Sashe 14
Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban san ya kike ji ba a matsayin ki na wadda aka batawa rayuwa, aka raba ta da mutuncinta ta karfi. Amma na san yadda ni nake ji a matsayina nan yaya, kuma dan uwa ga wadda irin hakan ya faru da ita. Uwa ce kawai ban san yadda ita kuma zata ji ba." Ya koma matse idonsa domin rage musu nauyin hawayen dake ta turereniya da juna a cikin su.
"Fadwa ki dubi Allah ki dubi halinda mu da Momynmu muke ciki ki dawo mana da Anisa. Wallahi na rantse miki a yanzu bana ganin laifinki. Mahaifina shi ne ya assasa komai kuma shi ne mai laifin. Na roke ki da Allah ki dawo da wannan 'yar ga mahaifiyarta." Ya karashe maganar cikin rishin kuka. Take ta ji wani iri ba dadi. Bata juyo ba, kuma bata ce komai ba. Ta bude komai da sauri ta fita. Baffa kuwa kansa ya daga sama ya ci gaba da kuka cikin kuna da zafin zuciya. Kukan da yake jin yinsa zai iya rage masa wannan zafi da nauyin da yake ji bisa kirjinsa.
Da zuwa ta fada kan faffadan gafonta, mai laushi da kyan shimfida. Ta lumshe manyan idanuwanta tana tariyo abinda ya faru, sam bata yi tsammanin yaron nan zai fahimta kuma ya sauko cikin sanyi haka ba. Mamakinta shi ne yaushe ma Ab'ha ya iya wannan jawabin da kokari na ganar da da laifin ubansa? Tunawa da maganganunsa yasa wasu siraran hawaye zariya kan kyakkawar fuskarta. Sosai kalamansa suka fama mata raunin zuciyarta, wanda ya fara bushewa. Tunawa ta yi da Ummynta uwar riko ba ma wadda ta yi dawainiyar kawota duniya ba. Ta amsa sunan uwa domin har ta koma ga Allah da tabo na ciwon abinda aka yiwa 'yarta duk da cewa ta dawo gabanta.
Sai tausayin mahaifiyar su Baffa ya kamata, hakika zata fi Ummy bakin ciki, domin kuwa ita Ummy bata ma gani da idonta ba. Ita kuwa ta gani, yadda aka keta haddin 'yarta gudan jininta sannan kuma aka badda ta ta inda basu san inda take a duniya ba. Kunkanta ya kara tsananta, tasayinsu yasa ta ga bata kyauta ba. Ta san duka abinda take tana yi ne domin ramuwa ga Shugaba, amma wannan hukuncin ya yi tsauri ga ahli. Domin kuwa shi uba ne kawai, ba zai taba jin kwatankwacin yadda uwa zata ji ba.
*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________
```Page 20```
Ranar kam kwanan bakin ciki da tausayin mahaifiyarsu Baffa ta yi. A ranta tana ganin rashin kyautarwarta, domin a ganinta hukunci na mai laifi ne. Su kuma basu san komai ba. Washe gari tun da asuba ta bar gidan bayan ta yiwa Ab'ha sallama da kara jaddada masa ya kula da gida. Shi kansa bai san inda ta nufa ba. Sai dai bayan fitarta ta kira waya ta umarce shi da ya kwance Baffa ya bude shi, shima ya sake cikin gidan kamar ragowar 'yan matan nan. Duk da ya ji mamakinta na yin hakan amma abun ba karamin dadi ya yi masa ba, domin kuwa yana jin dadin zama da Baffan. Guy din yana da saukin kai da saurin fahimta.
*Washe gari da dare*
Suna cikin yin kalacin dare suka ji an budo kofa an shigo. Fadwa ce ta shigo cikin wata shiga ta atamfa England dinkin zamani, na riga da sket. Kanta yane da wani karamin gyale sky blue kalar kayan jikinta. Hannunta rike da na Anisa wadda ta sha jinin jikinta tana jiran ganin inda aka kawo ta da kuma abinda zai koma biyowa baya. Ab'ha da Baffa suna kan danning suna cin abinci. Yayin da su kuma 'yan matan suke baje a kan Capet din falon suna gabatar da nasu kalacin. Ganin Fadwa da wadda ke tare da ita yasa ko-wannensu dakatawa da abinda yake yi suka zuba musu ido cike da mamaki da al'ajabin wannan ba zata.
Anisa kuwa ganin babu idon sani a gurin ya saka idonta suka fara cikowa da kwalla. Daya bayan daya take kallonsu, ai kuwa karaf idonta suka suka kan dan'uwanta gudan jininta Baffa. Wani uban tsalle ta daka ta kwace hannunta daga cikin na Fadwa ta nufe shi da gudu tana mai kiran sunansa da karfi. "Yaya Baffa!". Ta rungume shi tare da sakin wani irin kuka mai taba zuciya da sanya ta nutsuwa. Baffa da ya gama sandarewa idonsa kyar a kan Fadwa, ya kasa dauke su a kanta ya kuma rasa kalmar da zai furta mata a matsayin godiya ko nuna farin ciki bisa wannan gagarumin taimakon da ta yi masa.
Hannayensa ya daga dakyar ya rufe Anisa dake kankame da kirjinsa, ya damke ta tsam, yana ji kamar mafarki yake yau ga kanwarsa a gabansa. "Anisa..." Ya kira sunan cikin wata raunanniyar murya da ta fito can karkashin makogwaronsa, yana shafa kanta. Kukanta ya tsananta ta kankame shi tana son magana bakinta na rawa, a hakan ta daure ta fara maganar. "Yaya nan kuma ina ne? Me kake yi a nan? Yaya dan Allah ka dauke ni mu je gida, wannan da kake gani azzaluma ce yaya itace ta..." Hannun da ya dora a kan lebenta shi ya dakatar da kalaman dake fita bakinta. Ta dago kai ta kalle shi, sai ta ga yana girgiza mata kai idonsa cike da kwalla.
