← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A take kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai tana fadin "wallahi nima na yi nadama, na yi matukar da na sanin kasancewa haka. A zamana a hannun wannan abokiyar karatun tawa na kwana daya, ta ganar da ni abinda a baya ban sani ba. Ta tunatar da ni abinda na sani kwakwalwata ta yi watsi da shi. Ta ankarar da ni wata daraja da nake da ita wadda ni da sam ban san ina da ita ba". Ta saki kuka wiwi kamar wadda ta rasa uwa da uba lokaci daya.

Cikin matsanancin firgicin da bai taba shiga ba ya mike tsaye bakinsa na rawa hannu na karkarwa. Ya rasa wata kalma, ya rasa ko wace kalma da zata karyata wannan abin da Fadwa ke shirin aiwatarwa wato toma masa asiri. " karya suke, gaba dayansu karya suke. Wane ne ya biya ku ku kulla min sharri? Har nawa aka baku da zaku tsaya ku dage wajen tozarta mutum mai mutunci kamata. Ya mai shari'a walla..." Tasawar da mai Shari'a Musa ya daka mishi ita ce ta tsayar da kalominshi. Alhaji Habib kenan da ya yi matukar fita hankalinsa. Jikinsa ya hau tsuma kamar mai shirin kamuwa da ciwon barin jiki. Ya koma ya fada kan kujerar da ya tashi a kai gumi na bin gefen saje da jijiyoyin wuyansa.

Daga can wajen kotun kuwa kara da kururuwar wani dattijo ce ta cika mutanen dake wajen har yana kokarin hana su jin abinda ake fada daga cikin kotun. Hakan yasa mutanen dake kusa da shi rufuwa kansa suna tambayar dalilin kukansa. Tsohon cikin sautin kuka ya fara magana "mun shiga uku wallahi 'yar dan uwana ce Hameedatu. Tun da ta bar kasar nan da sunan ci gaba da karatunnan ana murna, bata koma dawowa ba. Iyaye na ta nemanta ta dawo ta yi aure ta ki, babu zaryar da bamu yi a gidan Alhaji Habib ba amma atafau yace sai ta kammala karatu sannan zata dawo. Ashe azzalumin ya san abunda take shukawa a can. Allah ya isa munafiki ba zamu taba yafe maka ba". Kuka sosai Tsohon yake yana doka tafukansa a kasa saboda tsabar bakin ciki da takaici. Ya ciro wayar hannunsa ya fara kiran yayansa wato mahaifin ita Hameedan. Mutanen dake wajen kuwa jikinsu ya yi sanyi, hankulan wadanda suka bada imaninsu ga Alhaji Habib sun fara tashi. Domin kuwa sun fara tabbatarwa duk abinda ake zargin nan gaskiya ne.

A cikin kotu kuma mai Shari'a Musa ne ya buga gudumarsa dan neman daidaito da nutsuwarsu. Bayan duka sun tsagaita da maganganunsu ya maida kallon shi ga Hameeda da kanta yake kasa yace "ke yarinya meye gaskiyar abinda wannan ta fada game da ke?". Shiru ta yi hawaye na bin kuncinta, ba tare da tunanin goge su ba ta fara magana cikin nadama marar amfani. "Kwarai haka ne ya mai shari'a, duk abinda ta fada gaskiya ne". Ta kwashe komai game da abinda ya shafi rayuwarta a can ta gaya musu...

Tana dasa aya Alhaji Habib ya yi zumbur ya tsallaka kujerun dake bayan nasa, ya kade rigarsa ya zuba da gudu...

