Sashe 15
Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya yaran suka zuba mata ido cike da mamakin jin abinda take fada musamman Faisal da bai san komai game da mahaifin nashi ba. Su kuwa Baffa da Anisa mamaki suke ta yaya Momy ta san laifin na mahaifinsu ne? Waye ya sanar da ita?... Suna cikin wannan tunanin suka jiyo Faisal yana jerewo Momyn tambayoyi cikin wata rikitacciyar murya mai dauke da dimuwa. "Wane Alhajin kike nufi Momy? Ba dai Dady ba ko? Me Dady ya yi miki wanda har kike cewa ba zaki yafe mishi ba Momy? Shin wace cuta kike ganin ya yi mana a matsayinmu na zuri'rku?
Momy kam sai lokacin ta san maganar ciki ta fito fili. Sam bata san a fili ta furta kalaman ba, amma a ganinta laifin Alhaji Habib ba abin boyo bane. Matsalarta daya ita ce ta yaya zata sanar ta kuma fahimtar da yaran laifin mahaifinsu?. Cikin kunci da tsantsar takaici ta jijjiga kai "kwarai kuwa shi, mahaifinku nake nufi Faisal. Babanku mutumin banza ne, azzalumi mai boye aibu da alkhairai. Shi kare ne da fatar kura, fuska biyu ke gare shi. Wannan halin na mahaifinku abin tir! Da Allah wadai ne". Ta kai hannu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa. Sannan ta ci gaba "ya zama dole in gaya muku babban aikin mahaifinku shi ne safarar 'yan mata. Kananun yara 'yan kasa da shekara ashirin yake diba yana sayarwa turawa suna yin abinda suke so da su". Ido waje Faisal ya gurfana gaban gadon da Momy take kai yana kallon fuskarta. A lokacin ji yake kamar ta saki murmushi tace duk abinda ta fada wasa ne. Ko kuma ma a ce wata zautuwa ce ta kamata ta fadi hakan a kan amintaccen mijin nata mafi soyuwa ga zuciyarta. "Momy!" Ya kira sunanta a razane yana jijjiga kafarta wai ko Allah zai sa ta dawo hayyacinta ta karyata abinda bakinta ya fada a kan Dadynsu.
Ganin babu sauyi ko alamar karaya a fuskarta yasa ya saki kafar tata da sauri ya koma gun yayansa da ya gani zaune daram kamar bai ji abubuwan da Momyn take fada a kan Dadynsu ba. Hannayensa ya kama cikin wani yanayi yake girgiza shi "yaya shin kaima kana jin abinda take fada ko da kunnuwa ne suke gaya min karya?" Ganin yayan nasa bashi da niyyar yin magana yasa ya juya ya koma kan kanwarsa "Anisa, Anisa baby kina ganinsu ko? Ita tana fade-fade shi kuma ya yi shiru. Shin ba zasu yi min magana ba? Kanwata kema kin ji me Momy take fada ne?". Wani matsanancin kuka Anisa ta fashe da shi ta fada jikin Faisal ta rungume shi ta tabbatar a yanzu su ababen tausayi ne. Bakin ciki kuwa su duka sun daura aure da shi. Tsoro da fargaba sun hana shi iya motsa gabban jikinsa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Abinda ya shiga furtawa kenan a lokacin da ya fahimci al'amarin da'iman ne. Kansa ya yi masa nauyi, dakyar ya kai hannunsa ya dafe shi. Ganin zai sami matsala ya sanya Baffa saurin mikewa ya janyo shi jikinshi da shi da Anisa duka ya hada ya rungume su. A ransa yake kwatantawa shikenan sun shiga maraicin rashin uba. Cikin tattausan lafazi yake kara tabbatarwa kanin nasa maganganun mahaifiyarsu. Ya dora masa da wadanda ya ji kuma ya gani. Haka ita ma Momy ta tabbatar musu babu ko shakka halayyarsa ce domin ita ma ta ji da kunnenta yana waya kan zai tura yaran ga wani bature dan kasar rasha.
Dukkaninsu kuka suke suna jajantawa kansu. Tsananin tsana ta bakin cikin halin uban nasu ya cika zuciyoyinsu. Momy ce ta yi karfin halin tsayar da nata kukan ta soma rarrashin su.
Ta kuma umarce su da su yi hakuri su danne zukatansu su ga karshen gudun ruwansa. A yadda tace bata bukatar ko-wannensu ya nuna a fuska ko a bayyane cewa ya san wani abu game da shi. Tana bukatar karin lokacin da zai yi dai-dai domin tarfa shi. Cikin kunan rai ta karkare zancen da cewa "idan har Alhaji bai fuskanci hukunci kan laifinsa ba to nima ban can-canci in amsa sunan 'ya mace kuma uwa ba". Gaba daya yaran suka jinjina kai cikin jimami. Karfe tara da mintuna ya dawo Asibitin dauke da ledoji masu kunshe kayan marmari da drinks. Mamaki ne ya bayyana karara a fuskarsa na ganin yaransa biyu da suka bata sun dawo a lokaci daya.
