← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 29

Sashe 22

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

a gaban fatima suka tsuguna suna kokarin dagata suna tambayan ta menene.

shi ko haydar fadi yake ummi yanzon haka mage ta gani kisan matsoraciya ce.

fatima KO hannu ta daga tana kuka take nuna haydar tana fadin shine wlh haydar ne shine wanda ya cuceni , wlh shine ummi, shine gashi nan agaban ki Allah ya tonamai asiri.

haydar sakin baki yayi yana kallon fatima

ummi ko gani take kamar fatima aljanu gareta.

dan haka tacewa taslim kiramin daddyn ku ya samo mana malami amata rukiya.

Matsowa haydar yayi yana fadin babu wani aljanu ummi yanzun haka be wace mage ta......... wayar shi daya hango agefen fatima shine ya dakatar dashi da sauri yakai hannun shi ya dauki wayar , zamewa yayi akasa ya zauna sannan ya cire hular dake kansa ya fara fifita yana fadin Inna lillahi wa inna ilaihir raju,un.

da sauri ummi ta juya gurin haydar tace toh kaikuma meya same ka.

basu ankara ba sukaga fatima tayi waje aguje, yayin da haydar ke fadin shikenan ummi nashiga uku.

taslim ce tabi bayan fatima da gudu ummi ko tana gun haydar sai fifita take mai zuwacen ta fara girgiza shi tana fadin haydar wai meke faruwa kar ku maidamu mahaukata mana.

itako taslim ko da ta fita kofar gidan babu fatima babu alamarta juyawa tayi tana kuka.

tana shiga tace ummi ban ganta ba.

da sauri haydar ya daki bango.

cikin bacin rai ummi tace taslim wuce muje tunda bazai gaya min abin da ke faruwa ba, Allah ya baku sa,a.

ummi tana komawa barayin su ta kira daddy awaya ta fad'a mishi halin da suke ciki.

ba,a dade ba saiga daddy ya shigo d'akin su haydar ya fara shiga, samun shi yayi ya hada kai da gwaiwa.

kiran sunan shi yayi haydar, da sauri ya dago kai ya kalleshi yace taso muje.

mikewa yayi sumi sumi yabi bayan shi bayan sun shiga motar daddy sun zauna daddy ya kalleshi sosai yace

" me ya hadaka da fatima harta wuce gidana ta tafi gidan mahaifin ta?, babanta yayi min waya cewa gata tazo ko mayafi babu kuma tunda taje ta kasa mgn illah fadin haydar ne, haydar ne, me ka mata dahar ta shiga wannan yanayin ?

kasa mgn yayi ya dukar da kanshi cikin matsanan cin tashin hankali.

daddy yasake yin mgn haydar badakai nake mgn back.

nan ma shiru babu amsa

daddy yace kana nufin bazakayi mgn ba kenan?

kara dukar da kanshi yayi kasa danji yake kamar kasa ta bude ya shiga.

kallon shi daddy yayi cikin takaici sannan yace

nakula baka da gsky tunda gashi ka kasa mgn , ummi ya kira awaya tana dauka yace dauko gyalen ki kizo muje , basu juma ba ummi ta fito.

gidan alhj yusuf suka nufah.

suna shiga cikin falon fatima ta mike da saurinta tace baba gashinan yazo shine macucin dakace idan ka ganshi zaka karban min yanci na , yau gashi agaban ka.

baba ne ya daka mata tsawa sannan yace koma ki zauna .
batayi musuba ta koma ta zauna sannan ta runtse idonta tace wlh baba bana son ganin haydar arayuwata tunda na fara sanin kaina yake cuta ta.

ahankali daddy ya matso inda take yace fatima gayamin wanne irin cutar dake haydar keyi?

kowa afalon ita yake kallo , haydar ne kawai kansa ke kasa.

cikin kuka fatima tace daddy haydar shine mutumin da yayi min fyade tun da kankanin kuruciya ta.

ummi ce ta mike dafe da kirji tace lallai fatima yau na tabbatar baki kaunan haydar ai basai kinmai sharri ba, dan kina son rabuwa dashi , muyar daddy taji yana fadin

ke banson mgnr banza keda kk wannan surutun shi haydar din kinga ya musa ne.

da sauri ummi ta kalli haydar taga ya kasa daga kan shi sai hawayen dake digowa, itama kuka take tace haydar da gaske ne?

bece komai ba illah kukan sa daya karu har mutanen dake falon na iyajin sheshshekan kukan sa.

kuka ummi ta fashe dashi tana fadin nashiga uku Allah ka dauki raina na huta daganin wannan abin takaici.

mama ce ta dafah ummi tace bar kuka dan Allah ai tama kona gidan sauki.

cikin fada daddy yace wanne sauki ai babu wani sauki, Kai haydar maxa katashi kabar wajen nan tun kafin na kwashe maka albarka, kuma aure tsakanin ta dakai babu dan iska me abin kunya kawai ina takaicin ka amatsayin dana tari ya fara babu kaukautawa haydar ya tashi da sauri ya nufeshi, tun kafin ya karaso daddy ya daga mai hannu cikin tsananin tarin yace idan ka sake ka tabani Allah ya isa tsakani na dakai.

kuka ya tsaya yanayi , baba yace kai haydar jeka kawai .

cikin matsanan cin tashin hankali ya fita waje, wani haushin anas yaji yana taso mai, wai wace ma ya dauki hoton, duk shine yaja mai wannan tashin hankalin dana ke ciki, cikin zafin zuciya ya nufi mota yau anas saiya ci uban shi,zai gayamin uban waye yasashi ya dauki hoton

