi ka ceto shi, bana so ya mutu". Tana gama fadin hakan ta juya ta fice. Dan tana da yakinin in dai ba lokacinsa ne ya yi ba Abba zai iya dawo da shi.

Tana zuwa da hotunan sai ta dora su kan media kawai a groups na Facebook da whatsapp tare da bayanin ga dan gidan shugaba da ya bata yana hannun 'yar gwa-gwarmaya tana azabtar da shi. Abinka da 'yan social net basa sanya wajen yada ire-iren wannan post din, sai nan da nan labari ya game ko-ina, hotuna suka bazu.

Yau ne ranar shiga kotu da sanannun 'yan ta'addan nan da Asp Sauwam ya kama wadanda suka bindige dan sanda daya kuma suka yi musayar wuta da jami'an tsaron. Bayan dogon bincike da azabtarwa sun sanar wa Asp cewa basu da wata alaka da Fadwa basu santa ba sai ta dalilin Shugaba Habib, domin shi suke yi wa aiki. Shi ne ya basu umarnin su kashe ta. Jikin Asp ya yi sanyi sosai, hankalinsa in ya yi dubu ya tashi. Yayinda zuciyarsa ta kasa raba daya biyu. Shin da gaske Shugaba mai laifi ne, ko dan tana neman bata masa suna ne ya yanke wannan hukuncin?. Domin bayan wannan ba abinda 'yan ta'addan suka sani game da shi. Kawai dai yace su kashe masa ita.

Wannan ne yasa ya kasa sanarwa kowa sakamakon bincikensa duk kuwa da matsin tambayoyi da yake samu daga 'yan jarida. Baban kotun ta gama cika da batsewa da lauyoyi da kuma masu son jin ta bakin 'yan ta'addan a kotu tunda sun kasa samu a gurin jami'an tsaro. Tuni 'yan jaridu daga bangarori dabam-daban suka hallara.

Hilix biyu aka ciko da ma'aikata tare da masu laifin suka faka a kofar kotun. Asp Sauwam ne kan gaba, sai yaransa dake rirrike da masu laifin suna rufa masa baya. Fitowarsu ke da wuya 'yan jarida suka yo musu caa da tambayoyi. Sai dai tun a can headcoter Ogan ya gaya musu kada wanda ya zanta da su. Hakan yasa ragowar 'yan sandan suka shiga ture mutanen suna buda musu hanya har suka shiga kotun.
Chapter 10 · 0% Book details