← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka tsayar da masu laifin a inda ya dace kowa ya sami guri ya zauna. Kotu kam ta cika makil, ba masaka tsintsiya. Sahun 'yan jaridu dabam na 'yan sanda da masu kallon shari'a dabam. Kowa da abinda yake cewa, hakan yasa dakin kotun ya kaure da surutu. Ana cikin haka aka buga kofar karamin dakin alkali dake bangare daya a cikin kotun. Tsit! Kake ji ba wanda ya koma magana. Ba jimawa sai ga alkalin ya fito "kooot!".cewar rajistara dake zaune a gaban kotun. Gabaki daya mutanen suka mike dan girmamawa ga alkali. Sai bayan da ya zauna, sannan kowa ya koma mazauninsa. Rajistara ya mike ya karanto karar dake kan layi. Karar dake tsakanin hukumar 'yan sanda ta Jiha da 'yan ta'adda biyu Nura tero, da Hali maiki. Shiru ya biyo baya. Sai da alkalin ya gama duba wasu takardu dake gabansa sannan ya dago ya kalli masu laifin. Dukkansu sanannu ne, kuma rikakkun 'yan ta'adda masu kisa. Ya sauke kansa ya yi dan rubutu sannan ya dago ya bada dama ga wakilin 'yan sandan wato furoskito domin ya karanto yadda al'amarin yake.

Furokiton ya mike bayan ya russuna ga mai shari'a ya fara magana kamar haka:..

*Ku ci gaba da bibiyana*

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

```Page 16```

"Ya mai girma mai shari'a, hukumar 'yan sanda ta Jiha tana tuhumar, Nura (tero) da Hali (maiki) da laifin ta'addanci. Karya dokar kasa, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, musayar wuta da jami'an tsaro. Har ma da bindige jami'in dan sanda guda daya Abbas Malik. A lokacin da suka zo kashe wata mai suna Fadwa. ma aikatanmu kuma suna kan kokarinsu na kama ta, kasancewarta mai laifi da ake nema ruwa a jallo, wato Fadwa 'yar gwa-gwarmaya." Ya dasa aya a nan ya koma mazauninsa. Alkali ya ci gaba da rubutun da yake tun lokacin da furoskiton ya fara magana.

Bayan ya kammala ne ya dago ya kalli masu laifin yace "kun ji abun da mai gabatar da kara yake tuhumarku a kai?". Suka ce "eh". Yace "to kun yarda kun aikata duka abinda ake tuhumarku da aikatawa?". Nan ma ba musu suka amsa da "eh".

Nan kana-nun maganganu suka fara tashi kasa-kasa. Kafin alkalin ya dago daga rubutun da yake sai kowa ya kama bakinsa.

Ya koma kallonsu yace "me yasa kuke son kashe mai laifi kamar Fadwa?". Hali ya yi shiru, hakan yasa Nura ya fara magana. "Muma saka mu aka yi". Alkalin ya yi dan gajeren rubutu kana ya dago "wa ya saka ku yin kisan kai?". Kansa tsaye ba ko shakka yace "Shugaba ne". "Wane Shugaba?". "Alhaji Habib Inuwa Shugaba".

Kotu ta kaure da hayaniyar 'yan kallon shari'a inda a nan a take wasu suke fadin "karya ne! Karya ne!". Har sai da alkalin ya buga gudumarsa sannan nutsuwar kotun ta dawo. Ya yi rubutu a takardar dake gabansa ya koma dagowa. "Mene ne alakarku da shi Shugaban?". "Bamu da wata alaka da shi, kawai dai ya kawo mana aiki ne". "Ku din baku da wani aiki sai kisan kai?". Suka yi shiru suna muzurai. Alkalin ya tattara takardun gabansa sannan ya dago ya kalli jama'ar dake kotun yace "an daga sauraren wannan karar zuwa ranar litinin mai zuwa uku ga watan bakwai kenan. Sannan kotu ta bawa hukumar 'yan sanda ta jiha damar zuwa da Shugaba a zama na gaba". Yana gama fadin haka ya mike ya fice. Ya bar kotu da hayaniyar jama'a.

