← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Bayan wasu hekarun uku.*
Sai ta tsinci kanta a wani yanayi na yawan yin mafarki da Ummynta. Tana yi mata fada da gargadi a kan ta gaggauta barin rayuwar da take. Koda zata mutu ne to ta mutu a kan hanyarta ta komawa gida Najeri. Nan fa hankali Fadwa ya fara komawa gida. Ta fara shiri cikin sirri da kwarewarta. Satar hanya ta fara yiwa mai gidanta James tana kula wasu mazan ta gefe tana karbar kudin. Ta bude asu-sun ajiya (bank account). Ta fara ajiye kudinta, kafin ka ce me Fadwa ta tara biliyoyin kudi. To a hankali kuma a sirrance ta yi passport (visa) ta fara shirin biyan kudin jirgi zuwa Najeriya.

Cikin wannan yunkurin ne asirinta ya tonu. James ya gano shirinta na son guje masa. Nan fa ya rikice ya kuma sauya mata. Ba imani balle tausayi ya shiga azabtar da ita. Ya hanata fita ko'ina. Daga gidanshi sai gidanshi. Ya saka ta aiki ya kuma yi amfani da ita. Duk lokacin da zai fita kuma sai ya kulle ta a gida. Haka ta shafe watanni biyu babu mafita. Ga mafarkin Ummynta sai kara matsanta mata yake. Ta matsa mata ta je gareta ko ta halin ya'ya.

Rayuwa ta yi tsanani, ta fara tunanin bin umarnin Ummy ta fita ko da James zai kashe ta. Wata ranar lahadi da safe James ya tafi Church wajen ibadarsa kamar yanda ya saba. Ita kuwa sai ta fara shirin barin gidan kafin lokacin dawowarsa duk da gidan yana kulle ne.

Tana cikin tunanin ne Jack ya bude gidan ya shigo. Jack abokin James ne na kud da kud. Shi kadai yake da makullan gidan James saboda amintar su, kuma shima ba aure ne da shi ba. Ya kan yi amfani da wadan-nan ranakun ya zo gurin Fadwa a wasu lokutan. Ya biya bukatarsa da ita.

Fadwa na ganinsa ta shiga farin ciki sabanin sauran lokuta da yake zuwa gareta. Ta tarbi Jack cikin murna ta bashi hadin kai, irin yadda bai taba samu ba. Sosai ta gajiyar da Jack sannan ta zare jikinta, ta bar shi zube a kan gado ta fada bayi na sashenta ta yo wanka. Sauri-sauri ta gama shirinta, ta tattaro kayan da take bukata, ciki hadda passport dinta. Da sanda ta lallaba ta yi ficewarta. Ta bar Jack can zube kamar kayan wanki.

Lokaci mai tsayin gaske ta dauka wajen fafutukar tafiyar ta'ta. Kasancewar bata shirya komai ba. Jirgin ma sai a lokacin ta nema. Hakan ya sa bata tafi ba sai karfe shida na yamma jirgin ya tashi.

Wohoho wannan ranar kam ku zo ku ga yadda murna da bakin ciki suke haduwa wa mutum daya a lokaci daya. Murmushi take a cikin jirgin kuma tana kuka. Cikin dare suka sauka birnin Kano. Bayan cire rai na shekaru shida, gashi ta dawo garin haihuwarta. Ta lumshe ido a hankali ta shaki daddadar iskar mahaifarta. Ta taki kasar da dukkan karfinta, zuciya cike da bururruka dabam-daban.

Babban abinda ya tashi hankalinta shi ne ganin Shugaba Habib a sahun masu jiran jirgin zuwa Holland. Yana tare da wasu 'yan mata goma sha daya. Sai murna suke suna zumudin barin kasarsu da nufin samo ci gaba.

A take abubuwan da suka shude suka fara dawo mata. Ta tuna da wan-can ranar. Ranar da ta kusa zamar mata ganin karshe ga Jihar Kano.

Ranar da ta zamo sila ga tarwatsewar shiryayyar rayuwarta. Ga kuma wannan azzalumin tsohon da ya yi mummunar illa ga maraicinta. A lokacin ta fahimci wannan ita ce sana'arsa. Fataucin mata, saka su karuwanci da kuma saida su tamkar bayi. A ranar ta sha kuka bayan ta yi kokarin boye kanta ga Alh. Habib tana kallo har jirginsu ya tashi. Inda ita kuma ta nemi taxi ta shiga zuwa babban gidan marayun, inda ya zama gida gareta. Kuka take sosai a cikin taxi din, tana takaicin yadda ta bar gidan tana cikakkiyar mace, yau gashi ta dawo cikakkiyar karuwa. Tausayin kanta ya kara kama ta. Ta tuna nasihohi da jan kunnen da Ummynta ta yi mata kafin tafiyar. Sai ta koma rushewa da kuka. Haka dai ta kasance har zuwa lokacin da mai taxi din ya shaida mata ya kawo ta inda ta bukata. Ta sauka ta kuma fidda kayanta. A lokacin babu kudin Najeriya a hannunta, dollars ta cire ta bashi ya karba yana murna ya tafi. Ita kuwa ta ja akwatin tana taku dakyar kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi gate din gidan nasu cikin matsanancin kuka...

