← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk da kokarin kwacewan da yake besa ya saketa ba saima kara matseta da yayi a jikin shi yana kai mata sunba, tun tana kwacewa har ta gaji tayi lakwass ajikin shi, dan ta gane wahala kawai zatasha bazata iya kwatan kanta ba.

zuwa can ya saurara mata ya bude baki ahankali yace

fatima dan Allah kiyi hakuri ki yafemin nasan na miki laifi, ina rokon alfarma ki yafemin ki dawo gareni, ki daina biyewa zugar hajiya rudun tsufa ne yake damunta, kara kwatar da murya yayi yace fatima idan kika amince kika dawo gareni zan nuna miki son daba kowane namiji bane zai iya nunawa matar sa, ko kuda bazan bari ya tabaki ba.

tuni hawaye ya fara zubo mata domin kaman haydar ya tuna mata da salis, shima haka yake fada.

cikin kukan take fadin wlh bazaka iya ba, dan ko yaya salis daya fadi haka gashi ya tafi ya barni, naso ace yana nan asirinka ya tonu, da kaji kunya.

cike da takaici yace fatima har akwai wata kunya da ta wuce wadda naji yanzo kowa fah acikin dangin mu yasan halin da muke ciki, hatta taslim karamar kanwata ta daina girmamani , kuma da kike mgnr salis, wlh ni nasan da salis na nan shine mutun na farko da zai fara gafarta min, nasan zaiji tausayi na kuma zaiyi kokari yaga ya fitar dani daga cikin kunci, dan haka ina rukonki albarkacin son da kikeyiwa salis kiyafe min.

kuka take sosai dan haka ya jawota kan kirjin shi yana fadi Allah yajikan salis, Allah ya gafarta masa ubangiji Allah ka haskaka kabarin sa.

cikin kuka fatima ke amsawa da ameen ameen, dan haka ya kara matseta kamar zai sakata ciki.

saida suka kwashe kusan minti talatin ahaka, sannan fatima ta daga kanta ta fara share hawayen, cikin ido ta kalli haydar tace

kace duk abinda nake so zaka min ?

da sauri yace eh
me kike so ko menene ki fadamin.

cikin sauri tace toh cikin za,a cire min.

shiru yayi zuwacan yace to shikenan gobe zan zo na dauke ki, kamar karfe na zanzo?

tace ko da yaushe ne amman dai da wuri zaka zo .

mikewa yayi tare da fadin angama ranki ya dade, sannan ya zuba hannu cikin aljihu yace to zan wuce baki ce nagaida kowa ba.

dan ya mutsa fuska tayi sannan tace nidai inajiran ka, kazo da wuri.

shima murmushi yayi sannan yace toh saikin ganni.

yana fitowa ya kalli hajiya dake saune afalo yace duk d'an bakin ciki sai dai ya mutu.

yana fita hajiya tayi murmushi tace ja iri.

cike da farin ciki ya koma gida, washegari kuwa 9 agidan hajiya tamai, lokaci fatima na bacci saida yajirata tashi, tana bude ido kuwa ta fito falo da niyar tambayan hajiya ko haydar yazo, tana fitowa kuwa ta ganshi zaune kusa da hajiya, cikin sauri ta koma ta dauko gyale ta fito tana fadin muje.

saida hajiya ta kalli fuskar haydar sannan ta kalli ta fatima tace ina kuma zaku.

haydar ne ya mike sannan yace ina ruwan ki.

itama hajiya mikewa tayi sannan tace babu fah, amman dai fatima anyi wayon banza.

basuce komai ba suka bar gidan.

koda sukaje asibitin haydar ne kadai ya shiga zuwacen yaxo ya kira fatima.

bayan ta zauna agaban likitan ya juyo gareta ya fara mata bayani madam mijiki ya riga yamin bayani , zan baki magani amman kisani komai yana bukatar sirri, ki kama bakin ki karki gayawa kowa, dan maganin dazan baki yana da kyau bakowan ni asibiti ake samun shi ba, idan kika sha maganin ta fitsarin ki cikin zai fita, saidai maganin yana da duko ki.

sosai fatima ta maida hankalin ta gare shi.

yaci gaba da cewa kadan daga cikin ka idojiji sune cin abinci akan lokaci, ba,aso meshan wannan maganin na zama cikin damuwa
sannan idan zaki kwata bacci ki kwata ta gefe dama ko hagu idan kika kiyaye wad'annan dukokin ko kwana 1 baza ayiba zaki fitsarar dashi.

mika mata manin yayi sannan yace koda cikin ya fita kuma badaina shan maganin zakiyi ba idan ya kare saiku dawo na cenza muku wani, dan idan kina shan maganin bazaki dauki ciki ba sai ranar da kika daina shan maganin.

godiya sukayi sosai sannan sukayi mai sallama suka tafi

suna cikin tafiya haydar ya kalli fatima data zauna tayi shiru, yace fatima tunanin me kikeyi, kina son cikin ya fita da wuri kuwa?

inaso mana ai insha Allahu yau zai fita, shiru sukayi zuwace fatima ta sake cewa yaya haydar daman kai baka son yara ne?

daidai lokacin dazai karya kwanan gidan hajiya yace

ina so amman ba yanzun ba.

tabude baki zata sake mai wata tambayar taji yana fadin toh fah alhaji babba yadawo.

tana daga kaikuwa taga jerin motocin dake gaban su, ta tabbatar eh lallai alhaji salisu ne ya dawo

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:59PM, 5/2/2017] Fadila Lamido: 🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

