← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

murmushin munta haydar yayi sannan yace

ummi waifah nan kunya taji dan kin ganta adakina.

itama ummi murmushi tayi sannan ta kara rugumo fatima jikin ta tace fatima menene abin kunya ke da d'akin mijin ki aini yau hankali na ya kwanta, Allah ya kara had'a kawonan ku , ko ma kiyi kwanciyar ki.

kuka fatima ta kara fashewa dashi tana buga kafarta akasa take fadin wlh ummi ni d'akina zan tafi ai ko jiyama bani nazo ba shine ya kawo ni.

da sauri ummi tace toh ya isa haka ni ban tambaye ki ba.

haydar na kallon fatima yana fadin ummi ji abin da take yi haka fah taitamin jiya.

fatima ce ta wurga mai wani kallo cikin ido tace wlh ummi ni karya yake min.

daure fuska ummi tayi sannan tace toh ya isa haka ke fatima meke damun ki?

tana share hawaye tace ni wlh karya yakemin lfy ta lau.

cikin sigar wasa ya harareta sannan yace amman dan tsabar muguta shine kika hanani bacci daga yau ko zaki kwana kina koke koken ki bazan kara kulaki ba.

ummi juyawa tayi tana fadin kudai kuka sani

ummi na fita fatima ta fashe da kuka.

haydar ko daure fuska yayi sannan yace ke fatima kk KO wa, daga yau duk ranan da nayi magana kk sake cewa karya nakeyi zaki gane shayi ruwa ne, tafiya ya farayi sannan yace kuma kafin ki fita ad'akin nan ki tabbatar kin gyara shi , dan ni bana son kazan ta.

yana fita fatima ta mike tana kuka take gyara dakin bayan ta gama d'akinta ta nufa saida ta gyara ko ina sannan tayi wanka tayi ras da ita.

shiko haydar yana fita bayan gidan ya nufah cikin dan wani lungu ya zauna sigari ya ciro aljihun shi ya kunna ya fara sha, besan meye dalili ba haka nan yaji baya son ya batawa fatima rai dan haka besha ad'akin ba ,sai da yasha ya koshi sannan ya nufa dakin ummi.

yana turo kofar fatima na sawo kai zata fita ad'akin , da saurin ta kalle shi tatoshe hancita ta kwasa da gudu tayi bayan ummi, tsugunawa tayi ta kudundune abayan ummi.

da sauri ummi ta mike ta rike ta daidai lokacin haydar ya karaso wajen.,

KO me ya tuna kuma sai ya fita da sauri.

fatima na ganin fitan shi ta mike . ummi ta kalleta sosai sannan tace anya kuwa fatima ba aljanu gareki ba, ya za,ayi daga ganin mijinki ki daka wannan uban tsalle.

wasa da yatson hannun ta take ga kuma hawaye na fitowa afuskarta ahankanli tace ummi nifah banason warin sigari, kuma yaya haydar sai ya dinga sha yana shakamin hayakin.

da sauri ummi ta dafa kirjin duk da cewa bataji mamaki ba domin kwanakin baya tasan har giya haydar na sha
saidai tana ganin kamar mutuwan salis yasa
ya bari , da sauri ta dago kai tace fatima haydar d'in ne yake shaka miki hayaki kina nufin har acikin gidan nan yana shan taba?

da saurinta ta daga mata kai.

tace toh shenan zanyi manin abin.

haka kwanaki sukaita tafiya har aka kwashe wata uku babu wani jituwa tsakanin haydar da fatima , saidai wani abu da fatima bata saniba tun ranan da ya labe yasha sigari yadawo gida yaga fatima na toshe hanci be sake sha ba
dan haka yayi kyau ya Kara haske.

kaman kullum yau haydar na zaune a office d'inshi anas ya shigo tare da sallama.

mikawa juna hannu sukayi cikin Fara,a , anas na zama yasa hannu a aljihu ya
dauko sigari yana kokarin kunnawa ,cikin sauri haydar yace

" dan Allah akarka kunna min ita anan kaje waje

kasha abinka kasan fatima bata son warinta karkajamin na koma gida tana toshe min hanci

dariya sosai anas yayi sannan yace

" a lallai Fatima ta samu shiga yanzun kana nufin kabar sha kenan tunda bata so, ko shiyasa naga kwana 2 kabar daukan yariyar ka?

Murmushi haydar yayi sannan yace

" bawai na daina sha bane, inason sha hakura kawai nakeyi ban san me yasa ba konayi niyar sha dana tuna fatima saina maida kasan wani abu dayake bani mamaki kofah awaje nasha sigari ina shiga gidan take ganewa har fah wani toshe hanci zakaga tanayi kamar taga kashi.

dariya anas ya sakeyi yace nikuwa wlh yadda na saba da sigari babu wata soyayya dazata sa na bari.

mikewa haydar yayi tare da fadin dallah gabara waya fad'a maka sonta nake inma tunanin ka kenan toh gara ka cenza nime zanyi da fatima yariyar da ko kwalliya bata iya ba tsaki yaja yabar wajen.

yana shiga gida barayin su ya nufah fatima ya gani zaune tayi tagumi hawaye nabin kuncin ta, har ya wuce ta ya dawo ya tsaya agaban ta , hannuwan shi ya zuba cikin aljihu wandon shi sannan yace ke menene?

cikin muryan kuka tace toh ba ummi bace ta hanina zuwa gidan baba, kuma tabar taslim ta tafi.

