← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 29

Sashe 28

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:12PM, 5/6/2017] Fadila Lamido: 🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

97 - 98

Ban sani ba saika fad'a, ummi ke fadin haka cike da haushin haydar.

Dariya yayi sannan yace ummi toh ki sallame fatima sai muyi maganar.

Tace bazan sallameta ba idan ma bazakayi mgnr ba ka barshi, ta juya gurin fatima tace ke kuma ki kwantar da hankalin ki karya yake miki, cikin ki na nan lfy kalau, kema ban da shashanci irin naki ina kika taba jin ciki ya fita ta fitsari.

Turo baki tayi tana hararar haydar tana fadin wlh ummi shine yace min wai yanzon haka akeyi.

Juyawa ummi tayi ta rufe haydar da fada, dan haka ya warware mata kome.

Bayan ummi ta gama sauraran haydar komawa tayi kan fatima , daga karshe ta koma nasiha tare da lallashin ta da ta kwantar da hankalin ta.

Hawaye take sharewa, haydar ko ido ya zoba mata.

zuwa cen ummi tace toh kutashi ku tafi dare nayi.

Fatima bata tsaya jiran haydar ba gaba tayi , tana tafe yana binta abaya.

Suna shiga barayin su haydar ya rike fatima, yace

Wai fushi kk yi dani?

Rufe idon ta tayi domin ko ganinshi bata sonyi.

Saidai azuciyar ta koda taji cikin nanan batajin tsanar shi, saima wani sabon so da takeyiwa cikin, abin da kawai yabata haushi rainin wayon da su haydar suka mata.

Muryar haydar ce ta katse mata tunanin dayake fadin , fatima banayi haka da niyar yaudararki bane, naga awannan lokacin bani da kalmar da zan rarrashiki da ita ne idan ba wannan ba. amman kema inda kina da wayo zakisan baxan dauke ki da hannu na nakaiki acire miki cikin ba, ni yanzon abin da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu nan bada dadewa ba salis karami zai iso.

Murmushi ta saki har zuciyar ta taji dade kanta tasa akasa saiga hawaye yana zubo mata.

Haydar ya kalleta yace toh meye abin kuka kuma, ke babu damar ayi maganar salis saiki kama kuka, kina nufin kin fini sonshi ne?

Cikin kuka tace ban fika son shiba amman nafika kaunar shi.

nan danan fuskar haydar ta cenza, yace toh naji mubar maganan kawai.

Shiru tayi zuwacen ta sake cewa kaima wlh idan har zaka fadi gaskiya kasan har son na shima na fika.

Mikewa yayi cikin daga murya yace nace miki kibar mgnr ko bazakibar ta bane, juyawa yayi har ya fara tafiya ya bude kofar zai fita sai kuma ya dawo idon shi jawur cikin fada yace ai dole ne ki fini sonsa tunda tare aka hayfeku, kuma ni banson kina sonsa ba sai ranar da kika....... kasa karasawa yayi ya dafa kanshi da duk hannuwan shi guda 2 sannan ya girgiza kai ya fita.

Binshi da kallo tayi itama hawaye ciki da idonta azuciyar ta tace kodai haydar kishi yake da yaya salis idan ba haka ba yaya za,ayi daga mgn sai ya dau zafi haka, mikewa tayi tabi bayan sa ta sameshi adakin shi ya hada kai da gado.

Karasawa tayi ta dafa shi ko d'agowa beyi ba, tace yaya dan Allah da gaske kk yi sunnan salis zaka saka min idan nahaihu?

Wani sabon haushi ne ya kamashi domin da ace fatima tasan zafin dayake ji azuciyar shi idan tayi maganar salis da bazatayi ba, badan yanajin kunyan kar ummi tace yana kishi da d'an uwan shiba dasai ya fasa mata baki wata kila daga lokacin zata kiyaye shi, dagowa yayi da jajayen idonshi ya kalli fatima sannan yace

Ai badan ke zansa sunan ba dan kaina zan saka dan d'an uwa nane tare muka kwanta acikin mahaifiyar mu aka kuma hayfemu tare kuma mukasha nono tare muka girma ,dan haka duk wata kyauna dazaki nuna kina mai a bayan nine, dan ku su ummi da sukai sular zuwan mu duniya bazasu fini kaunar shi ba, bare ke.

Cikin fatima cike da dariya tace meda wukar, yaya daga wasa saika dauki abu da zafi aini wasa nake maka ni son da nake mishi ma ai dane, Allah ya huci zuciyar ka.

Fuskar shi adaure yace ke kika sani, fita kibani guri.

Kalon shi fatima tayi damamaki azuciyarta tace wannan wani irin kishi gareshi dan tunda suka shirya baya taba bari su raba shinfida amman shine yau harda koran ta.

Mikewa tayi da niyar ta fita adakin amman saitaji batason yin hakan saboda tafi kowa sanin halil haydar idai ko har ta fita adakin yau bazaiyi bacci ba wata kila ma sai yayi ciwon ciki, dan haka ta fara kokarin hawa gadon, gefen shi ta kwanta ta daura kanta ajiki shi.

Ahankali yace wai banace ki fita bane?

Itama daure fuska tayi sannan tace nifa bazan fita ba, kwanciya zanyi, kuma ai nace maka kayi hakuri.

Baza yayi da ita ya rufe ido dan haka fatima ta zuba hannunta duk 2 cikin rigar shi tana mai cakulkuli tun yana fadin meye haka bari mana, har ya fara dariya, daga karshe ya shiga ramawa.

Tun daga wannan rana suka kara kullewa kamar sa ahad'iye juna sabo da yadda suke nunawa junan su so, tun da fatima ta gane haydar baya son tana mgnr haydar ta daina yi agaban shi, saidai data tuna salis zata shiga daki tai kuka dan son da takeyiwa salis ajininta yake.