A ranar kam duk jaridun Jihar kusan abinda suka wuni bugawa kenan. "Kutu ta bada damar kamo Shugaba a zo da shi a zamanta na ranar litinin, bisa tuhumar aika 'yan ta'adda su kashe mai laifin nan Fadwa 'yar gwa-gwarmaya. Wanda ya yi sanadiyayyar kashe dan sanda daya". Wannan al'amarin ya razana kowa, inda wasu mutanen suke cewa duk sharri ne. Wasu kuma su ce zai aikata ko dan yadda ta wulakanta 'yarsa, ta yada tsiraicinta a idon duniya bayan ta sace ta. Haka dai mutane suke ta musayar ra'ayi. Da yawansu sun kagu ranar ta zo, su ji me Shugaban zai ce?.

*Gidan Shugaba*
Gidan ya zama tamakar wurin zaman makoki. Su da suka saba da yin rayuwa mai dadi da yin abinda suke so. Yau gasu an tarwatsa su. An dai-daita su. Gidan daga Hajiya Laurat sai Faisal, dukkansu kuma ba wanda yake iya magana zaune kawai suke jugum bakin ciki na cin su. Yau ga su a gida babu Anisa ba Baffa. Babu kuma wanda ya san inda suke. Alhaji Habib kuwa rabonsu da shi tun da ya fita a fusace daga asibiti. Suna cikin haka wayarsa da ya bari a hannunta ta koma yin kara. Mr. Suwat. Shi ne sunan da ya bayyana, wannan kiran kuma shi ne kira na ashirin da biyu da aka yi da layin. Lambar kasar Rasha ce. Hakan yasa ta yanke shawarar daga wayar ta sanar masa mai wayar baya nan. Ta kai hannunta ta yi receive tare da kangawa a kunnenta. Sai dai kafin ta yi magana aka fara daga dayan bangaren a dan fusace a cikin harshen turanci.

"Haba, haba mana Abib. Har yaushe zaka saka ni in yi ta jira? Shi ne ina kiran wayar ma baka dagawa ko? Kaga in dai babu yarinyar nan a kasa kawai ka dawo min da kudina, na gaji da jira". Hajiya Laurat da zuciyarta ke neman bugawa ta daure tayi magana, ita ma da harshen turancin tace "mai wayar baya gida". Mr. Suwat ba kunya yace "idan ya zo ki gaya masa in ba kaya ya bani kudina". Ya kashe wayar ransa a bace. Hankalinta ya yi masifar tashi amma ganin Faisal a gurin yasa ta daure ta hadiye abun. Hakan kuwa bai hanawa gumi ci gaba da tsatstsafo mata ba. Ta mike ta nufi dakinta.

