← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

mikewa fatima tayi zata bar wajen taslim tace sister dan Allah ki rage nuna ma yaya haydar kiyayya abin da kk yi sister yayi yawa gashi har kinsa ummi ta farajin haushi ni ban san me yamiki ba har kk tsane shi haka.

cikin kuka fatima tace bakisan abin da yamin bafah kk ce ?, duk wannan abun da ya faru waya jawo shi inba shi ba, ai yasan yaya salis bazai so ace baya gurin ba amman ya wuce gantalin shi inda beje neman shi ba da yanzun muna cikin farin ciki, dan haka ni gaskiya bazan taba ganin farin haydar ba, ya cuce ni ya rabani da farin ciki na, ke badan ina tsoron Allah ba dasai na kashe haydar in yaso nima akasheni, dan rayuwana bata da wani amfani

muryan ummi sukaji tana fadin aiko zaki bar gidan nan tun da kin fara fado kalmar kisa bari alhj ya dawo.

batace komai ba ta koma daki taci gaba da kukan ta zuwa cen taji shigowan su daddy harda babanta azuciyarta tace ankawo Dan iskan nan kenan.

baya su alhj yusuf sun rako hayadar gida sun koma, ummi da daddy suna zaune abakin gadon da haydar yake ummi tace alhj Ina da magana.

toh inajinki me ya faru?

alhj ni gaskiya nagaji da zama da fatima ta koma gurin mahaifiyarta.

damamaki akan fuskarshi yace me kuma ya faru?

komai ta kwashe ta gayawa alhj haydar najin su .

nufasawa alhj yayi sannan yace

" wlh hafsat kin ban mamaki yazun sabo da Allah fatima zaki biyewa wa , menene ke damun fatima yan zun ban da kuruciya da zafin mutuwan salis dan Allah karki kuma saka wannan mgnr a lissafi idan kinji tana irin wanna mgnr nasiha zakiyi mata ina tabbatar miki da ace nasiha kike mata da tuni ta bari, kuma daga yau inason ki dauki fatima kamar taslim.

ummi tace shikenan alhj dama ni tsanar da naga tana nunamai ce tayi yawa.

wannan babu ruwan ki ni nasan maganin abun zama ta bari ne.

suna cikin haka haydar yace daddy inason na dan watsa ruwa.

da sauri daddy ya mike ya kama haydar ya mikar dashi tsaye ummi ta mikamai sandar sa daddy na rike da daya hannu shi har suka isa toilet din dake dakin , ummi fitowa tayi ta barshi da daddy zuwa cen shima daddy ya fito.

washegari da daddare daddy yace wa ummi ki shirya maza kizo muje cen babban gida.

kallon shi tayi tace

" alhj kana nufin haka zamu tafi mubar haydar shi kadai idan wani uzunrin ya tasan masa fah gashi taslim tana cen gidan.

gaba daddy yayi yana fadin nifa banason mita kizo muje yan zon zamu dawo.

haka ummi tabi bayan shi badan ranta yaso ba.

fatima ko tana ganin fitan su ta sake wani murmushi wanda rabon da tayi irinshi tun kafin rasuwan yaya salis tashi tayi da sauri ta nufi dakin haydar ahankali ta tura kofar ta shiga

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[9:33PM, 4/1/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

46-48

Ganin shi tayi kwance yana bacci a hankali ta isa gaban shi kare mashi kallo tayi sannan taje saitin kafar dake da ciwon ahankali tasa hannu ta rike kafan.

ganin da tayi be motsaba yasa ta dage iya karfinta ta murde kafan, kara ya saki me firgitarwa.

uhun da yake besa ta saki kafar ba ci gaba tayi da murdewa.

haydar ya hada zufa yana kurma ihu zuwa cen ta saki kafar ta matsa nesa da gadon ta kwashe da dariya.

haydar ko ihu yake yana salati yana kiran ummi da dadddy .

bayan fatima ta gama dariyarta ta tsaya ta hada fuska sannan tace haydar kadan ka gani indai ni ce kuma da izinin Allah sai an yanke kafar nan, fita tayi adakin ta koma nasu dakin ta kwanta daga dakin tanaji uhun da yake, amman ko ajikin tana cikin bargo ta shige ta rufe idanuwa.

zuwacen taji shigowan ummi aguje tana fadi ihun me kk yi haydar.

ganin shi tayi kwance inda ta barshi sai dai ya mirgina yana kokarin kai hannun shi kafar yana fadin zan mutu daddy Ku taimake ni.

adaran ranar dai basu runtsa ba suna kan haydar kwana yayi yana kuka da kafa dan haka washe gari aka fara cukucukun barin kasar dashi.

fatima ko ranar tayi kwanan farin ciki

da safe alhj yusuf yazo suka dauki haydar aka maidashi asibiti.

bayan tafiyan sune ummi ta shigo dakin su fatima ganin ta tayi zaune tana duba takardun makarantar ta saida ta kare mata kallo sannan tace.

yanzon sabo da Allah fatima abin kikayi ya dace kenan?

jitayi gaban ta ya bada dam dan ta zata haydar ya fada abin da tamai ne dan haka ta kasa cewa komai.

ummi ce ta sake cewa yanzon fatima zakice bakiji ihun da haydar ya kwana nayi ba.

mikewa tayi mama ni gaskiya banji ba bari naje na duba shi.

mama tace ai an mayar dashi asibiti inagama kasar za,a bari dan abin yayi tsanani

washegari aka wuce da haydar London domin asake duba lfyr kafan shi.

