← Book details Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Tsuntsu Me Wayo Complete Hausa Novel · about 8 min read

taslim ce ta saki dariya tace wlh brother ni yanzon ma tsoro yake bani haka ranar nan daga naje wucewa ta kusa dashi lokacin yana waya saiji nayi ya jifeni da cup wai nazo naji abinda yake cewa ne naje na gayawa ummi.

salis yace ai yana da matsala haka dai zakuita hakuri dashi.

ji sukayi anturo kofar ummi na gaba haydar na bin ta abaya zuwa yayi ya tsuguna agaban fatima kamar yadda yaga salis yayi kamar me ciwon baki yayi mgn ahankali sister kiyi hakuri na manta acemin kina gidan nan na dauka wata ce daban.

shiru tayi ko kallon shi batayi ba sai dai ko ahaka ta gane banbancin murya atsakkanin su domin kuwa muryar salis tafi na haydar sanyi.

jinda yayi tayi shiru yasa ya waiga ya kalli salis yace brother katayani bata hakuri

salis yace bakumai haydar ya wuce sai dai akiyaye gaba.

sai alokacin haydar ya kalli fatima daniyar yayi mata godiya amman yana kallon fuskarta ya kasa cewa komai sakamokon muguwar kama da tayi masa da wata yariya da yake marmarin sake kasan cewa da ita

mikewa yayi cikin sauri ya nufi kofa dukkansu binshi sukayi da kallo ummi ce tace ikon allah, Allah ka shirya wannan bawa naka

salia ko mikewa yayi daga gaban fatima yana fadin toh yanzo dai shikenan haydar ya hanamu fita.

Haydar na fita ya nufi dakin mahaifin shi kamar yadda ummi ta umarceshi ahankali ya tura kofar ya shiga neman guri yayi ya zauna sannan ya daga kai ya dubi mahaifin shi dake zaune yana karatun jarida, ahankali yace

" daddy ina yuni?

baza yayi dashi kamar ma besan da shigowar shiba zuwa cen yace a inakakwana?

kanshi akasa yace daddy mun je zaria ne muna kan hanyar mu ta dawowa motar ta lalace amman dan Allah kayi hakuri bazan....

tsawa ya daka mishi wanda yasa dole yayi shiru sannan yace Karka maidani mutumin banza haydar guda nawa kake, nine ubanka babu wani dubara da zakamin, batun yauba na kula kai mutumin banza ne, toh bari kaji daga yau kar magriba ta sake maka awaje kuma daga office ban amince ka wuce ko Ina ba kanajina ?

eh kawai ya iya furtawa domin hukuncin yayi masa tsauri.

da daddare salis ne zaune adakin su yana karatun Qur,ani yayin da haydar ke kwance akan gado sai juyi ya keyi.

zuwacen salis ya rufe Qur,anin ya iso bakin gadon ya zauna sannan yace

" brother meke damun ka ne naga sai juyi kake?

tashi yayi ya zauna sannan yace kasan matsalata brother bana iya bacci ni d'aya.

murmushin takaice salis yayi sannan yace haydar al,amarin ka yana bani mamaki kai wai bakajin tsoron Allah ne, ga hanya mafi sauki kabi kaki sai anyi amma mgn kacei Allah ne ya daura maka toh naji Allah ne ya daura maka kayi aure mana, ko mata hudu ne kana iya hadawa.

hannu haydar ya dagawa salis haba wai kai sai ka rinka cewa nayi aure duka duka guda nawa nake ko 30 years ban hadaba fah.

kulewa salis yayi cikin fada yace kananufin sai mutun yakai 30 sannan zaiyi aure wani malamin ne ya fada maka?

nidai kawai ka rufamin asiri na dan fita da suba zandawo.

cikin fada salis yace wlh bazan rufama ba kana fita zan fadawa daddy

tsaki haydar yaja ya tura kanshi cikin bargo yana fadin muna fuki kawai

naji ni munafuki ne kaikuma dan iska me lalata yaran muta ne.

hankade bargon yaye ya duro ya cefkke wuyar rigar salis nan danan dabe ya kyaure atsakanin su.

ummi da yan matanta suna falo suna kallon wani film suka farajiyu hayaniyar su aguje suka nufi dakin.

salis naganin su ya tsaya cek amman haydar be daina kaimai doka ba.

ummi ce ta fara kokarin jan haydar tana cewa haydar duk yadda akayi kana shan kayan maye ka rasa dawa zakayi fada saida dan uwanka innalillahi wa ina ilaihir raju, un.

salis ne yazo ya rike ummi yana fadin ummi jeki abinki ya wuce taslim zahra kuje ku kwanta.

ummi kuka takeyi dan haka su fatima suka fara kuka.

shiko haydar sai maida numfashi yake yana hararar salis ya koma bakin gado ya zauna.

salis ko ganin ummi tana kuka hankalin shi ya tashi, yayi daya sanin biyewa haydar yace ummi dan Allah kije ki kwanta babu abinda zai sake faruwa.
suna fita haydar ya mike ya koma kujera ya zauna hannu yasa a aljihunshi ya dauko sigari ya kunna ya fara zuka yana fesar da da hayakin

🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊

Comment 07014197556
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _©Exquisite Online Writers_

🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊

_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*

15 - 16

Salis tsaya wa yayi yabishi da kallo cikin mamaki yasan haydar yana shen sigari tunda yasha gani amotar shi amman betaba sha agaban shiba sai yau ,

filo ya dauka ya nufi falo dan baxai iya shakan wannnan warin ba.

washegari

salis yakai fatima makaranta secondary akasata jss 1
itako taslim tuni ta kare secondary ayanzo haka tana cigaba da karatu, dan haka kullum salis kekai fatima makaran ta drive kuma ya dakota saboda lokacin salis yana gurin aiki.

