← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka bangaren Asp Sauwam ma ya tashi da tsare-tsaren gudanar da bincike na musamman a cikin garin dan nemanta. Tun da ya samu tabbacin tana garin.

Hotel din nan na sharaton ta kuma komawa, saboda hasashenta ya bata Suhaima kwana zata yi a can. A bangaren cin abinci ta tsaya, inda ta yo odar abin karyawa ta fara ci. Hankalinta na kan mashigar wurin, kasancewar wajen gilas. Daga inda take zaune tana iya ganin duk wanda zai shiga ko zai fita harabar hotel din.

Wasa-wasa har karfe sha biyun rana ba labarin ta. Sai ta fara tunanin ko dai tun jiya ta bar hotel din ne? Da wannan tunanin ta mike ta biya kudin abincin da ta ci, sannan ta kama hanyar ficewa. Ranta ya sosu, sam bata ji dadin rashi ganin Suhaima ba. Domin shirinta na yanzu duk a kan karuwansa ne. Tafe take tana sake-sake a ranta.

Karaf! Ta ji ta yi karo da mutum wanda bata ma san daga ina yake zuwa ba...

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

```Wannan shafin tukuici ne ga babbar masoyiyar wannan labarin na``` *'yar gwa-gwarmaya* ```na gode sosai``` *Ikram* ```sakonni da yawan comment dinki sun nuna karara irin so da kikewa labarin. Ba ke kadai bace Iki, nima ina yinki sosai. Ina son mai sona. Allah dai ya bar so da kauna.```

```page 7```

Babu tsoro ko alamarshi a tattare da ita, ta dago. Sabanin wanda ta yi karon da shi. Alamu sun nuna ya tsorata matuka. Suka kafe juna da ido kowannen su na kokarin tuna inda ya san daya.

Ita ce ta fara tunawa, cikin abinda bai fi sakanni ba ta tuno da Ab'ha, (Abba kenan.) Mahaukacin masoyin class mate dinta Hamida a makarantar sakandiren government collage da suka gama. Duk da ya kara darjewa ya zama cikakken saurayi.

"Abba kai ne?". Ta tambaya tana nuna shi da yatsa. Ya gyada mata kai kawai ba dan ya gano wace ce ita ba. Sai kuma ya tuna da abinda yake tattalin da suka zube yayin karon da suka yi. Da sauri ya rankwafa ya fara tattare takardu da wasu hotuna da suka fadi a hannunsa.

Hakan yasa ita ma hankalinta ya koma kansu. Sai dai kafin ganinta ya sauka garesu ya riga ya gama tattarewa, daya kawai ta gani wanda ya dauko a karshe kafin ya saka a file. Ta girgiza, ta kuma cika da mamakin ganin hoton tsohuwar budurwarsa Hamida daga ita sai pant da bra, tare da wani ba'amurke dake sanye da gajeren wando a bakin ruwa. Ta tabbata ba a dade da daukar wannan hoton ba. Ta kuma kallonsa da mamaki tace "Abba har yanzu baka rabu da Hamida ba?" Wanda ta yiwa tambayar ya kuma zare ido. Duk da alamu sun nuna ya tsorata da tambayar sai dai karfin soyayyarsa ga budurwar tasa babba ne.

Ya kalle ta cikin ido yace "in dai ni zaki kira to ki hada sunana da nata. Kamar yadda yake tun farko, ki kirani Ab'ha, bani da sunan da ya wuce shi. Rabuwa da Ha'ab kuma sai dai bayan rai. Na rantse ko zan mutu sai na rabota da wannan kasar da kuma wannan rayuwar. Ba zan daina sonta ba. Still ina sonta a haka".

Yana gama fadin haka ya figi jiki ya yi gaba, kamar a fusace. Da sauri Fadwa ta sha gabansa "Ab'ha wai baka gane ni bane?" Ya kuma kallonta irin kallon da ya mata dazu. Tabbas yana ji ya san fuskar amma gogewarta ta hana shi gano ta farat daya. Ta mari kuncinsa da wasa tace "kai mahaukaci Fadwa ce fa. Class mate din Ha'ab dinka a Government collage".

Ab'ha ya saki dukkan fara'arsa yace "Fadwa?! Dama kina raye?". Bata tsaya bashi amsa ba ta kama hannunsa, ta ja zuwa hanyar fita hotel din, domin ta tabbata abinda yake bibiya nada alaka da bincikenta. Yana da muhimmanci gareta da bincikenta a yanzu. A karamin nazarinta ta lura har yanzu yana bibiyar tsohuwar budurwarsa. Wadda aka fitar da su tare zuwa kasar England. Tabbas zai mata amfan...

Tirjewar da ta ji Ab'ha ya yi ne ta katse mata tunani. Ta kalleshi da mamaki "ya dai?". "Ba zan fita wajen nan yanzu ba Fadwa. Bibiyata ake. Yanzun ma gudowa na yi daga harin wasu 'yan ta'adda". Kafin tace wani abu sai ganinsu suka yi a gabansu.

Wasu tsagerun 'yan ta'adda ne kusan su bakwai. Hannayensu rike da adduna. Ab'ha ya juya da zummar guduwa, Fadwa ta kara damke hannunshi dake cikin nata. Idonta cikin a kan masu bibiyarsa. Hakika ta shaide su, kamar yadda su ma suka shaide ta.

Yaran Shugaba ne. Ta san su farin sani, domin sun sha kai mata farmaki bisa umarnins... Kafin ta kai karshe ga tunaninta babbansu ya karaso wajen cike da izza. A lokacin kuma suka fara magana "kai Oga. Ka ga wata sa'a, wlh ga Fadwa nan Yar gwa-gwarmayar nan". Jin hakan yasa Chaka ya fito da karamar bindigarsa, tare da saita ta da ita. Yau kin gamu da ajalinki Fadwa, kwanankinki sun kare abin farauta'ta".

