← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan salamatu ta isa kano acinkin wani akauye ana kiran sa mai giginya bata kara marmari komawa gida ba agidan me unguwa aka sauketa bayan wani lokaci ta samu mijin aure wato malam habu.

lokacin da ta aure malam habu tasame shi yana da uwar gidan shi me suna baraka tasha matukar wahala awajen baraka ita da yarta fatima zagi iri iri babu wanda ba,ayi musu ba ita ta Fara kira fatima da suna daniju saboda tsabar bakin cikin cikin da takeyi da ita kuma sai sunnan ya beta acikin kyauyen.

kazafi kuwa kullum cikinyin sa take

*Cigaban Labarin*

bayan fatima ta gama shiryawa direct gadon dada ta nufa ta kwanta tana mai bakin cikin abun da ya faru da ita.

sai dare malam ya shigo gida ya tararda abinda ya cire tsanmani woto salamatu da jikar shi fatima .

bayan kwana 2 dada ta kira salamatu bayan ta zauna tace

" nakiraki ne domin na fada miki shawaran da muka yanke da baban ki kuma dole ne ki daure ko ya miki dadi ko be miki ba"
baffan ki yace yau dinnan akai fatima gidan kakan ta, saboda idan suka samu lbrn dawowar ki batare da munfada musu ba zasu zargemu kuma dama kyawun da gidan uban sa.

ahankali ta bude baki tace shi kenan Allah yasa haka shine maffi alheri.

fitowa tayi ta leka dakin da fatima take taga sai hada kaya take, ahankali ta kira sunan ta ta dago ta kalleta tace

" karki dauke komai daya danganci kayan sakawa naga sai wani rawar jiki kikeyi"

turo baki fatima tayi sannan tace toh mama ba dole nayi rawar jiki ba, ban fah taba ganin babana ba kuma idan na tafi babu kaya wani kayan zan rinka sakawa.

murmushi mama tayi sannan tace fatima kenan ai wannan kayan naki ko goge kitchen din su bazasuyi dashi ba dan gida ne namasu hali, babanki kuwa harsai kingaji da ganin sa , dan nasan idan ya ganki bazai kuma bari kizo gurina ba, dan haka zanci gaba da miki andu,a Allah tsareki aduk inda kk

maganar dada sukaji dana fadin toh fatima fito mu tafi.

cikin sauri ta fito domin kuwa bakaramin kosawa tayi ba tana tafiya tana fadin mama na tafi

toh kawai salamatu ta iya furtawa zuwacen ta kira sunan fatima ta dawo ta tsaya tace gani

ahankali tace kicewa babanki inagaida shi

toh kwai tace tabi bayan dada aguje,

suna fita ta saki kuka me ban tausayi.

🕊🕊
Ummu Yazeed
🕊🕊
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
: *_Fadeela Lamido_*

9-11
Tafe suke kowa yayi shiru babu mema wani magana salis ne ke jan motar yayin da taslim take gefenshi daddy da ummi ko suna baya sunyi shiru kowa da kalan tunanin shi duk da dai baya wuce tunanin dansu suke wato haydar dan uwan haihuwan salis, da haka suka isa gidan, salis nayin pakin taslim ta fita da gudu tayi cikin gidan.

bin bayan ta sukayi suna shiga suka sameta ta kwakume fatima tana kelketa dariya yayin da fatima kebinta da kallo tana murmushi.

yadidko ce ta fito daga daki tana fadin muryar wa nakeji, daidai lokacin iyayen suka shigo ummi ce ta kalli fatima tace

taho nan yata bayan ta zauna tazo gabanta ta zauna Hannun ta tasa ta kwatar da ita jikinta tana shafa kanta yadidko nakallon su tana murmushi.

taslim tace ummi muwuce da ita gida.

kafin ummi tayi magana yadidko tace ina aibaku isaba nan zata zauna.

" sai alokacin salis yayi magana danshi baifaye surutuba ahankali yace

" kunjita saikace ke kika haifet.....

bekai ga karasawaba daddy ya dakatar dashi da fadin kafara ko ?

yadidko tace barshi yayi ai bashi da kunya waima ina daya fitsararren ne?

shiru daddy yayi yasa kan sa akasa sai ummi ce tace yana cen wajen gantalin sa.

fada yadidko ta farawa ummi tace

" karna sake jin kince masa gantalalle kefa uwace addu,a ne ya dace dake ba mugayen kalamai ba Haba aiko dan sunan mahaifinki da yake dashi kyaraga masa.

kan ummi akasa tace toh nabari hjy.

suna cikin haka alhj yusuf ya shigo da kaya riki riki acikin manyan ledoji.

salis ne ya mike ya karfi kayan

alhj yasuf yace
kasa kayan amotar ku kayan kanwar ka ne gobe sai kakai mata dinki.

cikin sauri taslim tace baba yaufa da sister fatima zamu tafi.

murmushi yayi sannan yace Allah ya bada sa,a taslim.

mikewa tayi ta daka tsalle sannan tayiwa yadidko l gwalo .

murmushi dada tayi sannan tace ja,ira zanyi maganinki ne.

mikewa daddy yayi yayiwa mahaifiyar shi sallama sannan ya kalli ummi yace idan kungama ku fito
yana fadin haka ya juya ya fita. alhj yusuf ne ya mike yabi bayanshi.

bayan kamar 11 minutes suma suka fito harda fatima.

bayan sun isa gida taslim da fatima daki daya suka kwana.

the next day
9:5am
daddy ne ya tura kofar dakin su salis ahankali ya shiga ganin shi yayi zaune yana karatun alkur,ani zuwa yayi dafdashi ya zauna.