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊
[8:33PM, 4/22/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

79 - 81

Kai tsaye gidan su anas ya nufah yana isa ya fito daga motar ko rufeta beyi ba, d'akin anas ya tura.

anas naganin haydar abirke ce ya mike da sauri kafin ya bude baki haydar ya kaimai duka abaki, tuni bakin ya fara jini amman duk da haka bebari ba duka kawai yake aika mai , shiko anas yana dafe da bakin shi yake fadin haydar ka bari mana menene haka baka da hankali ko, mena maka, ganin da yayi haydar besan yanayi ba yasa ya fara ramawa.

mahaifiya anas ce ta fito da gudu tsakiyan su ta shiga tana fadin kai kai ku bari menene haka kuma, kai haydar anas kubari, bazaku bari ba ko saina kira maza, basuma san tanayi ba gashi gidan babu kowa me gadin ma ta aikeshi dan haka ta fashe da kuka.

ganin mahaifiyar anas na kuka yasa suka saki juna , da sauri haydar ya juya ya fita momy nakira kai haydar zo nan , ina harya tada mota.

yana shiga gida dakin ummi ya shiga ya sameta zaune kanta babu dan kwali ta kwanta akan kujera ta daga kanta sama tana girgiza kafah ga kuma hawaye nabin fuskar ta.

jikin shi asanyaye yaje gabanta ya tsuguna ya rike kafar ta yace

" ummi dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, ummi kidaina zubar da hawaye akaina"

cikin kuka tace haydar ka tashi kabani guri bana son ganin ka , dan ka bani mamaki kuma kabani kunya idan banyi kuka ba me kake son nayi, haydar ashe ka dad'e kana shiga kyauye kyauye kana lalata yaran mutane.

cikin kuka yace ummi wlh ba haka bane itama wannan tsautsayi ne, momyn su ansa ce ta aikeshi gurin yayanta , shine yace narakashi, wlh ummi muna kokarin shiga wauyen ne muka hadu da ita.

da sauri ummi tace kaikuma dayake bunsuru ne baka gani ka bari KO, ashe shiyasa lokacin da salis yanuna yana sonta kaita tsoro da tsurfa kala kala, wlh haydar bakayi ba kayi asara wlh, ni kuma kasani takaici ka shayar dani bakin ciki , inama kai aka dauke aka barmin salis

kuka haydar ya fashe dashi sosai sannan yace kiyi hakuri ummi in Allah ya yarda zan zama kamar shi.

cikin kuka ummi ke girgiza kai tana fadin bazaka taba zama kamar shi ba salis mutumin kirki ne , kwata kwata ba halin ku daya ba har yabar duniya bazan ce ga abinda yamin ba kai kuwa fah, tun kana karami kake batamin rai .

yana kuka yana rokon ummi ta yafe mai amman ina daga karshe ma tashi tayi tabarshi agurin.

tashi yayi ya koma barayin su yaci kukan shi ya koshi gashi besan wanne hali daddy yake ciki ba.

haka ya kwashe kwana biyu adaki dan ko sallah agida yakeyin ta babu ci babu sha duk yayi baki ya rame.

ummi ma zuwa wannan lokacin tayi kuka harta gaji.

daddy ne kwance a turakar sa yayin da alhj yusuf ke zaune agefen shi yana mai yajiki.

ahankali daddy yace naji sauki yusuf, Ina fatima fah?

fatima tana nan lfy tace agaida ka.

dan murmushi yayi kadan sannan yace nagode.

zuwacen ya sake cewa kaga abinda haydar yayi KO, ashe duk surutun da mukeyi kallon mu kawai yakeyi , ya maida mu shashatai.

dan dukar dakai alhj yusuf yayi kad'an sannan yace toh ya za,ayi sai hakuri kawai, itama fatiman tana cen tana cigaba da haukanta wai ita sai dai ya sake ta, nace zama tayi tabari ne.

cikin zafi daddy, yace ai indai ina raye mamana baza dawo dakin haydar ba, me zatayi da dan iska.

alhj yusuf da sauri yace yaya dan Allah ka dunga gyara kalaman ka akan haydar kai fah uba ne, kuma ai wannan abun daya faru da ne yanzon ya natsu.

Hmmm haka kake gani.

*****

ranar da haydar ya cika kwana 4 adaki hankalin ummi ya tashi dan ko motsin shi bata ji

kasa hakuri tayi taje ta samu daddy domin ta sanar dashi halin da ake ciki.

tana shiga tace alhj haydar fah bana ganin wucewan shi kuma na tambayi me gadi yace shima ya dade be ganshi ba.

da sauri ya daka mata tsawa bana son na sake jin kin kiramin sunnan haydar a gidan nan idai kina son zaman lfy, hannushi ya kad'a sannan yace fita ki bani guri.

tana kokarin fita daddy ya fara kwalawa taslim kira.

lokacin da ummi ta zauna afalo taga wucewan taslim aguje zata gurin kiran daddy, zama tayi ta dafe kai.

zuwa cen sai ga daddy ya fito taslim na binshi abaya ko sallama bema ummi ba ya fita abin shi, taslim ko zama tayi kusa da ummi.

ummi juyowa tayi ta kalli taslim tace taslim tashi kije dakin haydar ki gani lfy yake.

wasa taslim ta fara yi da yatsun ta sannan tace ummi daddy fah yace idan naje gurin yaya haydar be yafemin ba.
Chapter 22 · 0% Book details