Bai iya boye farin cikinsa na ganinsu ba duk kuwa da yana cikin damuwa. Haka ya zauna da yaran sama-sama domin hankalinsa ya riga ya kasu kashi-kashi. Kasancewar yau ta kama assabar, washe gari kuma lahadi, yayin da rana ta gaba zata kasance litinin kuma ranar da alkalin babbar kotu yake bukatar ganinsa a gabansa domin ya kare kansa bisa zargin da ake masa. A gefe daya kuma ga babbar barazanarsa Fadwa, wadda ta gagare shi, izuwa yanzu kuma bai san me take shirya mishi ba. Wannan ne yasa ga baki daya ya rasa nutsuwarsa domin kuwa shi mara gaskiya aka ce ko a ruwa gumi yake yi. A daddafe ya samu ya yi musu sallama ya bar Asibitin bisa bada uzurin cewa zai shiga wani zama na gaggawa da shugabannin kananan hukumomi.
*Mai tama*
Fadwa ce tare da Ab'ha a dakinsu na harhada bayanai da ajiye duk wani abu mai muhimmanci. Sun dukafa sosai ga aikin da suke yi na tattara bayanai da bidiyoyin da suka samu daga wajen 'yan matan nan na Alhaji Habib da ya tura kasashen duniya. Dukkaninsu suna cikin gagarumin farin ciki na samun nasa, wanda akalla sun san ko ba a sami wasu ba wadannan hujjojin kawai sun isa su daure Shugaba.
'Kirrrr...!' Wayar Ab'ha dake ajiye a gefen hannunsa ta dauki ringi, alamar wani yana son magana da shi. Ganin number bakuwa bai bashi mamaki ba kamar yadda ya ganta da alamar kari (+) wato dai number ta kasar waje ce. Shiru na dan lokaci kafin daga bisani ya daga wayar da sallama. Zumbur ya mike tare da dora hannunsa kan kirjinsa, saboda bugawar da ya ji yana yi. Fadwa ta zuba mishi ido kawai tana kallon shi. Shi kuwa muryar Hamidarsa daya ji cikin kuka tana ambaton sunansa yasa gaba daya ya rasa nutsuwarsa. "Ha'ab?!" Ya kira sunanta cike da son tabbatarwa. Ta amsa da sauri tana share hawaye kamar tana gabansa. "Abba ka yafe ni ka yi mini aikin gafara. Hakika na aikata kura-kurai da yawa a rayuwata, amma a cikinsu babu wanda ya kai kin ka da na yi. Na yarda kin masoyi babbar masifa ce, Ab'ha na tuba ka yafe min. Na san zaka yi mamakin ji na a wannan lokacin to ba yadda na iya ne. Alhaji Habib ya cuce ni. Ya maida ni baiwarsa mai bautar da rayuwarta a banza. Duk iya zaman da na yi da shi bai gani ba. A kan wani karamin kuskure da na aikata masa yasa ana farautar rayuwata. Ni yanzu ban damu da kaina ba, damuwata daya ita ce juya maka baya da na yi a lokacin da kake matukar kaunata. Na dauki alkawarin sai na tozarta rayuwarsa kanfin ya cimma nufinsa a kaina. Gobe zan shigo Najeriya, zan kuma zo da gagga-gaggan hujjojin da zasu daure shi iya rayuwarsa. Ka tare ni karfe bakwai dai-dai jirgin safe zan biyo". Duk wannan dogon zancen ta yi shi ne wani na bin wani. Sam bata bada wata dama ga Ab'ha ya yi magana ba har saida ta zo karshe.
Cikin sarkewar murya yake amsa mata da "Sikenan Allah ya kai mu goben". Dif! Ya katse wayar ya zauna kan kujerar da ya tashi a kanta. Idonsa a kan fadwa cike da murna yake sanar mata Ha'ab ta yi nadamar abinda take zata kuma dawo gida. Ya gaya mata duk abinda ta fada masa.
Fadwa ta jijjaga kai, tana nazarin maganar. Kafin ta kalle shi tace " Allah ya kai mu goben lfy". Iya abinda tace kenan ta ci gaba da aikinta.
Washe gari tun da ya yi salla zumudi bai bar shi ya koma kwanciya ba. Shi kansa a wasu lokutan yana mamakin irin yawan so da kaunar da yake yi wa Hameeda. Duk da ya san halin da take ciki dai-dai da rana daya bai taba jin sonta ya ragu a zuciyarsa ba. Yau yana cikin farin cikin da ya debi shekaru bai yi kwatankwacinsa ba. Duk rawar kan da yake yi Fadwa na lura da shi, amma bata tanka shi ba. Haka ya kammala shirinsa karfe bakwai saura kwata ya fita gidan ya nufi airport.
Karfe bakwai dai-dai jirgin Dubai mai dauke da fasijoji dari da sittin ya dira a babban filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Kano. A cikin jerin mutanen dake fitowa daga jirgin ya hango ta cikin shigar doguwar riga baka hade da mayafinta. Ta kara kyau ta murje, ta cika bul-bul da ita gwanin sha'awa. Ab'ha ji ya yi kamar ya ruga ya rungume masoyiya abar so da hangen ruhi da gangar jikinsa. Amma sai ya daure ya jira isowarta. Tana ganinsa ta fara sharar kwalla sannan ta saki jakar hannunta ta isa gareshi ta rungume shi tana ambaton sunansa cikin raunin murya.
Ab'ha kam kusan rasa ji da ganinsa ya yi a lokacin, saboda wani irin shauki na masoyan da a baya suka cire rai ga samun ababen son nasu. Dakyar ya iya raba jikinshi da nata yana dai-daita tsayuwa ya yi mata barka da isowa. Har zata tari taxi ya dakatar da ita yana sanar mata cewa ai da mota ya zo. Hakan yasa ta bi bayansa zuwa inda motar take a ajiye.