Yasa hannu ya janye ta daga gabansa ya fara takawa daga inda yake zuwa inda Fadwa take tsaye tana kallonsu. Har a zuwa lokacin babu wata kalma da ya ji ta zo masa wadda ta can-canta ya yi amfani da ita wajen godewa Fadwa. Sai da ya zo daf da ita sannan ya tsaya ya zamana ko-wannensu na iya jin numfashin dan'uwansa. Rashin sanin abin yi yasa ya sauke girmansa da ji da kansa ya tankwashe kafarsa ya gurfana a gaban Fadwa cikin matukar girmamawa da darajawa ya kama kafufuwanta yana son furta mata kalmar godiya amma ya gagara. Wani irin shokin ta ji ya shige ta tun daga kan yatsun kafar tata har cikin gashin kanta. Da sauri ta ja da baya tana mai girgiza masa kai alamar ya bari. Bata yi magana ba ta raba shi ta wuce da sauri ta shige dakinta kana ta rufo kofar.
Anisa kuwa tsaye kawai ta yi tana kallon ikon Allah. 'Yan matan nan sun zagaye ta suna mata barka da dawowa gida amma ko jin su bata yi. Idonta na kan yayanta da abinda ta ga yana kokarin yi ga wadda ta ruguza mata rayuwa. Kuka ta fashe da shi ta karasa gareshi "yaya kanka daya kuwa? Ka kuwa san wace ce wannan? Fadwa ce fa, wannan 'yar gwa-gwarmayar da ta d'ai-d'aita rayuwata ta maida ni karuwa, kuma abin ki fasik..." Baffa ne ya yi saurin toshe bakinta yana girgiza kai. Ransa a matukar bace ya fara magana bayan ya kama hannayenta.
"Aa kanwata, karki ga laifin fadwa bisa abinda ta aikata gareki. Domin kuwa babban mai laifin shi ne Dadynmu. Dady da kike gani shi ne cikakken azzalumi, wanda ya kai makura ga lalatawa da tarwatsa rayuwar 'yayan mutane..." Ya kwashe komai da ya ji game da mahaifinsu da abinda ya yiwa Fadwa ya gaya mata, ya kuma nuna mata hujjojin da shima aka nuna masa, ga uwa uba shaidar kan-kat! Wato wadannan 'yan matan da suke masa kasuwancin karuwanci.
Kuka sosai Anisa ta yi, wanda har yasa ta tsani ci gaba rayuwa a matsayin 'yar Alhaji Habib Shugaba. Tsananin son 'yan uwanta da Momynta ne kadai yasa take son ta rayu. Ba dan tana da su ba da yau ta zama daya daga cikin jerin wadanda bakin ciki yasa suka kashe kawunansu. Ta yi kuka, ta yi gumji, har ta dawo babu murya kuma babu hawayen.
*Asibiti*
Karfe bakwai da rabi na daren, yana zaune a kan kujerar robar dake fuskantar gadon majinyatan. Hannunsa rike da hannunta wanda aka saka mata roba ta karin ruwan jiki. Faisal kenan kanin Baffa kuma yayan Anisa d'a ga Hajiya Laurat matar Alhaji Habib Shugaba. Idonsa a kan uwar tashi dake kwance tamkar babu rai a jikinta. Banda kuka ba abinda yake yi. Addu'a kam bai sai adadin wadanda ya yi ba. Zaune kawai yake amma shi kansa hoto ne kawai ruhinsa ya balle izuwa duniyar tunanin wannan iftila'in da ya afka musu. Ga Momy kwance a asibiti, Baffa ya bata, ita Anisa ba a ma san inda take ba. Wannan wace irin masifa ce. Kofar dakin aka budo aka shigo, ya dago kansa dakyar ya zubawa mai shigowar ido. Mai gadin gidansu ne Izike. Har zai dauke idon nasa ya yi gaggawar komawa da su ga kofar, saboda ganin wadanda ke biye a bayan Izike. "Anisa! Yaya Baffa!!". Ya ambaci sunayen cikin tsananin mamaki da tan-tamar sune ko dai idonsa ne suka fara yi masa gizo?
Anisa ce ta tabbatar masa da su din ne. Ta hanyar rugawa da gudu ta kankame shi tana kiran sunansa "yaya Faisal". Firgigit Hajiya Laurat ta farka daga nannauyan baccin da take bayan ta dawo daga suma. Kamar a mafarki ta ji ana kiran sunayen 'yayan nata. Ai kuwa tana yin arba da su ta shiga kiciniyar cire robar dake hannunta ta mike zaune.
Gaba daya suka yi kanta suna kokarin kwantar da ita. Ta ja Anisa zuwa jikinta ta rungume ta. Wani kuka mai karfi ya kwace mata a dalilin tunawa da yadda ta ga ana wulakanta 'yar tata a fai-fan video ana keta haddinta. Ta rumtse ido da karfi tana kaico da alawadan kasancewarta matar shi.
Bata san lokacin da bakinta ya furta kalmomin ba. "Allah ya isa tsakanina da kai Alhaji, har abada ba zan yafe maka ba. Ka cuce ni ka cuci zuri'armu".
*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________
```Page 21```