salis ya juyo yakalleshi ya rufe kur,anin sannan yace inkwana daddy?

cikin fara,a daddy yace lfy lau babana, saidai abu daya dake damu danyau nakwana banyi bacciba idai kunne na yajimin gaskiya toh lallai haydar bekwana gida ba dan banji shigowar shi ba .

shiru salis yayi yasa kansa akasa.

daddy yasake cewa babana gayamin komai karka boyemin dama haydar ya saba kwana awajje ne?

kai ya daga alamar eh.

shiru daddy yayi nadan wani lokaci zuwacen ya dago yace mamanku ta sani ?

nanma daga kkai yayi

daddy yace toh yayi kyau, kunyi waya dashi ne.

kasan akasa yace a,a

toh kanemeshi awaya idan kasame shi kacemai nace idan ya wuce 2 hours be dawo gida ba ya neme wani uban.

cikin sauri ya juya ya fita adakin.

mikewa salis yayi ya dauki wayar shi ya fara neman layin haydar zuwace aka dauki wayar saidai abinda ya bashi mamaki muryar mace yaji cikin lankwasa harshe tace waye

shiru yayi nadan wani lokaci sannan yace iname wayar yake.

itama kamar bazatai mgn ba tace yana bacci,

cikin takaice ya kashi wayar yamike ya fara shiri zuwa Office.

yana kokarin fita agidan yaci karo da alhaji yana shigowa yace kasameshi kuwa?

cikin sauri yace a,a daddy bansame shi ba amman zuwa anjima zankara gwaawa.

4:02pm salis ya dawo gida yana ardu,a azuciyar shi Allah yasa haydar ya dawo.

afalo ya samu taslim da fatima suma kallon wani film a TV, fatima ya gani tasa wasu kaya masu kyau riga da siket na atamfa bakaramin kyau suka mata ba ya dade tsaye yana kare mata kallo suko hankalin su na wajen kallo hannun shi yasa acikin aljihun shi sannan yayi magana ahankali yace sister zahra.

dukkan su suka juyo suka kalleshi murmushi fatima tayi taslim tace yaya yaushe kashigo?

zuwa yayi dafda fatima ya zauna sannan yace zahara kinga yadda kikayi kyau kuwa.

cikin sauri taslim tace nifa yaya?

kema kinyi kyau amman zahara ta fiki kyau, tsaki yaja sannan yace haydar ya dawo kuwa.

nidai bansani ba ammafa kamar be dawowa ba.

mikewa yayi sannan yace kuje Ku shirya na kaiku kuyi gidan alhj

da gudu taslim ta tashi ta shige daki fatima ma mikewa tayi tabi bayan ta sumi sumi dan har yanzon bata gama sabawa da gidan ba.

bayan sungama shiryawa taslim tace nidai fatima ki sameni dakin yaya.

bayan fatima ta saka hijjabinta tace ummi mun tafi murmushi tayi sannan tace adawo lfy fatima.

tana fitowa falo ta hango salis kwance akan kujera idonshi rufe saidai abida ya bata mamaki kananan kayane jikinshi sun matseshi kuma daidai da takalminshi be cireba dashi ya kwanta kara matsowa tayi ta kalli shi sosai wani gashhi ne cike akan sa cibiri cibiri irin na samarin zamani tabe baki tayi sannan tace azuceyar ta toh ina taslim tayi,
gani tayi bata da mafita dole ta tasheshi wata kela ita suke jira gashi yaci uban kwalliya dan hakka ta matsa dafdashi tace yaya katashi muje nagama fah.

ahaukaci ya bude ido yakai mata tokari aciki ,cikin sauri ta duka ta rike cikin

matsowa ya Farayi yana fadin dan kutumar uban ki wacece ke dazaki zo ki tadani ina bacci.

a sittin ta mike rike da ciki tayi dakin

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

12 -14

Ummi na kwace akan gado taga fatima rike da ciki arude ta diro da kafafuwan ta tace

" fatima lfy me ya sameki aciki ?

kasa magana tayi illa kuka da ta keyi.

ummi ce ta kamota ta kwantar da ita jikinta tana rarrashinta ,ta gayamata me yasame ta

daidai lokacin salis da taslim suka shigo dakin, salis yace sister ya haka muna ta jiran ki kuma kinki fitowa,

kallonta yayi sosai yaga ashema kuka take ya sake cewa ummi me ya sameta.

nima abinda nake tambayanta kenan taki magana.

tsugunawa yayi gaban su yace sister gayamin me ya sameki?

cikin mamaki take kallon salis azuciyar ta tace lallai wannan munafiki ne wato har yaje ya cenzo kaya dan tsabar mugun ta ahankali ta dago jajayen idonta ta harare shi sannan tace

bakai bane kasa kafar ka ka naushe ni aciki.

zaro ido yayi sannan yace ni kuma ? gaskiya bani bane ,sister toh me kikamin da zan dake ki?

ummi ta kalli salis tace haydar ya dawo ne?

Ok eh ummi sanda muka fita nida taslim naga shigowan shi.

batace komai ba ta mike ta fita adakin salis ya matsa gabanta ya kamo hannun ta yana wasa da yatsuta yace kiyi hakuri, zahara bani bane kisan mu yan biyu ne kuma muna matukar kama nan gaba kad'an zaki fara banbance mu dan akwai dan banbanci,
kallon idonta yayi sannan yayi murmushi yace ban da abinki ma sister ai shigar mu ba iri daya bace shi bakiga ya tara gashi bane saikace mahaukaci.
Chapter 2 · 0% Book details