← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

" kasa yayi dakai cikin sanyin jiki yace ummi nima ba ason raina nakeyi ba amman ku tayani da addu,a.

aidama cen muna maka addu,a amman tunda kace haka zamu daura akan na da, kuta shi kuje kuci abinci, anas ga abinci cen.

*******

da daddare daddy da ummi suna zaune afalon daddy fatima tayi sallam ta shigo sanye da hijjab gaban kujeran da daddy yake zaune taje ta zauna ummi ta bita da kallo.

bayan ta gaida su daddy ya kare mata kallo sannan yace fatima me ya faru akwai wani matsala ne?

kanta akasa tace daddy Dama inason nakoma gidan yadidko ne.

murmushi daddy yayi sannan yace kina nufin ki koma cen da zama?

da sauri ta daga kai.

gyara fuskar shi yayi sannan yace saboda me?

ummi ce tayi karaf tace alhj ka mata ne makiyin ta ya dawo

da sauri yace kash haba hafsat wai me yasa kk haka wani irin makiyi kuma ita da d'an uwanta ai babu wata kiyayya tsakanin su , fatima haydar d'an uwanki ne baki da wani d'an uwan da ya wuce shi sai kuma taslim dan Allah ku rungumi juna kinga bayawa gareku ba Ku hudu Allah ya bamu kuma ya karbi daya yanzo sauran ku 3 dan haka muke fatan kuhaifa mana yara masu yawa tunda mu Allah be bamu masu yawa ba

batacewa daddy komai ba tamike tana share hawaye duk suka bita da kallo.

tana kaiwa kofar haydar na sayo kai ko kallon gurin dasu ummi suke beyi ba ya d'aga hannu ya sharara mata Marika har guda 3

wani wawan tsale ta daka takoma gefe ta fasa wani uban ihu domin kuwa Marin sun shigeta.

daddy da ummi kuwa mikewa sukayi kowa bakin shi bude suna kallon haydar

sai alokacin haydar ya kalli su daddy nan da nan ya fara sosa keya , meta maka, tambayan da daddy yayi wa haydar kenan

ahankali yace bigeni tayi.

" shine kamata wannan dukan toh Bari kaji daga yau karka kuma kai hannun ka jikinta , in ban da mugunta ma ko kusa dakai bataje ba , mutumin baza kawai.

ummi ce ta kamo fatima tana ,duba gurin da haydar ya dake ta fatima ko sai kuka takeyi.

itama ummi fada ta shigawa haydar yana tsaye kanshi akasa itako fatima tana kwance jikin ummi.

bayan haydar ya fita ummi takai fatima har daki sannan ta fito ta nufi dakin haydar.

tana turo kofar idonta yayi mata mugun gani haydar ne zaune yana kalon film din batsa ga sigari ahannun shi yana zuka

har takai tsakiyan dakin besan ta shigo ba saboda shagala da yayi da kallon salatin da ummi ta rafka ne ya dawo dashi cikin hayyacin shi da sauri ya kashe tv cikin tashin hankali ummi tace haydar daman abinda kk yi kenan?

kasa cewa komai yayi jiyake kamar ya nutse cikin kasa.

ta sake cewa kai dai bazakaji tsoron Allah ba KO?

nan ma bece komai ba dan haka ummi ta juya ta fita ranta bace.

washegari da yamma alhj yusuf da alhj babbba suka iso gidan su haydar, daman tun kafin sukaraso daddy yasanar musu da zuwan mahaifin shi gidan dan haka ummi ta tanazan musu komai dazasu bukata duk da cewa bata da lfy dan tun sandda tashiga dakin haydar tarasa abun da ke mata dadi.

fatima da taslim KO sunajin tsayowar mota suka rutumo aguje ganin haydar agaban su yasa taslim ta tsaya itako fatima gefen shi tabi aguje taje ta d'ane alhj babba taslim da haydar tare suka iso haydar sai hararar fatima yake.

alhj babba ko farin ciki ne ya lulubeshi ganin inda jikokin sa suke murnan ganin shi, gaba daya suka rankaya sukai cikin gidan afalon daddy su ka zauna.

bayan sun natsune alhj babba yace ni banga salamatu ba.

alhj yusuf yace baba bata jin dadi ne shiya sa bata zoba.

shiru yayi sannan yace toh Allah ya bata lfy ,juyawa yayi ya kali muta nen dake dakin yace toh duk kubani hankalin ku, wani abun alheri muke shirin kullawa tsakanin haydar da fatima .

da sauri cikin fatima ya bada kululuuuuluuu yayin da zufa ya fara karyowa haydar.

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊🕊
[7:55PM, 4/3/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

52-55

Alhj babba yace in Allah ya yarda nan da sati 2 za,a daura musu aure.

tuni fatima ta fara kuka, xuwa cen ta koma kusa da daddy ta kama kafar shi tace

" daddy dan Allah karka bari ayi haka wlh daddy bana son shi ,ni da ku had'a ni da yaya haydar gara asamu ko almajiri ne ahada ni dashi daddy haydar fah mazunaci ne kuma.... alhj yusuf ne ya daka mata tsawa , hunnun ta tasa dukka biyun ta toshe bakin ta tana fadin na shiga
uku.

alhj babba yayi tariya irin nasu na manya ,sannan ya kalli haydar yace haydar kai baka ce komai ba.

kan shi akasa yace ai alhj da dai zaku cenza shawara da yafi danni inason in aure wayayyiyar yariya ne kuma ma ni ai jinin mu be hadu da wannan fatimar ba.