93 - 94

Kusan tare suka isa gida, alhj babba na saukowa a mota suma suna fitowa, cike da fara, alhj ke kallon su, bayan sun shiga gida cike da anna shuwa alhaji salis ya zauna yaran shine guda 2 agaban shi gefe kuwa ummi ce da mama duk sunzo taryan sirikin su,

hardar da fatima ma suna zaune akasa, taslim ce kawai ta shige dakin hajiya ta boya domin yanzon basa zama inuwa daya da salis.

abinci aka baje kowa yaci ya koshi har fatima sake jiki tayi taita tura abinci, duk da cewa bason ci take ba.

bayan sun kammala ne kakan su alhj salis ya shiga tattaunawa da iyalan shi, haydar Allah Allah yakeyi yaji an sako zancen su da fatima.

zuwa can alhj yusuf yace baba bakace komai ba akan mgnr haydar da fatyma.

dasauri alhj salis ya maida kallon shi gare su yace ai na dauka kun gama komai, kuna nufin yanzon ba daga gidan su , suke ba, toh me kuke jira.

hajiya yadikko tayi caraf tace ai alhj bazata koma ba, sakin ta zaiyi idan Allah ya sauketa lfy tayi aure.

cikin sauri alhjn yace da wani dalilin, ai bazai yiwu ba wannan auren da kuke gani ko bayan raina ban yadda arabashi ba, abun da ya faru ya riga ya faru, gashi har ma naji kina cewa ansamu rabo.

duk shiru sukayi suka samusu kunne.

zuwa can hajiya tace alhj kana nufin duk rashin kunyan da haydar yayimin yace bulusss kenan, wacce kalma ce be kirani da ita ba, har fah habaici yake min, ko dazon saida ya kalli cikin idona yacemin duk dan bakin ciki saidai ya mutu.

d'an murmushi yayi sannan yace yamin daidai daya fad'a miki haka, yaga zaki kwace mai mata, ya juya ya kalli haydar daya dukar da kansa kasa yace

kai ka tashi ka dauki matar ka ku tafi gida, idan kana da hankali wannan kadai ya isheka ishara.

cike da farin ciki haydar ya fara godiya, fatima ta dago fuskarta cike da hawaye, hararar da alhj yusuf ya zafga mata yasa ta maida kanta kasa.

haydar kuwa tuni ya mike yaje gaban fatima yace tashi muje, ko saina d'aga ki?

hajiya ce tace to kuji irin rashin kunyar tashi ko.

cikin dariya alhajin ya kalli hajiya yace haba fatima me yasa kikeyin abu kamar wacce rikicin tsufah ya kama, me yakai kunnen ki gurin su.

shidai haydar tunda fatima ta mike tayi waje be tsaya jin me suke tattaunawa ba,
haka suka isa gida saikace kurame, fatima ko jifi jefi tana share hawaye.

suna shiga barayin su ta ganshi duk yayi kora duk da batajin kwarin jikin ta haka ta zage tashiga gyara gidan tana hawaye, shima haydar be zauna ba tayata ya shigayi.

zuwa can haydar yace wai fatima kukan me kikeyi inace mun riga mungama mgn, hannusa yasa ya riketa yace kibar aikin zan karasa, kije kiyi wanka sai kizo kisha maganin.

bayan fatima tayi wanka tasha magani nan bacci ya kwasheta batare da tasan lokacin ba, haydar kadai ya karasa aikin dan haka lokacin da ya fito wanka shima nan kusa da fatima ya kwanta gani yayi baccin nata yayi nisa dan haka ya dago kanta ya daura akan kirjin shi yasa hannun shi duk biyun ya zagaye ta

Sun dade ahaka gabadayan su bacci suke shararawa

su ummi kuwa sai yamma likis, suka dawo ita ma yau cikin farin ciki take dan haka suna dawo wa ta shiga kitchen domin daura abincin dare , tare da taslim sukayi komai suka gama.

sai kusan 5:59pm haydar ya farka yayi mamakin gudun lokacin, ahankali ya fara tashin fatima, ahankali ta fara bude idon, bata gama was tsakewa ba taji wani fitsari ya kulle mata mara dan haka ta tashi da sauri tayi toilet.

aguje haydar ya bita fitsari ya samu tana yi, saboda yadda fitsarin ya matseta har wani lumshe ido take.

haydar na rike da kofar yana kallon ta zuwacen yaji tace Alhamdulillah yaya haydar ka gani cikin ya fita.

dariya ce taso kwace mishi daker ya iya daurewa, yaje ya dagata yana fadin sannu fatima, har wani langabewa take wai ita adole ga me mara lfy

cikin haydar cike da dariya har suka fito falo, kan kujera ta kwanta tace toh kaje ka gayawa su ummi.

daure fuska yayi sannan yace kin manta abinda likita yace, ko bakisan komai da sirri yafi ba.

turo baki tayi sannan tace toh idan sukaga ban haihu ba fah.

yace babu ruwan ki ,kibarni ni zansan yadda zanyi nagaya musu.

********

washegari da daddare haydar ya shiga dakin fatima cikin shigar da fatima keson gani zama yayi kusa da ita sannan yace fatima ya kamata ace zuwa yanzon musan abinda muke yi , ya kamata mugyara zaman mu, mudunga sauke hakkin junan mu, muyi zama naso da kyauna, bana umarni ba.

ahankali ta daga idon tace waye zai so ka yayama za,ayi naso yaya salis sannan kuma naso ka.

fuskar shi daure yace fatima ki daina yaudaran kanki, kuma ni banason kinamin maganar salis indai ba addu,a zakiyi mai ba, matata ce ke, kuma nina san kina sona yaudaran kanki dai kawai kikeyi.
Chapter 26 · 0% Book details