← Book details Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Yar Gwagwarmaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dasa aya idonsa a kanta. Murmushi ta yi sannan ta ja hotunan gabanta ta fara budawa. Sai da ta gama sannan ta dago ta kalle shi. "Aiki mai kyu. Kai ka dauki hotunan?". "Eh ni na dauka duka". Ta gyada kai. Takardun bayanai ne a kan yadda suke tafiyar da rayuwarsu a can. Sai hotunan da ya dauka na ita Hamidan a wuraren da take harkokinta da maza dabam-daban. Ta kalli Ab'ha da ya zuba mata ido yana jiran jin me zata ce.

Tace "na yarda da kai. Na kuma yarda zaka iya. Kamar yadda ka so, nima na amince mu yi aiki tare matukar rai. Babu sauyin ra'ayi, babu ganin wahala ko wuya a karaya. Mu yi aiki bisa burukanmu babu makawa zamu yi nasara".

Ya saki murmushi "na ji dadin haduwa dake Fadwa". Ta masa hararan wasa tace "Yar gwa-gwarmaya dai". Gaba daya suka yi dariya sannan suka hada hannayensu waje daya suka damke tare da fadin "alaka ta fara, aiki zai kankama".

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Wannan shafin naka ne Autanmu, KING BOY ISAH. Zamanawa da daukacin makaranta litattafan hausa online suna matukar alfahari da kai... Kai din na daban ne. Ubangiji ya kara girma da daukaka Allah yasa ka fi haka amin*

```page 10```

Daurewa ya yi ya lalubo nutsuwarsa. Sai da ya fara da gyara murya tukunna yace "ina jinka Sauwam, lafiya dai ko?". Asp ya amsa "lafiya kalau. Dama zan sanar maka ne mun koma karo da Fadwa, a wannan karon ma Allah bai bamu ikon kama ta ba. Amma a tare da ita mun samu wasu 'yan ta'adda. Ga dukkanin alamu babu jituwa a tsakaninsu. Mun yi nasarar kama biyu daga cikinsu. Insha Allah zamu tsananta bincike a kansu, ta nan ne nake sa ran zamu kara gano wace ce ita, su waye suka tsaya mata? Da kuma manufarta. Alamu sun nuna da akwai 'yar tsama sosai tsakaninsu. Da wannan zamu binciki wadan-nan da suke hannunmu dan gano meke tsakaninsu da ita."

Ya dasa aya, yana jiran abinda Shugaban zai fada. Shugaba daya zama kamar mutum-mutumi ya fara tsuma. Cikin rawar murya ya fara magana. "Haba dai Sauwam ta yaya wadan-nan 'yan ta'addan zasu amfane mu cikin wannan case? Gwara ma ka sake su su tafi, Fadwa nake son jin ka kama, ba wasu tsageru ba. Batawa kanka lokaci ne kawai zaka yi. Ka sani sarai mugu baya tona aibun mugu. Ba mamaki ma wasu kudin ne suka hada su. Ka yi watsi da wannan kawai ku nemo Fadwa ita ce abar farauta."

Ya takaita yana sauke numfashi kamar wanda ya yi gudun mitoci. Mamakinsa ya kama Asp. Kasancewarsa kwararren ma'aikacin tsaro da bincike, ya tsinci alamomi na tsoro da rashin gaskiya a cikin kalaman Shugaba.

Bai koma cewa komai ba ya katse wayar. Shugaba ya sauke numfashi yana godewa Allah. Dan shi a zatonsa har an gudanar da binciken ne, sun bayyana sunansa a matsayin wanda ya tura su yin kisa.

Ab'ha ya kalli Fadwa dake kallon hotunan manya da kana-nan karuwan da Shugaba yake aiki da su yanzu. A cikin karamin falon hidanta da ya zame musu gurin zama. Yace Fadwa ni kuwa da zaki karbi shawarata da na baki ita. Na tabbata kuma muddin muka yi amfani da wannan shawarar ba karamin girgiza wan-can tsohon zamu yi ba". Ta sauke numfashi zuciyarta na mata tafasa, kamar ko wane lokaci idan tana kallon hotunan. Tana ganin yadda ya kara jefa rayukan 'yayan jama'a cikin bala'i. Ta sauke manyan idanuwanta a kansa tare da cewa "ina jinka".

Ya dan shafi gefen kansa. Yana al'ajabin yadda Fadwa ta zama marar fara'a kuma mara son yawan magana. Yace "abinda ya kamata mu yi yanzu shi ne, mu fara sato 'yan matan nan da yake amfani da su wajen bunkasa kasuwancinsa a nan. Mu tanadi waje na musamman inda zamu tara su. Na san wannan ba karamin tashin hankali zai haifar masa ba. Tsakaninmu da 'yan matan kuwa ba cuta ba cutarwa a hankali muna nuna musu illar abinda suke yi, ga rayuwarsu da ta iyayensu har Allah yasa su dawo hanya.

Kin ga babu mamaki hakan ya zamo mana wata sauka-kakkiyar hanya ta tona asirinsa." Ya kare maganar idonsa a kanta. Fadwa ta yi shiru tana nazari, a ranta cewa take babu shakka duk kaifin basira da tunanin mace, ba zata taba zama dai-dai da namiji ba. Wannan ita ce hanya mafi sauki da zasu bi su girgiza Shugaba kuma su tashi hankalinsa. Duk da cewa bata da burin da ya wuce jefa shi a tashin hankalin amma sam bata taba kawo wannan ba.

Ab'ha kuwa har ya fara cire rai da zata yi magana. Domin ya fara sabawa da wasu halayenta. Sai kawai ya ga ta saki wani lallausa kuma kakkyawan murmushi, wanda tun da suka hadu bai taba ganin irinsa a fuskarta ba. Ta kama hannunsa ta rike gam a cikin nata. Cike da farin ciki tace "har yanzu basirarka tana nan Abba. Hakika wannan ita ce shawara mafi dadi da muhimmanci da na taba ji tun bayan da na fara gwa-gwarmaya. Na gode Ab'ha. Babu shakka tarayyarmu zata zamo makamin tarwatsa zalumcin Shugaba."

Ab'ha ya ji dadi sosai. Yadda ta karbi shawarar tashi, har ma ta nuna jin dadinta a fili. "Babu filin godiya tsakaninmu Fadwa, kin manta duk tafiyar daya ce?".

Ta yi dariya. Abu mafi tsada a rayuwar Fadwa. Tace "haka ne, sai mu fara shiri. Domin na dade da sanin gidajen da yake tara su".

Ta dauko hotunan nan da list na sunayensu suka fara dubawa. Yana budawa tana gaya masa guraren da suke zaune.

*01:30am*
Karfe daya da rabi na daren ranar. Kamar yadda suka shirya suka fito cikin shirinsu. Ita din tana sanye da bakaken kaya na roba, riga da wando. Sun bi jikinta sun shafe, kai kace a nan aka kirkire su. Sai bakar hular sanyi da ta saka bayan ta tufke gashin kanta waje daya. Takalmin kafarta ma bakake ne irin masu shegen tsinin nan. Sai glass da ta rufe idonta da shi wanda shima dai bakin ne. Wannan ita ce shigar Fadwa a duk lokacin da aiki irin wannan na fitar dare ya same ta.

Ab'ha yana cikin kayan sanyi up and down. White in colour. Ya rufe kansa da hular sanyi ita ma fara. Sai takalminsa cover farare. Bai saka wani glass a fuskarsa ba. Haka suka jero cikin takun nuna isa da izza har suka isa gaban wata mota kirar boss dake ajiye a garejin dake ciki matsakaicin gidan suka tsaya. Ba wanda ya yi magana a cikinsu. Suka kalli juna na 'yan dakiku kafin daga bisani suka yi shaking hand, sannan ko wanne ya zaga ya zauna a mazaunin gidan gaba. Ab'ha ne mai tukin ya tada motar a hankali ya silalata suka fice...

*Nasmat* ✍
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

*Keep following...*