*Nasmat* ✍

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Godiya ta musamman ga masu nuna so da kokarin bibiyar labarin 'YAR GWA-WAGWARMAYA babu shakka kulawarku ita take karawa Nasmat kwarin guiwa a dukakkanin al'amuranta. Na yarda babu kamar MASOYI a rayuwa. Ku ci gaba da so na, nima nan mai son ku ce* ```one love``` 😍

```page 5```

Tana da'da nufar kofar kukanta na kara tsananta. Wannan ne yasa mai gadin gidan fitowa da torchlight dinsa mai dogon haske. Ya dalla mata ita daga nesa tun kafin ta karaso inda yake, ya tambaye ta "wace ce wannan?". Cikin kukan ta bashi amsa, dan ta shaidi dattijon tace "Baba nice. 'Yarka ce Fadwan Ummy". "Fadwa?!". Baba Ilu ya tambaya cikin tsananin firgici. "Fadwa mutum ko fatalwa? Domin mu dai wadda muke da ita a nan Allah ya yi mata rasuwa." Fadwa ta koma fashewa da kuka "Baba nice fa, yaushe kuka sami wata Fadwa bayan ni? Yaushe kuka maida ni matacciya?". Ta yi masa tambayoyin da karfi cikin matukar mamaki.

Dattijon ya karasa fitowa daga gate din ya nufo ta, cikin tsananin mamaki. Yana mai kara haska fuskarta da fitilar hannunsa. Tabbas Fadwa ce. "Ya Allah!". Baba Ilu ya fada kana damki hannunta ya ruga cikin gidan, yana kwalla kiran sunayen iyaye da shugabannin gidan yana cewa "ku fito! Ku fito ga 'yar Amina ta dawo bata mutu ba. Ku zo, ku ga abin al ajabi ga Fadwa ta dawo a raye, wallahi bata mutu ba."

Maganganun Baba sun kara ma Fadwa duhun kai. Kenan ce musu aka yi ta mutu?

Kafin kace me mutane sun cika tsakar gidan, yara da manya. Tsofaffi da ma'aikata. Cikin masu son yin arba da Fadwa hadda Ummynta wadda ta kwashe fiye da shekara tana fama da ciwo, na hakurin rashin Fadwa da ta kasa yi. Tun bayan lokacin da labarin mutuwarta ya riske su.

Saboda hasken da yake kewaye da tsakar gidan kowa na iya ganinta, wanda babu makawa sun tabbata ita ce. Sai ko canji na jiki da girma da ta kara yi. Ummy ta fashe da kuka ta ruga ga Fadwa ta rungume ta. "Fadwa 'yata. Dama kina nan baki mutuba? Meya same ki 'yata? Sun ce mana kin mutu. Fadwa sun saka ni kukan da ban taba yi ba. Ashe baki mutu ba 'yata." Ta koma fashe da kuka ta kankame ta jikinta. Haka iyayen suka yi ta shafa fuskar Fadwa suna mamakin ganinta a raye. Daga karshe suka zarce zuwa ofishin shugaban gidan, wanda dama yana cikin ayarin da suka taru ganinta. Shi kuma ya bukaci su bishi zuwa ofishinsa. A can ne bayan kowa ya nutsu suka bawa Fadwa labarin yadda suka sami labarin mutuwarta a bakin Shugaba, Alh. Habib kenan. Wanda suke yiwa kallon Uba ga marayu da marasa karfi. Har ma suka dora mata da gagarumin tallafin da ya basu.

Bayan shugaban gidan ya kai aya ne, ita kuma ta fara basu labarinta tun daga tafiya har dawowarta bata boye musu komai ba. Ciki har da karuwanci da aka tilasta su yi, da kuma shaye-shayen da ta fada yi.

Hayaniya da koke-koke suka kaure a ofishin. Masu kuka na yi, masu jifar Alh. Habib da tsinuwa suna yi. Tsananin tausayin marainiyar ya kara kama su. A ranar su kam suka yarda da duk bayananta, suka sanya Alh. Habib a layin azzalumai masu ha'intar kasarsu da rigar karya. Ta kuma shaida musu har yanzu bai daina dibar 'ya yan talakawa yana kaiwa kasashen ketare ba. Ta gaya musu ta ganshi yau din-nan ya fita da wasu zuwa kasar Holland.

Ranar kam kowa a gidan sai da ya yi kwanan bakin ciki. Washe gari suka maka Alh. Habib kotu dan nemawa 'ya ya mata 'yanci da kuma nufin dakatar da shi daga wannan kazamar harkallar. Tsoro da firgici suka dirarwa Alh. Habib a lokacin da ya sami labarin wai wata daga cikin 'yan matan da ya fitar waje ta dawo har ma jagororin gidan marayun da take sun saka shi kotu. Sun ce asirinsa ya tonu yarinyar da ya ce musu ta mutu ta dawo gida bayan shekaru shida. Ta bar gida tana nutsatstsiyar budurwa ta dawo musu a rikakkiyar karuwa.

Hankalinsa ya yi mummunan tashi a ranar, sam bai tsaya yin cinikin yaran da ya tafi da su ba. Ajiye su kawai ya yi ya dawo Najeriya. Da saukarsa ya gayyato manya kuma kwararrun lauyoyinsa suka hadu a wani gidan gonarsa. Ya gaya musu cewa shi bai san komai ba game da zargin da suke masa, ba mamaki 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar dan ta bata masa suna. Ya umarce su da su yi, duk abinda ya kamata su lalata wannan case din. Dukkansu sun yarda da zancensa kasancewar duk kusancinsu da shi basu taba ji ko ganin wata alama da ta kusanta shi da wannan ba.

Haka aka fara gwa-gwarmayar shari'a. Shari'ar da ta dauki hankulan dubannin 'yan kasa. Wadan-da da yawan su sun fi yarda da maganar lauyoyin Alh. Da suka ce 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar don ganin sun bata mishi suna.
Chapter 3 · 0% Book details