daddy ne yace zai hadu nan gaba dan babu wani uzurin ku da zai lalata mana shiri, mun riga mun gama shiryawa.

haydar babu abin da yake sai share zufah itako fatima kuka take harda majina.

ummi ko tana gefe ta hada rai maganar fatima ce take mata yawo wai fatima ce ke cewa haydar mazunaci wato ita ta manta da tabon da yake jikinta dan ma ta samu za,a rufah mata asiri tunanin ummi kenan acikin zuciyar ta.

alhj babba ya dubi ummi yace hafsat naga kamar bakiyi farin ciki da wannan auren da muke son hadawa bane?

nan danan ummi ta saki fuska tace alhj ba haka bane akwai dai abin da nake tunani ne kaga yaran nan bashiri suke ba ina jin tsoro abarsu agida su biyu dan ni dake zaune dasu ni nasan halin su.

alhj na dariya yace ki daina jin tsora hafsat, babu abin da zai faru dalilin dayasa nace ahada su aure kenan, yusuf ya gayamin halin da suke ci ,dan haka naga idan muka barsu ahaka zasu haifar mana da gadaddiyar gaba, kinga auren da zamu hada su zai dakatar da gabar daman bahaushe yace _*tsuntsu me wayo ta wuya ake kamashi*_

cikin kuka fatima tace alhj indai dan muna gabane za ahadani dashi toh wlh daga yau na bari ,bazan kara gaban dashi ba, dan Allah ajanye maganar auren nan .

duk falon dariya sukayi ban da ummi da haydar.

bayan alhj ya gama darawa yace fatima ni zakima wayo toh naki wayon aure nan babu fashi idan kinga ba ayiba toh dayan ku baya nunfashi, ya waiga gurin ummi yace hafsat na amshi uzurin ki dan haka acikin gidan nan zasu zauna kicigaba da lura da irin zaman da sukeyi kafin wani lokaci.

nan danan ummi ta washe baki tanawa alhj godiya.

sanna ya sake cewa ke kuma fatima tashi ki hada kayanki kibi baban ki ya kai ki gurin mahaifyar ki kafin ranar daurin auren

sumi sumi ta mike ta fita shima haydar mikewa yayi ya fita

gaba daya kayanta dake gidan ta hada ta fara fitowa dasu ta sawa amotar alhj yusuf har ta gama kuka takeyi motar ta shiga ta zauna har sun fara kokarin fita daga gidan alhj babba ya kalli Fatima yace

" kinyiwa ummin taku sallama kuwa?

cikin kuka ta girgiza kai.

cikin fada baba yusuf yace aiko ranki zai baci.

da sauri ta fita daga motar har tana tuntube.

kofar ummi ta tura tare da sallama ganin haydar tayi kwace akan ciyar ummi sai buga bayan shi take kamar me lallashin karamin yaro.

duk d'agowa sukayi suka bita da kallo har haydar.

ahankali tace ummi muntafi.

cikin ya tsuna ummi tace hmmm fatima kenan wai har ke ce kike cewa haydar mazinaci ke kin manta tabon dake jikin ki, ai haydar rufah miki asiri zaiyi kuma kome d'a namiji yayi ado ne .

har ummi ta gama maganar ta haydar be d'ago ya kalli fatima ba.

itako fatima kara rushewa tayi da kuka tana me bakin cikin abun da ya same ta gashi har an fara goran ta mata lallai kowaye yaketa mata mutuncin ta ya cuceta take ta tuna sunan da taji abokin sa na kiran sa da shi wato big boy tana tafiya tana fadin big boy ka cuceni in Allah ya yarda sai Allah ya karbamin hakki na dahaka ta isa motar ko ahanya kuka take sosai dan haka alhj babba yita mata nasiha.

bayan sun sauke alhj suka nufa gida

har suka shiga gida alhj yusuf ko kallon inda fatima take beyi ba, afalo suka samu mama tana kwance akan kujera, tana ganin su ta mike tace alhj lfy na ganka da fatima?

zama yayi yacire hula sannan ya kwashe komai ya fad'a Mata, sannan ya kara da cewa kiyi mata fad'a sosai dan na kula so suke su kawo mana rabuwan kai , ya kalli fatima yace

" fatima kece karama Ina rokon ki da ki kwantar da kai kinga haydar ya fiki wayo tunda yayi mgn su daya yaga ba,a goyi bayan shi ba ,be sake cewa komai ba, dan haka kema kiyi hakuri da hukuncin da aka yake akanku , bana son naji kin sake cewa baki son haydar.

cikin kuka tace toh.

daga nan be sake cewa komai ba ya tashi ya shiga d'aki.

mama tasowa tayi ta dawo kusa da fatima ta dafata sanan tace

" fatima wai me ya had'aki da haydar ne wannan abin naki yayi yawa fah.

cikin shashekar kuka tace mama wlh bansan dalili ba nima haka na tsinci kaina.

shawarwari mama taita bawa fatima har ta dan saki jiki.

ranar da fatima tayi sati 1 dawowa gidan tana kwace afalo hannuwan ta duk suna kan fuskar ta hawaye ne ke tsiyayo mata, tana cikin haka taji sallaman haydar , kara damke idonta tayi kamar me bacci tana jin su suka shigo har takiyan falon shida anas.

zama sukayi anas na fadin maryan tamu ma bacci take, haydar yaja tsaki yace

" bawani bacci zama tashi ne"
Chapter 15 · 0% Book details