← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

daddy yajuyar da kallon shi ga haydar yace kaifah

Sosa keya yayi sannan yace daddy ni ba yanzon ba.

sai yaushe?

daddy idan na shirya zanyi mgn

cikin fada daddy yace baka isaba rana daya zakuyi aure KO kaki KO kaso kanajina?

daga kai yayi sannan yace daddy inason zamuyi mgn amman su taslim su fita tukum

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊

[8:17PM, 3/24/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

*Gaisuwa ta mussaman gareku*
_matar abbatie barno_
_hussaina faji_
_murjanatu_
_yahancy_
_hajju_
&
_zinat_
*all in Fadeela Lamido novels group*

24 - 26

Daddy ne ya umarci su taslim da fatima da su fita

bayan sun fita daddy yace toh inajinka.

saida haydar yayi kasa da murya sannan yace daddy dama shawara zan bada yariyar nan fa be kamata salis ya aure ta ba, dan sai da ta gama yawon ta tukun aka kawo ta gidan nan.

da mamaki daddy da ummi suke kallon haydar

daddy yace a ina kaji wannan lbrn ?

kanshi tsaye yace yadidko ce ta fadamin

sai alokacin salis ya dago kai ya kalli haydar

daddy yace hjyr da kanta ta fada maka haka, toh gaskiya bahaka lbrn yake ba kuma ko ba ayi haka ba dama zangawa salis halin da fatima take ciki sannan yajuya barayin ummi yace ke dama tun zuwan fatima gidan nan nafada miki halin da take ciki.

kai kuma haydar karna sakejin wannan kallamar abakin ka fatima bata yawo fayd'e aka mata shine dalilin da mahaifiyarta ta kawota.

kan salis na kasa har yanzun be dago ba hawaye ne kawai ke zubo masa.

ganin halinda salis ya shiga daddy yace wa haydar tashi ka tafi.

mikewa yayi yana kallon salis yana mai farin cikin yau ya dana tarkon shi adai dai.

yana fita daddy ya mike ya taho kusa da salis hannun shi yasa ya dago kansa ganin fuskar yayi tajike sharkaf da hawaye ahankali ya fara sharemai hawayen sannan yace kayi hakuri babana kar kace wannan abun zaisa ka fasa abinda kayi niya inason ka yadda da kaddara mekyau da mara kyau wannan abinda ya faru da fatima zai iya faruwa DA kanwar ka taslima kuma baza mu so taki aurowa ba saboda wannan dalilin, dan haka ka daure,

bece komiba ya mike ummi tace kuma duk abinda haydar zai fada maka karka saurareshi dan na kula so yake ya lalata mgnr.

daker ya bude baki yace toh

yana fita falo yaga wata yariya ta shigo
riga da wando ne jikin ta sunyi matukar matseta cikin mamaki yace lfy wa kk nema.

cikin hausarta wacce bata fita tace dan Allah Ina Neman haydar ne

bece mata komi ba ya yamutsa baki ya shiga daki, yana shiga yacewa haydar kayi bakuwa kaje ka sallameta tunkafin ummi ta fito.

atsorece haydar ya fito yana fadi axuciyar shi wacci yar iskar ce zata Jamai masifa

yana fita sukai arba da ita, wata budurwar shice wacci suka kwashe kusan shekara biyu basu hadu ba suna hada idon suka sakar wa junan su murmushi cikkin sauri ya kamo hannun tasuka fita

salis na lekensu ta window har suka fita sannan ya koma kankujera ya zauna yayi tagumi yana bakincin wannan abu dazai ga wanda yayiwa zahara wanna abu lallai bazasu rabu lfy ba, daren ranar kasa bacci yayi haydar kuwa tunda ya fita sai 7:33am ya dawo lokacin salis ya fito wanka yana kokarin saka riga.

yana shigowa ya fara fadin angon fatima meye lbr kodai haryanzon kana kan bakar ka .

banza yayi dashi ya dauki key din motar sa yayi waje

haydar ko bayan yayi wanka yau be nufi office ba, gidan su wata budurwar shi yaje ya daukota yakaita dakin anas.

ad'akin ya wuni da mubaraka saidare ya maidata gida har ya kama hanyar gida yaji shifa har yanzun hakalin shi be kwanta ba so yake ya sake kasan cewa da wata nan ya fara tunanin wacce yariya zai d'ako wadda zata kwantar mai da sha,awar shi.

tunani ya fara yi cikin yan matan shi wad'an da yake harka dasu wan da besan yawan suba dan sufi dozin, kasa tuna ko guda daya yayi sai dai abinda ya bashi mamaki daya fara tunanin girjin fatima yake gani lokacin da takewa salis shagwaba, lashe baki yayi sannan yace inama nine salis na samu damar da yariyar nan takema wannan girgiza kasa daina tunanin fatima yayi dan haka daganan ya wuce mashayar su yasha yayi tatil besabo komawa gida aranar ba sai washe gari.

damuwa ya taro yayiwa salis yawa abin duni ya isheshi yau haydar kwana biyu kenan be kwana gida ba yana cikin tunanin nan wayar shi tayi kara yana dubawa yaga anas ne abokin haydar da sauri ya dauka cikin faduwan gaba yace anas ina haydar.

daga cen cikin wayar aka bashi amsa gayin nan dama nakiraka ne kazo ka shiga dashi cikin gida bayajin dadi ne, cikin sauri yadar ya mike ya fita.

