← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

daidai lokacin mama ta fito tace a,a su haydar ne?

eh mama ai mushigo ba kowa afalon sai fatima tana bacci sai ma asace ta bata sani ba

dariya sukayi har mama amman mama tasan cewa fatima ba bacci takeyi ba.

komawa d'aki tayi tabarsu afalon .

mama na barin falon haydar ya mike yaje gaban kujeran da fatima take ya sauke ahannuta ya kama hancinta ya matse.

da sauri ta fara cikicikin kwacewa tana bige hannu shi.

sakinta yayi yana fadin munafukkar yariya ai kin kusan shigowa hannu na sai kin gane baki da wayo yar kauye kawai kuma bari kiji na fada miki kin ga wannan hijjaban naki karki sake kizomin dashi gida na ,idan kuma kin ki ji toh kizo dashi ki gani, dashi zan shake ki, ni ba salis bane ni nan da kika ganni mugu ne

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:17PM, 4/4/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

56 - 58

Bata ce komai ba in ban da binshi da kallo da take.

komawa yayi ya zauna sannan ya sakke kallon ta yace

meye kika tsare ni da kallo dawani idon ki sai kace na mujiya.

mikewa tayi tana tafiya tana fadin toh me zankalla agurin ka inban da kayan haushi tsaki taja ta shige d'aki.

haydar ya girgiza kai sannan yacewa anas yariyar nan tana wasa dani, amman ba komai bata sanni bane ba dai zata shigo hannuna ba, saita gane shayi ruwa ne.

anas ya tabe baki yace kai matsalata dakai baka daukan shawara, matsalar ka yawa gareta

suna cikin haka sukaga fatima ta dawo ranta bace nesa dasu ta zauna tana zubura baki.

anas ya dube ta yace fatima dama munzo muji ko akwai wani abun da kk bukata sabo da kinga lokaci yana zuwa yama zo.

kasa cewa komai tayi hawaye na tsiyayowa a idon ta tayi matukar bawa anas tausayi.

haydar KO yi yayi kamar besan sunayi ba, sai danna waya yake.

ahankali anas yace fatima kin yi shiru bakice komai ba, kodai na samu taslim ne muyi mgnr?

kuka ta kara rusawa ta kasa furta komai.

anas ya mike yaje har kusa da ita yace haba fatima me yasa kikeyin haka irin wannan ai sai kijawa kan ki wani ciyon.

sai alokacin haydar ya kalleta yace

" kai kake wani lallabata karabu da ita mana tayi kukanta idonta ne zaiyi zafi, kuma bari kiji na fad'a miki kinga irin wan nan kayan dake jikin ki karki zomin dashi gida na dan ni bana ra,ayin su .

" ahankali tace ni dama nace ne kayi ra,yin su, ni Ina ruwana dakai"

mikewa yayi da sauri ya fizgota anas ne ya rike shi yana fadin ya haka ne, kamanta a inda ka ke ne.

da sauri ya saketa yace ai zan rike ki, kuma karkiga kaman wai ina son ki ne ,ni bason ki nake ba, kuma bazan taba sonki ba amman yazaman miki dole kisamin irin kayan da nake so ,ke dole ne ki kumin biyayya ko kin ki ko kinso.

mikewa tayi tana tafiya tana fadin wlh baka isa ba wai kai nan har kana ganin kai namiji ne, katon banza dan daudo kawai.

binta yayi aguje ya ya damke ta ya fara kai mata duka abaki

fatima ihu take tana kiran mama amman taki fitowa.
.
daker anas yaja haydar suka fita agidan .

fatima d'akin mama ta fad'a ta fashe da kuka tace mama kinaji yaya haydar na duka na shine kk barni ya sheni ko?

muryan mama taji cikin kuka tana cewa

Fatima me kk son nace muku sai da baban ki yace miki haydar ba sa,an ki bane kece karama ke ya kamata ki kwantar dakai, ya kamata ace yanzon kin hakura kibin umarnin mu kuma da kk cewa na Bari ya kashe ki, idan na ceceki yau idan kk je gidan shi zan biyu ku ne domin inceceki?

tana kuka take fadi mama toh ai shine yake fadamin bakaken maganganu shi baku ganin lefin shi sai nawa.

toh shikenan karki bari ke zaki sha wuya ni babu ruwana.

haka kwanaki sukaita tafiya mama da ummi a nata shirye shirye fatima ko sai ramewa takeyi kulum cikin tunani.

fatima ce kwace akan sallaya ta kudun dune kanta cikin hijjabi hayaniya muta ne ta faraji afalo ,dumin yau sauran kwana biyu daurin auren.

cen ta ffara jin gud'a, tsaki taja ta kara kudun dunewa har da toshe kunne.

tana nan kwace taslim ta shigo da gudu tace sister , da sauri fatima ta mike tace

taslim sai yau kk ga damar zuwa?

dafah ta taslim tayi sannan tace fatima meya sameki kk rame haka baki da lfy ne?

hawaye ne ya fara zubo mata ahankali ta bude baki tace toh ba dole na rame ba, wai arasa wadda za,a had'ani dashi sai haydar dan dai kawai anga babu yaya salis nasan daya nan bazai bari ayi wannan auren ba sabo dashi yasan waye haydar .

itama taslam kuka ta fara sannan tace

sister kibar wannan mgnr kema kisan da ace yaya salis nanan baza,ace ki aure yaya haydar ba kuma kema ya kamata kiyi hakuri da yaya haydar din kinga fa kamar su daya banbancin kadan ne.

