Sashe 7
Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiko haydar baki ya saki yana kallon fatima tuni yanayin shi ya fara cenzawa ji yake kamar ya tashi ya rungume ta
fatima ce ta lura haydar ita yake kallo dan haka ta tsaya cak tana mamakin shi kuma wannan me yake kallo.
salis ko yanajin fatima ta daina kuka ya bude ido cikin bacin rai yace meyasa kike min haka ne zahara dan Allah idai baso kk kijamin fushin Allah ba toh ki dakata da irin wannan abun, kije kiyiwa mama sallama kizo mutafi.
sumi sumi ta wuce ta tura dakin mama tana shiga haydar ya kalli salis yace wlh kai wawane d'an kauye.
murmushi salis yayi tare da mikewa yana fadin Allah ya shirye ka.
zuwacen mama da alhj yusuf suka fito fatima na rike hannun babanta .
alhj yusuf yaga salis da taslim tseye yace kardai har zaku wuce?
salis ne yabashi amsa eh baba zamu tafi.
yace toh daman Ina son ganinku kaida haydar tsakanin ku wanene akace sun daidaita da fatima?
da sauri haydar ya d'akai ya kalli salis shima salis d'in kallon shi yayi
🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[10:02PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
33-37
Alama salis yakewa haydar ya fad'a aman haydar sai make kafad'a yakeyi.
alhj yusuf yace daku nake mgn fa .
" taslim ce ta lura salis kunya yakeji dan haka tayi sauri tace baba yaya salis ne.
haidar ne ya d'ago kai ya harari taslim yace ke dan ubanki dake ake mgn
alhj yusuf yace haydar me yasa bakin ka ya iya furta zagi ne, ai taslim batayi laifi ba abin da tayi kai ya kamata ace kayi amman sai kayi shiru, juyawa yayi ya kalli salis yaga ya dukar dakai yace salis ni dama nasani baban ku ya fad'amin dama naso ne naji daga gareku amman tunda kun kasa magana taslim ta fanshe ku.
ya juya ya kalli haydar yace toh kai kuma fah.
baba ni bayanzon zanyi aure ba .
bata rai baba yayi yace toh sai yaushe?
idan salis yayi ni daga baya zanyi.
baka isaba kafison kai ta d'ako mana mgn ai ni inda sosamu ne nan da one week kayi aure dan haka duk abinda akeci nan da Wata 1 kawo yariyar da kk so,Dan mun riga mun yake rana nan da wata biyu dan haka kuje kufara shiri.
haka suka koma gida cike da farin cike sai dai azuciyar salis ranar da akasa yayi mai yawa
dan haka da suka kebe da fatima yace zahara gaskiya ranar nan da akasa yayi yawa.
haba yaya wata 2 ne yayi yawa toh ni wlh kusa ma naga yayi min dan nifah wlh tsoron ma ranar nakeji.
da sauri ya kalleta tsoro kuma toh tsoron me kikeji, kardai ki kecemin tsoron miji kike, toh idai haka ne gara ma tun yanzon ki cire shi dan gaskiya bazaki takurani ba , zahara kinsan fan nayi hakuri
haharara shi tayi sannan tace hakuri me kayi?
murmushi yayi sannan yace Zahara Kenan kisan fah kina da kyau kuma na kusa najiki jiki na
kawai daurewa nakeyi karne abin kunya, kasa ya yayi da murya ya Kira sunanta sannan yace kifah shirya dan idan mukayi aure akan kirjin ki Zan rinqa kwana.
hannuta tasa ta rufe ido dan be saba mata irin wannan maganganun ba.
murmushi yayi sannan yace zahara idan akace yau andaura mana aure bakaramin farin ciki zanyi ba, bare kuma na ganki ad'akina, Hmmm ranar zan nuna miki irin son da nake miki zan tarairayeki kaman kwai zan nunamiki soyayyar daba kowane namiji bane zai iya nunawa matar sa irin saba.
kwashewa fatima tayi da dariya sannan tace amman dai yaya sambatu kk KO, wannan irin cin buri ne haka.
shima dariya yayi sannan yace aidama nasan bazaki gane ba amman ahankali zan ganar dake, mikewa yayi tare da fadin bari naje gurin haydar.
dasauri tace bayan zon ,muka dawo ba shine har zaka koma, ni wlh natsani haydar d'in nan banason ganin shi.
shima cikin mama ya kalleta yace zahara kinada hankali kuwa d'an uwan nawa, meya miki ?
toh yaya ai shima ya tsane ni dan haka nima bana sonshi wlh ko sunan shi aka kira gaba na faduwa yakeyi.
kallon ta yayi cikin ido yace xahara haydar ba tsanar ki yayi ba haka halinsa yake nima bakiga yana min ba, kuma dan Allah ki yafe masa karki kara kullatan shi aranki kinga d'an uwanki ne , koya miki wani abu kijin haushi toh ki gayamin ni kuma xan faranta miki rai kinji KO ?.
da sauri ta d'aga kai .
yace kin yafe masa?
eh tace ahankali.
Shirye shiryen biki nata kankama acikin wannan family ummi shiri take sosai komai ta gama had'awa da dan ganci na
fatima dan yazun bikin saura sati 2 kuma har wannan lokacin salis be kawa yariyar da zai aura ba dan haka akabar batunsa dama alhj yusuf ne yaso ahad'a amman daddy tuni yabar zancen haydar kamar yadda yace ya cireshi acikin 'ya'yan shi.
haydar ne zaune shida abokin sa anas a harabar gidan su anas sigari kawai yake sha daya shanye wani sai ya kara d'akkowa
anas ne ya lura haydar ya kusa shanye kwalin sigarin dauke ragowar yayi sannan yace big boy waikai meke damun ka?
yana fesar da hayakin dake bakin shi yana fadin fatima.