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Na yarda so shi yake kawo kauna. Abinda kuke nuna min kauna ce ziryan masoyana. Ina sonku ina kaunarku ina matukar jin dadin kulawar da kuke nuna min. Ubangiji ya albarkaci zumuncin dake tsakanina da ku gaba daya amin. 👏*

```Page 27```

"Arrest him". Muryar alkali Musa ta ratsa kotun cike da amsakowa. Kafin ya kai ga kofar da zata sada shi da wajen kotun jami'an tsaron da suke tsaitsaye a ciki suka zagaye shi. Cak! Ya ja ya tsaya yana maida numfashi da kokarin daidaita shiga da fitar numfashin nasa, yana zare ido kamar wani bokon duniya. A yadda yake tsayen ji yake kamar a mafarki ne, zuciyarsa ta kissima mishi ina ma ace mafarki yake yi? Da kuwa ya mallakawa duk wanda ya tashe shi abinda yake da shi a duniyar nan. Wannan wace irin bakar rana ce ta zo mishi? Ta yaya hakan zata faru da shi farat daya?' Yana cikin wadannan nazarce nazarcen ya fara jin sautin ihun mutanen dake wajen kotun suna jefo shi da munanan kalamai marasa dadin ji. Tamkar an yagi fatar kirjinsa an murza masa gishiri, haka ya ji wani irin zafi da radadi sun ziyarci zuciyarsa. Ya rumtse idonsa da karfi yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Habib na cuci kauna". Ya fada lokacin da yake dafe kansa da hannayensa guda biyu cikin matsananciyar Dana sani.

A cikin kotun ma hayaniyar ce ta kaure mutane suka mimmike tsaye suna la'antarsa suna nunashu da hannu kamar zasu rufe shi da duka, a cikinsu hadda manyan abokanansa 'yan siyasa da sanannun 'yan kasuwa. A kokarinsu na ganin sun wanke kansu kar a zarge su kan wannan mummunan laifin nashi da basu ma san yana aikatawa ba.

Lokaci mai tsayi aka dauka a hakan, yayin da jami'an tsaro suka dawo kokarin kare Shugaba daga fushin 'yan kallon shari'ar dake cikin kotun. Dakyar alkalin ya samu nasarar tsawatarwa game da hayaniya da rudanin. Alhaji Habib kuwa ya yi tsuru tsuru a gaban jama'ar da a da suke daukarsa a matsayin jigonsu kuma uba, jagira ga ragamar rayuwarsu. Alkalin ya yi gayaran murya, sannan ya maida kallonsa ga lauyoyin Alhaji Habib yace "ko a cikin ku da akwai wani mai ja game da wannan shaida da ta gabata?". Dukkansu suka yi kasa da kansu cike da jin kunyar kasancewarsu masu kariya a gareshi. Suka ce "babu". Alkali Musa ya kalli Fadwa dake tsaye yace "zaki iya ci gaba da gabatar da shaidannunki yarinya". Ta yi godiya ga kotun sannan ta dora da kiran sunayen 'yan matan nan. Wadanda dukansu babu boyayya a cikinsu. Manya ne kuma sanannun karuwai, wadanda mafi yawan mutane suka sani a cikin garin Kano. Daya bayan daya suka gabatar da kansu da ayyukansu, da kuma alakar dake tsakaninsu da Alhaji Habib. A karshe suka rufe da bada gamsassun hujjojinsu masu bada tabbacin abinda suka fada din. Na faro hotuna ne da video wadanda suka yi dauka a sace idan suka hadu da shi Alhaji Habib din. Kamar yadda suka saba. Wato zaman kasafi na kudi da suke yi da shi, inda yake fidda musu nasu ihisani kan ko wace fita da suka yi a karshen wata.

Sai voice record da suka dauka na umarnin da yake basu na suje nan, su je can a kan waya. Da kuma wadanda suke dauka na turawan nan da ake turasu wajensu. A karshe ta rufe da cewa "ya mai girma mai shari'a wadannan sune tsayayyun hujjojin da nake da su game da wannan mutumin. Ina kuma rokon kotu da ta taimaka ta duba hujjojina da kuma shaidannun da na gabatar, da kuma halin da mai laifi ya nuna karara a bainar jama'a. A taimaka a yanke masa hukunci daidai da laifinsa". Ta gama tana mai hada hannayenta waje daya tana rokonsa, hawaye na bin kuncinta. Alkalin ya sadda kai kasa yana 'yan rubuce rubuce. Yayin da kotu ta kaure da wata hayaniyar ta 'yan kallo ciki da waje. Alhaji Habib kam kansa ya gagara dagowa, ba zai iya kallon jama'a da wannan zunubin ba. Ya sunkuyar da shi kasa yana zubda hawayen nadama. A daidai lokacin ne kuma Hajiya Laurat da yaranta suka kunno kai cikin kotun. Wata sabuwar haniyar ce ta koma kaurewa ana fadin "ga yaransa nan, ga su nan yace bai san inda suke ba". Hajiya Laurat ta tsaya tangaram a gaban kotun tana karewa mijin nata kallo cikin cunci da kunan rai. Yaransa kuwa gaba dayansu kuka suke suna sharar kwalla.

Mai shari'a Musa ya tsawatar ga masu tace nacen dan ci gaba da shari'a. " ke kuwa wace cs ke, kuma mene ne alakarki da wannan case din?". Hajiya Laurat ta share hawayen da suka kasa yankewa daga idonta ta amsa. "Sunana Hajiya Laurat kuma ni matarsa ce. Wadannan dake tare da ni kuma duka yaransa ne". Alkalin ya kalleta shekeke sannan yace "to meke tafe dake ne, ko kina da wata hujja da zata wanke mijin naki daga zargin da ake masa?".

Hannayenta na rike da wajen tsayuwar ta sauke idanunuta bisa gare shi, tare da nannauyar ajiyar zuciya. Tana mai kara jin tsantsar tsana da kyamar halinsa tace "na zo nan dan in kara tabbatarwa kotu da abinda ta ji a bakin wannan baiwar Allah. Ta fada tana nuna Fadwa. Babu ko shakka mijina munafikin mutum ne wanda ya dade yana cutar al'uma da fuska biyu. Ni nan shaida ce game da hakan. A karshe ina rokon kotu da ta yaimaka yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Domin 'yaya mata su sami salama da nutsuwar rayuwasu. da haka ne kadai zamu iya yakar ta'addanci da wannana safarar yaranmu mata a wannan kasar. Ganin an hukunta wannan mugun bawan ne kadai zai sanya salama ga rayuwata, domin kuwa shi ne sila kuma dalilin lalata rayuwar 'yata". Ta kai karshen maganar hade da kuka mai ban tausayi.
Chapter 20 · 0% Book details