shakuwa ce tashiga tsakanin salis da fatima me karfi dan ayanzon har fatima ta saki jikin ta dashi sosai.

shiko haydar tun ranar da su kai hayaniya da salis kwata kwata baya mai maga gashi har an hada one week amman daddy yake cire takunkumin shi saima kara samai ido da yake haka kullum zaita juyin shi akan gado sai dai salis yayi tsaki ya juyamai baya dan haka abin ya fara damun shi.

yauma kamar kullum haydar ne kwance agado rike da ciki yana murkusu ya hada uban zufa.

salis ne ya taro kofar ya shigo kallon haydar yayi cikin sauri ya karasa bakin gadon yace make damunka.

daker ya iya bude baki yace cikina ne.

mikewa yayi ya nufi kofa ahankali haydar ya kirashi bayan ya dawo yace Ina zaka.

zan fadawa daddy ne.

zaro ido haydar yayi yace dan Allah karka gayamai nasha magani zuwa anjima zai sauka.

shiru salis yayi ya zauna abakin gadon ganin inda haydar yake hada zufa ya sake mikewa ya kunna mai A.C amman duk da haka zufa yake zuwa cen hawaye ya fara zubowa a idon shi hannun shi kuwa yana kasan cikin shi yana dan matsawa
zuwa cen bacci ya kwashe shi.

ajiyan zuciya salis yayi sannan ya gyara kwanciyar shi .

washegari

sunfito cikin shirin su na tafiya Office salis ya kalli haydar yace au me ciwon ciki ya cikin naka?

tsaki haydar yayi sannan yace sai yanzon zaka tambaye ni.

fashewa yayi da dariya sannan yace

" wlh brother mamaki kake mani jibeka one week kawai dobi inda kayi zuro zuro, kasan Allah kamata yayi ahada maka mata hadu dan daya ta maka kadan.

tsaki haydar yayi ya shege motar shi yabar wajen.

yana isa Office yayi amfani da wayar shi ya kira babban aminin shi anas,

ba ajima ba anas ya shigo, wata budurwa nabinshi abaya.

haydar naganin su ya miki yariyar ya rungumo yana kissing dinta itama yariyar yar duniya ce dan tuni ta fara aika mai da makata nan suka lalace.

jin nurfarfashin da haydar keyi yasa anas barin office din dan yasan idan ya zauna zasu tasomai da tsumin sa.

saida ya kwashi awa 3 yana zaune abakin office din sannan yamike ya tura kofar ya shiga ganin yariyar yayi kwance tana barci akan kujeran dake cikin office din tayi matashi da cinyar haidar shima bacci yakeyi hannun shi acikin rigarta..

hannun shi ya hada yayi tafi nan danan suka mike anas yace toh waikai yau baka da aiki ne, tsaki yaja sannan yace bar aikin nan gobe nayi, juyawa yayi ya kalli yariya yace

babyna naga alamar kin
gaji da yawa yau nabaki wahala am sorry nayi missing dinki ne dawa.

cikin shagwa tace zani gida nayi wanka na kwanta.

OK baby badamuwa anas zai maidake gida amdai gobe zaki dawo KO, saboda kar mukuma samun irin matsalar yau.

cikin shagwaba ta mike tana buga kafa kamar zatai kuka take mgn ciki ciki

haydar kara rudewa yayi dan yana balakin son yaga mace na irin wannan shagwabar bare wannan yariyar da komai dake jikinta rawa yake besan lokacin daya isa gareta ba ya zura bakinshi cikin nata saida yayi son ransa sannan yabarta.

karfe 4:00 hayadar ya baro office cike da farin da walwala domin yau ya samu abinda zuciyar shi take muradi yana shiga gida ya samu salis da fatima suta hira suna dariya.

bebi ta kansuba ya shige daki bayan yayi wanka ya biya basussukan sallah da ake binshi ya fito falo .

suna nan yadda ya barsu saidai ayanzon harda taslim, zama yayi agefe ya kure fatima da ido shi dai yana ganin kamar yasan yariyar nan, idan ma ba itabace toh sunada dankantaka tv ya kurawa ido amman lokaci zuwa lokaci yana satar kallon fatima.

zuwacen taslim tace fatima kitashi muje gidan yadidko.

salis yayi karaf yace ke bazata ba ni banason yawace yawace.

cikin sanyin murya taslin tace haba yaya gidan yadidkon ne yawace yawace kuma fa bajimawa zamuyi ba.

kalon fatima salis yayi cikin ido yace zahra kinason zuwane?

cikin sauri fatima ta dukar dakai dumin duk lokacin data kalli cikin idon salis saitaji gabanta ya fadi.

riko hannunta yayi tabi hannun shi da kallo yana wasa da yatsun yake fadin idan kinason zuwa ki tashi kuje amman karki irin shigar taslim, kisa hijjab ne kuma karku dade.

da mamaki taslim take kallon salis shima haydar shi yake kallo .

suna fita haydar yadawo dafda salis ya zauna yace

" brother kardai son yariyar nan kake?

a,a haba meka gani, kodan nace tasa hijjab dama shiyasa naga kana kallo na.

hannu haydar ya daga mai kaga malam bawani kwana kwana da zakamin ka fito fili kace sonta kake.

dariya sosai salis yayi sannan yace ni dai bance maka inasonta ba nidai kawai nasan yariyar tana birgeni kuma idan muna tare ina samun kaina cikin nishadi har inji manason mu rabu.

shine zakace bason ta kake ba wlh sonta kakeyi kuma wlh bazaka aureta ba.

murmushi yayi sannan yace tunda kaine ubana ba
Chapter 3 · 0% Book details