ganin haydar yayi rike ahannun anas idon shi rufe, yana isa gurin warin giya ya daki hancin shi.
ja yayi da baya daidai lokacin hancin motar daddy ta sawo kai cikin sauri salis ya kama haydar yana kokarin barin wajen dashi, amman ina tuni daddy ya karaso guri yana fadin lfy meya sameshi, salis kasa mgn yayi anas ne yace beda lfy ne

daddy na isa gaban haydar yace innalillahi wa inna ilaihir raju,un haydar dama abinda kake kenan .

juyar da kallon shi yayi gurin anas yace kamayar dashi inda ka dauko shi nabar makushi kar ya Kara dakowa inda nake na yafeshi acikin 'ya'yana.

salis yace dan Allah daddy kayi mai hakuri.

kai salis babu abinda ya dameka dan haka maza ka shiga gida, Ku kuma Ku fitar min agida

juyawa yayi yana waiwayen dan uwan shi har ya shiga gida.

shiko haydar sai dare hakalin shi ya dawo jikin shi anas ya shiga fadamai abinda ya faru.

tashin hankali ya shiga sosai nan da nan ya mike ko sallama bema anas ba.

gidan alhj yusuf ya nufa ya sameshi zaune yana duba wasu takarddu

alhj yusuf yaji mamakin ganin haydar acikin daren nan dan basu cika zuwa gidan shiba sabo da ba mata gareshi ba binshi yayi da kallo sanan yace kai kuma daga Ina?

cikin rawar murya yace baba dan Allah ka taimakeni muje kaba Abba hakuri cewa yayi wai Karna kara shigo mishi gida.

atakaice alhj yusuf yace me ka masa?

kasa magana yayi sai hawayene keta zuba afuskar shi.

alhj yusuf ya sake cewa haydar me yasa bakajin maga ne ,alhj ya dade yana fadamin bakajin mgn kana mutukar bata mishi rai, jiya ya gama cemin wata ranama baka kwana agida, haka ne?

dukar dakan sa yayi kasa bece komai ba.

shima shiru yayi yana kallon haydar zuwacen yace tashi muje

bayan sun isa gidan atare suka fito daga cikin motar alhj yusuf ya dafa haydar yace haydar ko dai aure kk so?

dasauri ya girgiza kai.
murmushi alhj yayi sannan suka shiga har falon daddy

daddy na ganin su ya mike cikin fada yace

meyasa ka shigon min da wannan mashayin cikin gidana.

alhj yusuf yajuya ya kalli haydar yace mashayi kuma.

eh katon mashayi ne ka tambaye shi giya yake sha.

tsayawa alhj yayi shiru daga bisani ya dawo da kallon shi gasu taslim, yace kai ku tashi ku fita, ya juya ya kalli haydar yace kaima jeka dakin Ku.

suna fita alhj yace yaya ni inaganin koran haydar bashi bane mafita ai sai abin ya kara lalacewa addu,a zamuyi tayi Allah ya shiryeshi, kuma ni Ina ganin yakamata amai aure kila ta sanadin haka saikaga ya shiryu, haka yayita wa daddy nasiha cikin dabara har ya saki jiki suna hira.

bayan kwana biyu salis ne zaune shi da fatima ababban falon gidan suna hira kallon shi fatima tayi ta d'a hannunta tanuna mai yaya wai bakaga nayi lalle bane,

nagani Zahara yayi kyau sosai amman ni banason kinayi ki bari sai munyi aure, kinga kayan nan ma na jikin ki da zakiji mgn ta danace ki daina sawa idan kuma zaki saka toh ki daura hijjab akai.

turo baki tayi sannan tace waikai badama nayi ma kwalliya saika gwale ni.
murmushi yayi sannan yace bahaka bane zahara nagani kuma ya burgeni.

cikin muryan kuka tace toh ai baka kallaba.

ahakali ya mika hannun shi ya rike nata duk 2 yana kallon su ,zuwa cen yayi ajiyar zuciya cikin muryar rada yace zahara. dagowa tayi da sauri ta kalleshi cikin ido. yace hannunki laushi.

da sauri ta kwace hannunta tana rufe ido.

ahankali ya sake cewa zahara zaki iya gane mutumin da ya keta miki mutuncinki?
gabanta ne ya fadi dan bata taba zatan salis yasan wannan mgn ba .

muryar haydar sukkaji daga bayan su yana fadin toh iidan kasan shi me zaka mai?

cikin sauri sukka kalli gurin haydar ne tsaye hannun shi cikin aljjihun shi.

salis ya bude baki zayi mgn aka turo kofar falon ,wata budurwa ce agaba bayanta kuma wata matace dagani mahaifiyar yariyar ce

suna hada ido da haydar ya zaro ido yace me kika zo yi agidan mu?

babu ko alamar tsoro atattare da ita tace niba gurinka nazo ba, nazo ne ingayawa iyayen ka ina dauke da cikin ka

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:37PM, 3/25/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

27 -29

Da sauri ya farajan yariyar yana kokarin barin gidan da ita ummi ce taji hayaniya yayi yawa da sauri ta fito, ganin haydar najan yariyar ta fara dakamai tsawa cikin sauri ya saki yariyar yana mazurai, ummi takalli dadtijuwar matar da suke tare da yariyar tace sannu da zuwa hajiya shigo ki zauna.

ba musu tahau kujjera ta zauna fatima da salis ko kallo sukabi yariyar dashi.

haydar ko yana jingine jikin bango sai aikawa yariyar harara take

ummi ce taji shirun yayi yawa tace baiyawar Allah ban fah ganeki ba.

kamar jira matar take tace dama ai bazaki gane ni ba amman ai d'aki haydar bazai ce be gane mu ba, atakai ce dai hajiya Nazo ne na shaida miki 'yata zinat ta dauke da cikin danku haydar
Chapter 10 · 0% Book details