Gaba daya suka saka dariya, kafin ta katse su cikin daga murya.

"Karya kake banza kare, ko da Fadwa zata mutu to ba dai a hannun karnuka irin ku ba". Kafin dukansu su yi wani yunkurin sai suka ji wucewar harsashi da karfi ta kansu. Ya wuce ya daki gilashin kofar shiga sashe na biyu na Hotel din. Asp Sauwan ne da tawagarsa.

A take yaran Chaka ma suka fiddo nasu bindigogin, suka fara maidawa jami'an tsaron martani. Suna kokarin ficewa daga wajen. Sai ko aka shiga musayar wuta.

Ganin haka yasa Fadwa jan hannun Ab'ha suka kauce a gurin.

Cikin sauki suka fice daga Hotel din. Suka bar su nan suna aikawa junansu harsa-sai.

Zan ci gaba...

*Nasmat*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Slm masoya, ma biya labarin 'yar gwa-gwarmaya. Hakika shafina na yau zai kasance na musamman domin zan sadaukar da shi ne ga wata ta musamman. FATIMA USMAN kanwata. Ina alfahari dake da kuma kwazonki. Fatana shi ne Allah ya kara haskaka min haska-kakkiyar kwakwalwarki amin. Ana matukar tare. 🤝*

```page 8```

Lokaci mai tsayi suka dauka suna musayar wutar, kafin daga bisani 'yan ta'addar su sami nasarar bindige police daya. Su kuma 'yan sandan suka kashe musu mutum biyu suka kama wasu biyun. Hudunsu kuma suka sha dakyar.

Bayan Fadwa da Ab'ha sun fita wajen, bata nufi gidanta da shi ba. Wani Hotel din ta samu suka shiga. Ab'ha wanda gaba daya hankalinsa yake a tashe ya kalleta bayan sun zauna yace "wai dama ke ce 'yar gwa-gwarmayar da nake jin labarinta?." Ta sakar masa murmushin nan nata tace "ni ce." A takaice. Tana kurba lemun da suka saya. Mamakinsa ya kara bayyana yace "kaina yana cikin duhu dan Allah ki bani labarin rayuwarki. Kin san bana kasar ina can ina bibiyar ruhina a kasashen duniya."

Ta yi murmushi mai bayyana sigar tausayawa ga wanda aka yi wa shi. Tace "Abba kana bani tausayi sosai. Hakika so ya yi maka mugun dabaibayi. Yayin da kaddara ta yi wa rayuwarka karan tsaye. Na tabbata ba zaka iya barin ta ba. Amma ta yaya kake ganin zaka iya samunta a wannan rayuwar?".

Ya sauke numfashi kansa yana sunkuye a kasa. Hakika yana cikin damuwa da manyan hadarurruka game da wannan burin, amma giyar so sam, bata nuna mishi zai rasa. A kullum zai samu cikar buri yake gani. Bayan gajeren nazarin maganganunta ya dago kansa cikin sanyin jiki yace "bani da zabi Fadwa. Kaddarata kenan. Ba sai na gaya miki ba, abu ne da kika dade da sani. Son Ha'ab a cikin jinin jikina yake, ba zan iya hakura da ita ba. Ki sani saboda ita na rasa kowa. Abbanmu ne kawai yake tare da ni yanzu. Amma Umma da kannena duk sun tsane ni saboda son ta, da nace matan da nayi. Fadwa na sha yin addu'a, amma son ta bai taba raguwa a zuciyata ba. Kullum hauhawa yake. Bacin sabani da familyna kin ga halin da rayuwata take ciki. Farauta ta ake tamkar nama. Rayuwata ake nema ruwa a jallo."

Ya sarara yana shafa file din gabansa. Bata ce komai ba sai kallo da kara nazarinsa da take yi. Ya ci gaba. "Bayan dogon bincike na gano gaskiya. Da gaske ne Ha'ab karuwanci take yi a can. Sabanin karatun da shugaba yace suna yi. Koda ba ke ce 'yar gwa-gwarmaya ba ina da burin nemanta a matsayina na mutum na farko da ya gano gaskiyarta kuma ya yarda da ita. Wlh Fadwa wannan Shugaban azzalumi ne, fataucin yaran mutane shi ya mayar sana'a. Kin ga Ha'ab yanzu ta manta da kowa. Bata tuna kowa, ta mance da shakuwa da zurfin soyayyarmu. Ta manta Abba mahaukacinta. Kaina ya gama kullewa, na rasa mafita, ina son ta har yau ina kaunarta. Na kasa nisanta kaina da ita. Na kasa ficewa daga lamarinta, duk da an nuna karara za'a kashe ni saboda bibiyarta.

Ki kalli hotunan nan, rayuwarta take cikin kwanciyar hankali. Shekara daya ina bin rayuwarta ba da saninta ba. Rana daya kuma ta farko da na bayyana kaina gareta cike da yakinin zata saduda saboda ni. Tar-bar da ta yi min shi ne sanar da shugaba ina bibiyarta. Tun a England aka fara neman raina. Dakyar na dawo Najeriya, gashi nan din ma ban tsira ba. Kamar yadda kika kudurta nima na kudurta. Koda zan mutu sai na tona asirin munafikin tsohon nan. Sai na sa shi dana sani. Na fara hada gagga-gaggan hujjoji a kansa. Na kuma ji dadin haduwa dake."
Chapter 5 · 0% Book details