Ayanzun haka dai cikin fatima ya isa hayhuwa girma yayi sosai dan yanzo fatima zama da ker dashima haka, wani zubin idan fatima ta kalli cikin tsoro yake bata, daidai wannan lokacin ne aka tsaida bakin taslim ita da mubarak dane agun kawar ummi , kuma mahaifin shi hamshakin me kudi ne, ba,asa rana me tsayi ba sati 2 kawai akasa

Fatima bataji dadin saranar da akayi a wannan lokacin ba dako tafiya daker takeyin ta, dan haka lokacin da daddy yake sanar musu ta fara kuka.

Daddy ne ya lura da ita dan haka yace mamana yayadai?

Goge hawayen ta fara sannan tace daddy da anbari bayanzun ba, kagani fah bana iya tashi

Dariya sukayi sannan haydar yace ton idan kina iya tafiyar me zakiyi?

Bata kulashi ba ta sake cewa daddy dan Allah abari sainan da wata 1.

Fukar daddy cike da dariya yace mamana ki cire mgnr biki azuciyar ki mu fatan mu Allah ya rabaku lfy, wata kila ma kafin bikin ,kiga kin haihu, ina fatan dai duk kunsaya kayan haihuwa?

Kan fatima akasa tace nima ban sani ba.

Daddy ya waiga ya kalli ummi sannan yace kuna nufin ba,asai komai ba har yanzun?

Murmushi tayi sannan tace alhj komai yana hannu itace dai bata sani ba.

yace toh yayi kyau ina fatan dai komai 2 kuka saya?

ummi ce ta bashi amsa eh , daddy yace to ai yakamata ku nuna mata ko akwai wani abun da take so ba,a saya ba.

Ummi tace toh mijinta ne yace kar anuna mata.

Fada daddy ya farawa haydar akan me zaice kar anuna mata, daga karshe yace maza aje anuna mata.

Dakin ummi suka shiga ummi ce ke nuna wa fatima kayan haydar na zaune agefe.

Gani tayi komai 2 ake daukowa, daidai da bahon wanka ma guda 2 ne, dan haka tace ummi meyasa naga kayan komai 2?

Haydar ne yayi sauri yace, sabo da idan wani ya lalace ad'ako wani.

Harara fatima ta galla mai sannan tace ni bakai nake tambaya ba.

Ummi ta kallesu tayi murmushi sannan tace fatima haydar boye miki yake, likita yace yan 2 ne acikin ki, dan haka ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu lfy lau zaki hayhu.

Watsi tayi da kayan dake hannun ta tafara kuka.

Ummi ta bita da kallo nan danan hankalin ta ya tashi ,zuwacen ta mike tayi daki, saboda tsoro amai ta dinga kwarawa, haydar na biye da ita, zuwacen ta rike ciki.

Hankalin haydar ya tashi, wayar shi ya daga ya kira ummi ya gaya mata halin da fatima ke ciki, ba a dau lokaci ba saigata ta iso.

Ummi naganin inda fatima keyi tace wa haydar yi maza ka fito da ita muje asibiti.

Arikece haydar ya wawusu fatima yayo waje da ita

🕊🕊
Maman yazeed
🕊🕊🕊
[10:01PM, 5/7/2017] Fadila Lamido: 🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

*Na sadaukar da wannan page din ga iyalan 👇marigayi*

_Alhj Lamido Bello_

*Godiya ta mussaman ga yan group d'ina Fadila lamido novels ,bansan taya zan nuna farin cikina akan yadda kuke bani goyon baya ba, gasky Ina alfahari daku wannan page din bazai isa nakira sunan ku ba saidai nace Allah ya barmu tare*😍😍

Jinjina gareku

Faty Afreen
Cwtjiddah
zeezee
Billy galadanci
Ummi jafar
hussaina ubandiya
zeenasir
Aisha big girl
Yar gatan hudah
Yar mutan yudil
Hamagee
Fatima umar abdallah
Nana zee
Meenat tabacco
Anty sa,adatu

Marubutan👆 mu kenan

99 - 100✋

Kai tsaye asibiti suka nufa, daka kalli haydar kasan hankalin shi tashe yake, bayan anshiga da fatima dakin haihuwa ummi ta kalli haidar taga duk jikin shi yayi sanyi, dan haka ta matsa ta dafah shi tace ya haka kaida zaka mata addu,a Allah ya rabasu lfy kuma saikabi ka tada hankalin ka.

yace ummi ina tausayin fatima sai nake ganin kamar bazata iya hauhuwan yara har guda 2 ba.

Ummi tace Hmmm haydar kenan in Allah ya yarda lfy zata haihu lokacin dana haifeku nima ai kamar fatima nake .

Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa.

Zuwacen ummi tace haydar tashi kaje gida ka karbo min sako gurin taslim.

tashi yayi badan ransa yaso ba.

yana kokarin shiga gidan ummi ta kira wayar shi, cikin sauri ya dauka.

Muryan ummi yaji cikin fara,a tana fadin Alhamdulillah fatima ta sauka.

Alhamdulillah ya fara furtawa komawa yayi ya fada mota batare da ya karbi sakon da ummi ta tura shi ya karbo ba.

Yana isa dakin da fatima take ya nufah ya samu ummi da mama zaune adakin.

cike da fara,yake kallon su, mama tayi dariya sannan ta mike ta mikamai jaririn dake hannun ta, sannan ta dauko dayan ta sake mikamai , rugume su yayi ya kuresu da ido ganin yaran sunyi kama dashi sosai, idon shi cike da hawaye yace

Mama ina hasan din yake?
Chapter 28 · 0% Book details