murmushi yayi harda sauti sannan yace

" shine kika zauna kina kuka zaman kanki kikeyi kin tambaye ni ne ko ummi ce take auren ki , tamin daidai dan wlh da ace nadawo na samu baki nan harcen zan biki naci miki mutunci.

mikewa tayi cikin kuka ta nufi d'aki.

shima bayanta yabi tana shiga dakin ta fad'a kan gado tsaye yayi ya bita da kallo wani yanayi yaji ajikin sa wanda ya kasa fassara shi da sauri yasa hannun shi ya d'ago ta yana fadin tashi ki zauna zan kaiki amman da sharadi .

tona kuka tace eh naji kafada ni koma menene zanyi indai zaka kaini.

yana d'an dariya yace ai bawani abu me wahala bane kawai inason ne nizan baki kayan da zaki saka.

da sauri ta fara share hawaye tana fadin wlh zan saka.

yana murmushi ya fita adakin zuwacen ya dawo da wasu kaya rike ahannun shi mike mata yayi ta bude riga da siket musu d'an karan kyau aciki sai wani d'an karamin gyale.

daga kayan take tana kare musu kallo zuwacen tace

" yaya wadannan kayan fah sumin kadan bazasu shigeni ba"

tafiya ya fara yana fadin babu wani kad'an da zasu miki idan kinason zuwa ki sa saiki sameni amota.

ba yadda ta iya tanason zuwa dan haka ta saka ta fito bata shiga barayin ummi ba Kai tsaye ta nufi motar haydar tundaga nesa yabita da kallo.

bayan sun dauki hanya ma satar kallon ta yake dan idan kaga yadda kayan ya amsheta sai ka rantse da Allah ta saba sakawa, sunyi nisa da tafiya mutar ta tsaya sakowa haydar yayi ya fara yan tabe tabe har ya gaji motar bata tashi ba, dan
haka yace da fatima ta sakko su karasa da kafah.

koda fatima ta sakkko sai da ta jajjawo rigara sannnan suka fara tafiya

yamma ce dan haka unguwar cike take da gungu gungu na maxa kuma abin da haydar ya lura dashi duk inda sukabi fatima akebi da kallo take yaji wani haushi ya kamashi, duk da cewa wannan bashine karon farko da ya fara yawo da mace ahakaba, toh meyasa naji haushin wannan tambayan da haydar yayiwa kansa Keenan

wani majalisar samari ya sake hangowa agaban shi gani yayi tun kafin sukai gurin samarin suna waigowa dan haka ya juya ya kalli Fatima ya daure fuska sannan yace

" ke kina nufin tacikin mazan nan zakibi kuma a haka

turo baki tayi sannan tace to bakai bane kace na fito haka.

cikin sanyin murya yace bar wannan maganan fatima kinga ga wani gida nan kishiga ciki kice dan Allah su aramiki hijjab

Mmn Yazeed
[8:52PM, 4/15/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

67 - 69

Kallon shi tayi sosai sannan ta turo baki tace

" ni dai gsky baza ni ba haka kawai bansa mutanen gidan ba kuma sai naje aron hijjab.

kara daure fuskar shi yayi sannan yace fatima Ina wasa dake ne?, maza ki shiga tunkan raina ya baci.

buga kafa ta fara tana fadin ni dai kazo kawai mutafi nina gaji da tsayuwa.

haydar sakin baki yayi yana kallon fatima komai dake jikinta rawa yake, hankalin shi kara tashiyayi dan haka ya matsa daf da ita cikin tsawa yace

" baki da hankali ne bakyaganin mutane na kallon ki?

"tace toh kazo mutafi mana"

cikin tsananin bacin rai yace bazamu ba idai har baki shiga kin ara hijjab ba toh sai dai mukoma gida.

tuni fatima ta fara ganu haydar kishin ta yake , dan haka ta kara dakewa tace

" aiko sai dai mukoma dan wlh bazanje aro ba, toh wai kai meya da meka dani dazaka ce saina saka hijjab.

da saurin sa yace bansani ba mara kunya kawai ai zan kamaki ne .

murmushi fatima tayi tana kallon haydar ta gefen idon ta sai wani hura hanci yake idon shi ko jawur waya taga ya dauko daga aljihun shi ya fara dannawa matsawa yayi cen gefe dan haka bata san dawa yayi waya ba, tsaye sukayi gaba dayan su, zuwacen ta hango motar anas na tahowa, gaban su ya tsaya da sauri haydar ya bude gaban motar ya shiga.

anas ne yaga fatima bata da niyar shiga dan haka yace madam shigo mana.

ahankali ta fara tafiya kamar wadda kwai ya fashewa aciki tana shiga anas yaja motar.

haydar yana zaune ne ya had'a fuska becewa anas komai ba, ahankali anas ya kalleshi yace

big boy ya dai ?

take gaban fatima? ya bada damm dan bazata taba manta wannan sunan ba, kuma tun bayan mutumin da ya keta mata haddi bata sakejin ankira wani da irin sunan ba sai yau,

muryar haydar taji yana fadin wannan fitsarariyar yariyar ce ta batamin rai.

murmushi kawai anas yayi adai dai lokacin suka isa gidan .

fatima bata saurare suba ta bude motar tafita ko waiwaye babu .

da murnanta ta shiga d'akin mama dan tunda akayi bikisu bata taba zuwa ba.

mama na kallon fatima tayi salati sannan tace yau kuma mezan gani fatima abin da bakiyi kina budurwa bane sai yanzon zaki tsiro dashi , duba jikin ki fah duk awaje.
Chapter 18 · 0% Book details