```page 9```

Bangaren Shugaba kuwa hankalinsa ne ya yi masifar tashi a lokacin da Chaka yake gaya masa police sun kashe masa yara biyu, sun kuma kama wasu biyun. Domin in da akwai abinda yafi tsoro a duniya bai fi tonuwar asirinsa ba.

Zaune yake shi kadai a tafke-ken falonsa yana zare ido. Ya rasa yadda zai yi. Ga wani wahalallen gumi dake tsatstsafo masa a duk kofofin gashin dake jikinsa. A haka ya fara jin karar wayarsa alamar kiransa ake. Saboda halin da yake ciki sam bai yi tunanin duba lamba ko sunan mai kiransa ba. Ya daga wayar da guntuwar sallama. Karar tashin dariyar da ya ji ne ya saka shi saurin cire wayar daga kunnensa, ya duba number. (Unknown) ya gani. wannan ya tabbatar masa da mai kiran "Fadwa ce". Ya fada a cikin zuciyarsa. Dan kuwa ya sani ita kadai ce mai kiransa da boyayyiyar number. Kamar zai katse kiran, sai kuma ya kasa. Yana so ya ji me zata ce masa.

Ya mayar da wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba. Fadwa kam dariyarta ta yi mai isarta sannan ta takaita ta fara magana. "Alh. Habib Shugaba. Gaskiya kana da matukar wayau. Sosai nake yabawa zummarka ta son ganin ka kawar da duk wanda ya fara gano gaskiyarka. To ba ma wannan ba. Na kira ka ne dan tayaka murna na ji an kama karnukan farautarka biyu, bayan da aka aika biyu barzahu. Ba shakka 'yan sandanmu na aiki tukuru wajen ganin sun kawar da ta'addanci a kasarnan. Sosai na jin-jinawa aikinsu. Sai kuma ka bani tausayi..." Mai makon ta karasa maganar sai ta koma kecewa da wata dariyar. Nan ma sai da ta yi mai isarta, sannan ta ci gaba da magana. "Ka san inda kake bani tausayi? Duk da cewa ka sani amma bari in kara tuna maka." Ta yi shiru kamar ba zata yi magana ba. Sai can tace "gaskiya ka bata wayonka wajen barin karnukan nan su san cewa kai suke yi wa aiki. ka san fa tsagerun yanzu sam basu da juriya. Ya kake tunani idan suka ji horo suka bayyanaka a matsayin uban-gidansu? Kai inaaa gaskiya abin ba zai maka kyau ba. Fatan alkhairi Shugaba..". Sai ta karashe cikin dariyar nan tata. Sannan ta katse wayar.

Shugaba da ya gama tafiya duniyar mutuwar sassan jiki ya tattara dan ragowar kuzarin da ya rage masa ya motsa hannunsa dakyar ya sauke wayar daga kunnensa. Ya zuba mata ido, kamar mai neman mafita a jikinta. Ya tabbata abinda yarinyar nan ta fada duka zai iya kasancewa.

Nan ma ya koma shiga wani sabon rudu, hankalinsa ya kara tashi. Ya mike daga zaune ya fara zarya a falon, yana kai da komo kamar wanda aka saka matarsa labor. Ya rasa inda zai fara. Tun da yake harkokinsa bai taba haduwa da matsala kamar Fadwa ba. Gashi babu hali ya kira jami'an tsaro game da wadanda aka kaman.
Chapter 6 · 0% Book details