Da shigarta dakin ta fara binciken wayar tashi tun daga bangaren test message har zuwa email. Amma bata samu komai mai kama da wannan ba. Hawaye kuwa sai zariya suke a fuskarta jiki na bari. Kar dai zargin yarinyar nan ya tabbata. Kar ace da gaske mijinta safarar mata yake. To in ba haka ba wace yarinya ce ya karbi kudinta da har ake cewa in babu ita ya dawo da kudin?. Bata da amsar tambayoyinta, amma dukkanin alamu sun nuna mijinta na safarar mata ne. "Innalillahi wa inna ilaihi raji-un". Kalmomin da bakinta ke ta nanatawa kenan, a kokarinta na ganin ta samun nutsuwar zuciya. Ta kasa zama ta kasa kwanciya bata toilet bata dakin nata cikinta sai juyi yake. Tana cikin haka Alhajin ya shigo ransa a matukar bace, saboda sakonni biyu na tashin hankali da ya samu. Na farko hoton gawar dansa da ya gani Fadwa ta yada, dan shi a tunaninsa babu rai a jikinsa. Ga kuma labarin kiran da kotu take masa ya wanke kansa a ranar litinin, da ya riske shi. Hajiya Laurat ta yi iya kokarinta wajen ganin ta boye tashin hankalinta. Ta masa sannu da zuwa bai amsa ba. Tace cikin sanyin jiki "an yi ta kiranka a waya baka nan, musamman wani Mr. Suwat da ya maka kira sun fi ashirin. Shi kam saboda yawan kira ma sai da nasa aka daga aka ce masa baka nan". Da sauri ya kalleta "wa ya daga wayar?". Tace "Faisal ne. Yace mutumin yace in babu kayan ka mayar masa da kudinsa man". Wani gwauron numfashi ya sauke cike da godiyar Allah a ransa. Sannan yace a diririce "su turawan nan sam basu da hakuri, da zarar abu ya hada ku sai su yi ta matsa maka". Yana kokarin fita ta jefa masa tambaya "kasuwanci ka fara Alhaji?". Tambayar ta zo masa a ban-barakwai ya kalleta da mamaki "au da baki san ina kasuwanci ba?". tace "wallahi ban sani ba, Allah ya sanya alkhairi" yace "amin" yana danna kiran wayar tare da ficewa.

Dakinsa ya nufa kai tsaye. Da sauri ta mike ta bi bayansa da sanda. Saboda zuciyarta ta kasa hakuri lallai tana son sanin gaskiyar mijinta.

Ya murda kofar ya shiga yana magana kasa-kasa a wayar. Dai-dai kofar dakin ta tsaya. Dukda bata jin me yake cewa sosai amma ta tabbatar da Suwat din ne yake magana, dan taji yana bashi hakuri. Ko matsowa ya yi oho, ta dai ji muryarsa ta fito sosai yana cewa "kai matsalarka kenan wlh. Na gaya maka yarinyar nan an sace ta tare damatan nan da aka sace min. Amma ka nace sai ita. Ka bari in kawo maka wata ka gwada ta, na tabbata zata fi maka waccan ma. Domin wannan mai zafi ce bata dade da farawa ba". Bata ji me aka ce masa a cikin wayar ba, ta dai ji yace "to ko kai fa, gobe zan turo maka ita ka tare ta airport. Saboda ni banida lokaci yanzu, ina cikin wata damuwar". Duk a cikin harshen turanci yake maganar.

Jin kafufuwanta na rawa yasa ta yi gaggawar barin wajen tun basu kasa daukarta ba. Da taimakon Allah ta isa dakinta saboda duhu-duhu da idonta ke gani. Addu'a kam duk wadda ta zo bakinta yi take. Wannan wace irin masifa ce? Ashe dama haka Alhaji yake? Ashe yarinyar nan mai gwa-gwarmaya a kan gaskiyarta take? Innalillahi wa inna ilaihi raji-un. Sai ta fashe da kuka. Nan da nan zazzafan zazzabi ya rufe ta, jikinta sai kyarma yake yana ciccira.

*Maitama*
Bayan dogon lokacin da matashin likitan ya shafe a kansa. Baffa ya dawo hayyacinsa, har ma ya shiga baccin dole.

Da dare misalin karfe takwas ta shirya zama da matan nan da suka sato, wadan-da tun da suka zo gidan basu taba ganinta ba. Suna zaune cirko-cirko aka budo kofar aka shigo. Gaba daya suka dago tare dan jin wani lafiyayyen kamshi da ya cika dakin, sabanin kullum idan mai shigowar ya zo. Ganin mace ya basu mamaki matuka. Hakan yasa suka kara maida hankali gareta. Kujerar robar da ta shigo da ita ta ajiye ta zauna tana fuskantar su.
Chapter 11 · 0% Book details