cikin fad'a tace wace miki kyaun fuska ko na jiki nake nema, niba kyaun su ke gabana ba nasan naso yaya salis ne saboda kyawawan d'abi,un sa bawai dan wani abu nasaba kamar yadda kk tunani.

taslim share hawayen fuskarta tayi ta mike sannan tace sister bazaki gane ba, yazon dai ki tashi muje anas najiramu zai kaimu lalle.

itama mikewa tayi tana bin bayan taslim tana fadin ni bazayi lalle ba.

suna fitowa falon fatima taga mutane cike afalon suna kallon akwati sai d'aga rigunan suke suna dariya daidai lokacin da wata mata tace ikon Allah dube wata riga saboda lalacewa wannan ai da ita gara babu kuma duk su sukafi yawa acikin kayan.

hjy amina kawar mama tace ai wannan kayan da kika gani Allah kadai gasan kudin da aka kashe gurin sayan su.

dayar ta sake cewa komai tsadar su ni basu dameni ba dan wlh da ace 'yatace aka kawo wa wannan kayan mayar dasu zanyi haba dubi fah dan Allah sai kace na 'yar arna daga wandona sai wasu yan iskan riguna sake daga wani tayi tace wannan kuma menene?

gaba daya falon akasa dariya ban da mama dumin matar ta fara bata haushi .

itako fatima kitchen ta nufa tanajin maganar da matar ke fad'a dan haka ta fara kuka.

saida mama tasa baki sannan fatima ta yadda tabi taslim, sai dare suka dawo , mama ta kalli fatima tace

kinga har kinyi kyau, dan Allah kirinkka cin abinci kidan ciko kafin jibi..

turo baki tayi tare dasa hannuta ta goge fuskarta.

ana gobe dauri auren ne fatima taita addu,a Allah yasa abin da ya samu salis shima haydar ya faru akansa kafin daurin auren.

washegari da rana aka daura auren haydar da fatima acen gidan kakan su alhj salisu.

tunda fatima ta samu lbri an daura auren hankalinta yayi mummunan tashi.

daddare abokan haydar ne sukazo daukan amarya.

kuka tayi ba kad'an ba da za,akaita gidan haydar.

wani sabon gini kayi kafen nasu ummi nan aka nufa da fatima fuskar ta rufe yake.

abakin gado aka zaunar da ita tana rusa kuka, bayan kowa ya wuce aka barta ita kai tana kuka ta mike ta cire gyalen dake jikin ta dauko wani zunbulelen hijjjabin ta, ta saka ,komawa tayi cen lungun gadon akasa ta kwata ta kudundune acikin hijjabin

zuwacen ta farajin takun ta fiya alamar ana tahowa dakin cen taji an daki kofar garramm.

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:15PM, 4/5/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

*Aslm 'yan uwa da abokan arziki Ina mika gaisuwata agare ku bansan taya zan nuna muku farin ciki naba akan yadda kuke nuna soyayyar ku ga wannan lbrn musam man 'yan group d'ina fadeela lamido novels 👍✔✔✔❤❤*

59 - 60

Kara takurewa tayi guri daya, jikin ta ya hau kerma dan jitayi yau balakin tsoron shi take ji.

shikuwa haydar ganin bata cikin d'aki ya tsaya yana kallon kofar toilet zuwacen yaje ya tura kofar toilet din ganin da yayi babu kowa yasa shi zagayowa lungun gadon , da saurin sa yasa hannu ya jawota saida ya jawota har saitin kafarshi sannan ya cikuikuyeta acikin hijjabin , zama yayi bakin gadon sannan ya dauki kafarshi daya ya daura akan cinyarta, saida ya kureta da ido sannnan yace

" ina wasa dake ne, bana ce karkizo min da wad'an nan hijjaban ba?

jikinta na rawa tace mantawa nayi.

yana murmushin mugunta yace eh ai naji dadi da kk manta daga yau idan nabaki umarni bazaki manta ba, mike tsaye.

da sauri ta mike sannan yace ki cire hijjab d'in' ki mikomin

tana rawar jiki ta cere ta aje agefen shi.

haydar ya lura fatima ta firgita dashi dan haka yayi murmushi ya kara cewa ki bude kunnuwan ki da kyau daga yau karna kara ganin ki da hijjab, wai ke adole kina boye min breast d'in ki, toh indai nine ko abude kika barsu babu abin da ya dameni dasu idan kuma bakiji ba toh kikara sakamin hijjab kiga ni dake da abin da kk boyewa zaku gane baku da wayo.

cikin sauri yabar daki fatima taja Wata ajiyar zuciya ta koma bakin gadon ta kwanta ,kasa bacci tayi sai cen wajen asuba bacci ya kwasheta.

washegari

bayan haydar ya gama shiryawa bebi takan fatima ba dakin ummi sa ya nufah.

yana shiga ta washe baki bayan ya gaidata tace

" haydar sai yanzon da na ganka hankali na ya kwanta dan d'azon taslim taje kai muku breakfast ta dawo wai tata mugawa ba,a bude ba, sosai hankalina ya tashi dan gaskiya fatima tana bani tsoro.

murmushi haydar yayi sannan yace

ummi ki kwatar da hankalin ki bazata yimin komai ba duk cika baki ne kawai.

shiru tayi zuwa cen tace toh ina fatiman ko bazata gaishe mu bane.

dukar dakan shi yayi sannan yace

ummi bacci take har yanzon bata tashi ba .
Chapter 16 · 0% Book details