*******

bayan tafiyan haydar hankalin fatima ya kwanta dan yazon har tana sakin jiki da kowa na gidan ayi hira ayi dariya amman fah duk ranan da salis ya fado mata haka zata zauna taita kuka har ummi ta saba dan dataga fatima na kuka sai tace abin ya motsa.

kwanci tashi ba wuya gashi har haydar ya cika wata hudu da tafiya kuma da alamun ansamu na sara dan ayau daddy da baba yusuf zasu dawo dan haka yau ummi taketa garke girke taslim da fatima ke tayata.

4:13pm su daddy suka iso gida anas ne ya dauko su.

bayan sunci abinci sun huta ummi ta kalli alhj yusuf tace baku bani lbrn haydar ba.

yace keda kuke waya kullum kuma kike tambaya na jikin shi, ai nace abin naki ko kara babu ke ki kira salamatu ta kira.

dariya ummi tayi sannan tace wlh alhj ciwon ne ya bani tsoro dashi nake kwanciya dashi nake tashi dan gani nake kamar za,a yan ke.

dariya su alhj sukayi sannan daddy yace ai shima har roko yake wai dan Allah ayan ke mai .

ummi tace Allah sarki babana ai yaji jiki.

taslim tace baba yanzon yaya haydar yana tafiya kamar da?

yace ras yake tafiya taslim ai sati me zuwa zai dawo

fatima ko daure fuska tayi domin kuwa bata ji dadin lbrn ba dan ta tabbatar haydar ba zai bar ta ba dan haka hankalin ta yafi na barawo tashi, sai faman zare ido take.

ummi tana lura da halin da fatima take ciki zuwa cen tace alhj na gaya muku abin da kuke kokarin shiryawa bazai yiyuba yanzon ka dubi halin da fatima ta shiga.

hakalin kowa komawa gurin fatima yayi daddy yace fatima me ya faru ?

dukar dakai tayi sannan tace babu komai.

alhj yusuf yace dan Allah ku rabu da ita nasan maganin ta ya nunata da hannu sannan yace wlh karki yadda ki kaini bango dan wlh zanci mutuncin ki fiye da inda bakya zata.

daddy ne yaja alhj yusuf suka fita waje

bayan sati daya
ummi da taslim ne keta girkin tarban haydar ummi ta kalli taslim tace taslim fatima tana bani mamaki kiri kiri take nuna tsanar haydar yanzon ki duba fah hatta me gadin gidan nan murna yake haydar zai dawo amman ban da fatima... wayar ummi ce tayi kara cikin rawan jiki ta dauka tana Fara,a tace haydar yaya ka sauka ne?

daga cen cikin wayar aka bata amsa eh ummi gamu nan ma anas ya dauko ni.

murna ce ta rufe ummi ta mike ta nufa daki.

2:58pm suka iso gidan fira suke suna dariya shida anas amman abin da yaba anas mamaki suna shiga gidan haydar ya daure fuska zuwa cen ya fara kwafa anas ya kalleshi yace haydar lfy kuwa ?

Hmmm anas ina tunanin abin da zanma yariyar nan ne kasan Allah sai tayi nadamar zuwanta duniya

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊🕊
[7:55PM, 4/2/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

49-51

Anas yace wacce yariya kenan?

" saida yayi kasa da murya sannan yace fatima"

da mamaki anas yace meta maka, ai kamata yayi yanzon ka rinka tausayawa yariyar nan tun bayan rusuwan salis saboda ta shaku da salis.

Hmmm dan ta shaku da salis kuma saita nemi kashini ita fah ta tayar min da ciwan kafar nan saboda taga bana iya tashi tabini har daki ina kwance akan gadona dan tsabar mugunta tazo ta bankaremin kafah.

,dariya anas ya fara sai da yayi me isarsa haydar na kallon sa zuwa cen yace toh ya isheka wlh ka kiyayeni ina nan yadda kasanni ba cenzawa nayi ba

anas ya gintse dariyar shi sannan yace abin ne yabani dariya kaiko kana kwance kabari karamar yariya kamar fatima ta gana maka azaba, kodai mafarki kayi?

dariya haydar yayi sannan yace wlh ba mafarki bane toh yazanyi bacci fah nakeyi kawai naji anrikemin kafah ni kasan ma abin da yafi bani haushi idan na tuna uhun da na kurma amman sai naga ta koma gefe tana kyalketa dariya wato zatace tunda salis ya mutu gara nima na bishi.

anas yace ni kuma atunani na kodai fatima ta gane cewa kaine wadda ka lalata mata rayiwa?

zaro ido haydar yayi sannan yace bana tunanin haka kaima ka daina wannan tunanin idan ba haka ba zaka sa na fasa abinda nayi niyya.

da haka suka shiga falon ummi , ummi ko kunya babu ta mike ta rungume haydar shima kwaciya yayi ajikin ta tana buga bayan shi kamar me lallashin yaro yayi bacci tana fadin mu godewa Allah babana Allah ya karbi addu,a mu.

yana murmushi yace ummi ina godiya da nuna soyayyar ki agareni bansan kuna sona ba ummi sai da ciwon nan ya kama ni.

daga kanshi ummi tayi sannan tace haydar akwai wadda zai haifi dansa yace baya so daman cen munason ka halinka ne bama so dan Allah ka gyara halayen ka ka koma kaman salis
Chapter 14 · 0% Book details