← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin zuciyarsa, a yanzu irin ya girma ya fito fili. Abin da ya fi damun Anas shi ne bai san yadda za a yi ya girbi bishiyar kaunar dake cikin zuciyarsa ba. Mabaruka! Ya kira sunanta a sanyaye, ita ce kadai babbar katangar dake tsakaninsa da Ummi haka nan... "Anas." Zazzakar muryar ta katse tunaninsa. Ya juyo firgigit, ya ce bakinsa na rawa. "Ummi." Ummi ta dubeshi da murmushi ta ce. "Ashe nan ka dawo Mabaruka na can tana jiranka." Anas ya dubeta ya sunkuyar da kai ya ce a sanyaye. "Har kun gama tattaunawar?" Ummi ta gyada kai da murmushi sannan sai ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yan yatsunta Tsawon lokaci matasan biyu suna nan tsaye suna duban juna Wutar bege ta dada ruruwa cikin zuciyar Anas musamman sa'ar da iska ta buga kamshin turaren dake jikinta zuwa hancinsa. "Ummi." Anas ya kirawo sunanta a sanyaye. Ummi ta matsa kusa dashi sannan ta dago kai ta dubeshi ido da ido ta ce "Anas." Anas ya yi sororo jiki na rawa ya kasa cewa da ita komai akwai wani irin kwarjini a jikinta da ya karya zuciyar Anas duk kuwa da kwarewarsa a harkar mata. To amma duk da haka sai ya sake ta yan maza ya ce. "Ummi..wani abu ne ke damuna wallahi na rasa yadda.." Ummi ta katseshi ta hanyar dora hannu a bakinta ta ce "Ba sai ka fada ba, na san abin dake damunka sai dai nan ba wurin da ya dace a yi irin wannan magana ba ce." Ta yi shiru sannan sai ta mika masa wata yar takarda ta ce. Gashi nan sai mun hadu, ka yi sauri ka koma tana can tana jiranka ka santa da zargi." Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta bar shi anan tsaye. Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran.TSOHON ALKAWARI-8 . Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran farin ciki a duniya da ya wuce Ummi, to sai dai kuma wani bangare na hadamammiyar zuciyarsa na cewa "Uhum-uhm Anas ka bi a hankali yanzu fa zabinka biyu ne ya rage a rayuwarka ta duniya, ko dai ka zabi kudi da tashin hankali ka bar Ummi, ko kuma ka zabi Ummi ka bar kudi. *** Karfe goma sha daya saura minti uku na dare, Mabaruka da Anas suka shiga dakin kwanansu. Tun daga sa'ar da ya koma wurin. Mabaruka a farfajiyar lambun ya lura da cewa lallai yau akwai masifa domin ta cika ta yi fal har wani kumbura take yi. "Ina ka tafi ka zauna ina ta nemanka?" Mabaruka ta tambayeshi a fusace sa'ar da Anas ya dawo ya zauna a kusanta. Bi a hankali dan samari wata zuciya ta ce dashi. "Ina can baya a zaune muna gaisawa da bakin ki." Mabaruka ta dubeshi a yatsine cikin tsananin zargi sannan ta dauke kai gefe guna. Har bayan da suka gama sallamar baki suka shiga dakin kwanan nasu Mabaruka bata kara cewa dashi uffan ba. Anas ya lura saboda tsabar fushi bakinta har wata kumfa-kumfa yake fitarwa, haka nan duk illahirin jikinta rawa yake yi kamar kamun zazzabi. Anas ya tura Mabaruka akan kujerarta daf da jikin gadon kamar yadda suka saba, sannan ya yi yunkurin daukanta ya daura akan gado. Ga mamakinsa sai ya ji ta buge hannunsa a fusace. "Ka da ka taba ni!...Na ce da kai kada kabani munafuki...!" Anas ya ja baya cikin kaduwa a tsorace. "Me na yi miki?" Mabaruka ta kifa fuskarta akan cinyarta, sannan sai ta fashe da kuka mai karfi jikinta sai rawa yake yi kamar zata fado daga kan kujerar. Tsohon lokaci sai ta dago kai ta ce. "Me ye...hadinka da Ummi?!" Anas ya yi kokari ya sa alamun rudewa akan fuskarsa ya ce. "Ummi kuma...ba kawarki ba ce ni ban ma taba ganinta ba sai sau biyu kuma duk a dalilin ki." Mabaruka ta ci gaba da shisshikar kuka sannan ta nuna shi da dan yatsa ta ce. "Anas, ina son ka sani cewa na aureka ne don ni kadai ba don ka samar min kishiya ba. Na yi maka abin da duk duniya babu wanda ya isa ya yi ma haka ba don komai ba sai don cikar farin cikina." Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "Tun farko sai da na ce sayenka zan yi Anas ban fada maka ba? Idan kuwa haka ne to kai nawa ne ba na kowa ba, don haka daga yau sai yau zan gargade ka, babu kai babu Ummi, koda ta zo gidan nan bana son ka kara ko da kallonta ko gaisawa ban yarda ku yi ba, kai ba ma Ummi ba duk wata mace a duniya in ta wuce kanwarka ta jini ko mahaifiyarka ban yarda ku gaisa da ita ba, kuma daga yau ka daina zuwa wurin aiki, zan ci gaba da biyanka albashinka na fi son daga yanzu kullum kana tare dani kana faranta min, duk inda zaka daga yanzu tare zamu ke tafiya, dare da rana safe da yamma, ruwa da iska kai ko bala'ine bai isa ya rabamu ba, domin muna tare zan manne ma kamar cingam domin sayenka na yi." Mabaruka ta yi ajiyar zuciya sannan ta daga dan yatsa ta nuna shi ta ce. "Idan kuma kana ganin da takura, to ina shawartarka da ka rubuta min takardar sakina yanzun nan, sai ka hada naka ya naka ka bar min gidana, amma ka tuna daga lokacin ka daina karbar albashin naira dubu dari biyu ka daina karbar kudin da mahaifiyata ta ke baka duk wata ka kuma daina hawa motocina kai hatta kayan da ka saya da kudin mahaifiyata sai ka ajiye min kayana kuma sai ka yi sallama da fita wata kasa a duniya domin na san a rashin zuciya da lalaci irin naka da wahala in zaka yi arziki a duniya mutumin da ko sallah baya iya yi!" Anas ya yi tsaye sororo cikin tsananin kaduwar da bai taba irinsa a duniya ba. Wani abu mai kamar gare-gare ya fara yawo a cikin kwakwalwarsa, nan da nan ya ji cikinsa ya murda kamar zai yi amai Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki na rawa ya ce "Ki yi hakuri Mabaruka abin duk bai kai da zafin haka ba." Anas ya dada dafe ciki sannan ya dubi Mabaruka. Mabaruka ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji ba zai iya daurewa kukanta ba dan haka sai ya ruga bandaki a guje yana zuwa sai ya fara keta amai. Bayan tsawon lokaci ya gama zubar da abincin da ya ci a wurin liyafar. Daga bandakin yana iya jiyo shisshikar kukan Mabaruka hakan shi ya tuna masa da guntuwar takardar da Ummi ta bashi cikin sauri ya laluba aljihunsa ya dauko takardar sannan sai ya warwareta ya fara karantawa...... . Anas Tun da nake a duniya ban taba sanin mene ne so ba domin ni ko zance ma bana fita wurin samari To amma tun ranar da na dora idanuna a kanka sai na ji duk duniya bani da abin so kamar ka. Na yi matukar farin ciki sa'ar da na dubi cikin kwayar idanunka, sai na tabbata kai ma kana kaunata. Haka nan na yi bakin ciki da ya kasance wannan gurguwa ta yi min shigar sauri ta aureka. Wannan shi ya sa na yi amfani da damar wannan liyafa domin na isar da sakon zuciyata zuwa gareka Na gode, zan tsaya anan, idan har abin da nake zargi gaskiya ne, na san zaka so mu hadu. Ga adireshina nan a kasa, zan jiraka gobe gida tun daga karfe bakwai na dare har zuwa goma na dare...sai na ganka mai... Ummai. Anas ya kankame takardar a kirjinsa cikin farin ciki sannan kuma cikin tsananin rudewa. "Daga yanzu duk inda za ka muna tare zan manne maka kamar cingam!" Ya tuna da kalaman Mabaruka. "Ina jiranka gobe a gida..." ya kuma tuna da kalaman Ummi na karshe. Anas ya lumshe idanunsa, sannan ya kara takardar wasikar akan hancinsa, ya shaki kamshin turaren jikin Ummi dake jikin wasikar, cikin jin dadi. Daga can falo ya jiyo gurnanin kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri ya toshe kunnensa domin baya son kukan ya bata masa farin cikin da yake, kai da zai yiwu ya gwammace ya kwana cikin bandakin rungume da wasikar Ummi! Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci guda. Na dubeshi cikin kaduwa na ce bakina na rawa. "To mana Baba Sidi...ci gaba mana ya ka tsaya bayan labarin ya gama daukar dadi." Sidi mai Jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici, sannan ya dubeni da kyau ya ce. "Kada ka bari dadin labari ya dauke ka, saurara da kyau ka ji kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka yi sallah idan an idar da sallar sai mu sako wani sabon zaren labarin." Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauki tsohuwar butarsa ta karfe mai kwarin tsiya ina tsammanin butar tafi shekaru arba'in. Na mike tsaye cikin sauri na ce. "Baba Sidi dan Allah...da na gama sallah fa zan dawo." Baba Sidi ya dubeni da murmushi ya ce. "Idan za ka dawo ka tabbata ka dawo min da karin tubani, domin idan babu shi, to babu labari Nas, na riga na fada ma ni da tubani tamkar tsohuwar mota ce da man fetur. Ya juya cikin sauri da butarsa a hannu ya nufi waje zai yi alwala. *** Ban sami damar dawowa wajen Sidi mai jaka ba sai bayan sallar La'asar sakamakon tsayawa da na yi a sake dafa min sabon tubani. "Kai dan nema, bana son shakiyancin banza, me kuma zaka sake yi da tubani. Na dauka dazu-dazun nan na yi ma cikin kwano guda?" Kakata ce ke fadin haka. Na dubeta da dariya. "Kin ga in za ki dafa min ki dafa, in kuma ba haka ba yanzun nan in baki takardar saki akan tubani." Ta fashe da dariya. "Amma kuwa da ka yi abin kunya wallahi ka saki matarka saboda tubani?" Daga karshe
Chapter 9 · 0% Book details