Hmm daman aikai ya kamata ka aureta sai da fad'a maka kace bahaka ba sai yanzun da lokaci ya kure zakace wani fatima, kana nufin sonta kk?
niba sonta nake ba amman ni banason salis ya aure ta, saboda Ina matukar sha,wan yariyar dan haka nafison wani daban ya aure ta, yanzun fah duk tarin 'yan matan dana ke dasu basa birgeni Dana rufe ido fatima nake gani
tsaki anas yayi cikin takaici yace toh yanzon dai saidai kayi hakuri garama ka cireta aranka dan tafi karfin ka.
tsaki shima yayi yamike yabar wajen tundaga ranar haydar ya zama kamar mara lafiya baya mgn sosai besan me yake damun shiba.
Yau sauran kwana biyu biki dan haka yan baki sun fara isowa fatima da taslim sai shirye shirye sukeyi daddy na cikin farin ciki.
ummi ce ad'aki zaune da kawayenta suna kallon akwati ta zuwa cen saiga salis rike da hannun haydar ummi ce ta kalli haydar tace meya kawoka?
haydar ne yace ummi ninace yazo yaga akwati.
cikin fad'a tace to tunda kai ka kirashi saika shirya amsan da zakaba babanku idan yadawo ya samu haydar agidan na, mikewa tayi tafita adakin ahankali mutane dake dakin suka fita daya bayan daya.
haydar ya tsuguna gaban akwati yana dariya yana duba kayan zuwace yace brother kaya sunyi saidai kacika hijjab dayawa aciki.
murmushi salis yayi sannan yace ra,ayina kenan.
anagobe daurin aure da daddare salis ya shiga har d'akin su fatima fatima ya hango manne jikin gado ta rufe fuskarta gefe ko kawayen su ne zaune suna hira sunna ganin shigowan shi suka bar daki gaban Fatima yaje ya tsuguna dariya yayi sosai sannan yace zahara duk tsoron auren ne haka,
batace kome ba ya sake cewa zahara dan Allah ki kwantar da hankali bana son ganinki cikin wannan halin .
cikin kuka tace yaya kwata kwata banajin dadi, azuciyata taki natsuwa nayi nayi in natsar da ita nakasa gani nake kamar wani abu zai faru.
da sauri yace babu wani abu dazai faru zahara sai alheri kiyi tunani dakau kila akwai abinda yake damunki.
shiru tayi zuwacen tace yaya jiya nayi mafarkin na auri yaya haydar.
dariya yayi sannan yace ni daman nasan akwai abunda yake damunki dan Allah ki cire tsanar haydar azuciyar ki, kuma kidaina wannan tunanin mafarki ne kawai insha Allahu gobe warhaka burin mu ya cika saida muyi fatan cikawa da imani, haka haydar yayi ta rarrashin fatima harta fara dariya.
washe gari aka tashi da shirye shiryen dauren aure tun 12:00 bakin daddy suka fara halara kofar gidan ya ciki makil da jama,a sai hada hada ake salis ne ya fito cikin babban riga farare kal yayi matukar kyau waige ya farayi yana neman haydar amman ko alamar shi begani ba dan haka ya shiga neman no barshi tsaki yaje sabo da layin kwata kwata yaki shiga ya koma cikin abokan sa ya tsaya ranshi bace zucen yaga guri ya kara cika duba agogo yayi yaga karfe 12:43 cikin sauri ya nufi motar shi wani abokin sane yabi bayan sa yana fadin inakuma zaka?
yana kokarin barin wajen yace tahir yanzon zandawo zanje na dauko haydar ne.
gidasu anas ya nufa yana tura kofar anas dakin yaga haydar zaune ya tasa sigari cikin zafin zuciya yace haydar kana nufin bazaka halarci daurin aure na bane?
bece komaiba dan haka yasa hannushi ya fara jawoshi bayan motar ya turashi anas ma ya shiga sun kamo hanya kenan kiran daddy ya shigo wayar salis cikin fada yace kana ina?
yace daddy ganinan zuwa naje dako haydar n.......
salatin dasu anas kiyine ya dakatar da shi yana d'ago kanshi yaga Wata babban mota ta nufosu salis yayi kokarin kaucewa amman Ina tuni motar ta fara watan gaririya akan titi.basu kara sani me ya faru ba
zucen haydar ya bude ido ganin shi yayi kwace cikin jini muryan salis yaji yana kiran sunan shi daker yaja kashi ya kalli gurin kwance yaganshi jini na bulbulowa ta cikin shi jan jiki ya fara har ya isa gaban shi ya kama hannun shi babu abun yake kira banda zahara zuwace yayi kalmar shada be kara motsawa ba haydar ya farajan shi duk da shima ajikace yake.
karan wata mota yaji yana kallon gurin yaga daddy da baba yusuf suna tahowa, gurin salis suka nufa daddy ne ya daga hannun shi yace ya innalillahi wa inna ilaihir raju,un Allah ya karbi abun sa😭😭

*Gaisuwa da fatan alheri gare ku*
*Zainab bobbo adamawa*
*Yahancy gombe*
*bilkisu muhammad*
*xeeshata*
*mmn abdulnasir*
*hajju lokoja*
*Fatyma*
*harda wadan da bankira suna ba inajin dadin yadda kuke nuna sayayyar ku ga wannan lbr*😍😍😘
38 - 39
Tattara su akayi gaba daya aka nufa asibiti har anas.