Sashe 4
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
basu sami damar shigowa da motocinsu ba saboda cunkuso.Anas da sauran ma'aikatan dake bangaren girke- girke suka yi ta rabon kayan lashe-lashe da makulashe. Dakin da ake liyafar tangamemen gaske ne, wanda aka gina shi da zummar ya dauki mutum dari uku ba tare da wani ya shaki numafshin dan uwansa ba, Anas ya fara waige-waige yana kokarin ya karewa Mabaruka kallo.Ya ce gaba da zagaya wa lokaci guda kuma cikin jama,a yana yin abin da ya kamata sai dai kuma akwai wani abu da ke damun Anas sa'ar da ya kawo kusa da inda su Mabaruka suke zaune da manyan kawayenta. Jikinsa na bashi cewa kamar kallonsa ake yi a baya. Wannan ita ta sa Anas juyawa a wayance ya dubi bayansa. Gabansa ya fadi ras! Sa'ar da suka hada idanu da Mabaruka, ko shakka ba ya yi shi take kallo, haka nan har da murmushi a fatar bakinta. Anas ya ji bugun zuciyarsa ya karu lokacin da yaga kamar mabaruka ta daga hannu ta yafato shi. Anas ya shiga cikin rudani domin yana fargabar kada ya je wurin kuma ya kasance ba shi take kira ba.Anas ya waiga bayansa domin ya ga koda wani take sannan ya sake juyowa, sai ya ga ta sake yafuto shi da hannunta. Cikin rawar jiki ya nufi inda take zaune tare da sauran kyawawan matannan. Anas ya ji duk gwiwarsa ta yi rauni kamar ba za ta iya daukarsa ba domin kyawun matan da suka kura masa idanu ya yi yawa, ko kusa ko alama basu yi kama da irin yan matan da yake mu'amala da su a baya ba.Anas ya ratsa a hankali ta tsakanin kyawawan tebura ya karasa gaban Mabaruka. Yana zuwa saiya rankwafa a gabanta ya ce."Gani ranki ya dade ko bani ki ke kira ba?" Mabaruka ta dubeshi da mummunar fuskarta ta saki wani abu da take tsammanin wai tattausan murmushi ne."Kai nake kira mana" Ta dan yi shiru, sannan ta ci gaba."Daman so nake na fada ma don Allah ku yi sauri ku gama shirye-shiryen mana, ka ga kamata ya yi ace tun da wurwuri kun gama komai kafin mu zo" Anas bai iya dago kai ya kallisauran yan matan da ke bayanta ba, to amma yatabbata duk kallonsa suke."To ranki ya dade" Anas ya amsa. Ya yi kamar yamike tsaye ya koma kan aikinsa to amma sai ya ga alamun bata gama bayaninta ba. Mabaruka tadubeshi ido da ido, kana sai ta yi kasa-kasa da muryarta ta ce dashi."Ka bar aikin haka nan ka tafi ka gyara jikinka sosai, ka jirani a waje idan an tashi ina son ganinka. "Kasa-kasa da murya, Ehemm.. Anas ya dubeta cikin mamaki, lokaci guda kuma ya godewa hayaniyar al'ummar dake wurin liyafar domin ya tabbata hatta kyawawan matan dake jere a bayanta ma ba su ji abin da ta ce dashi ba ballantana sauran jama'a. Shi kansa yasan ba dan yana kallon motsin fatar bakinta ba da ba zai taba fahimtar abin da ta ce ba. To amma duk da haka yana shakkar abin da ta ce dashi. Dan haka sai ya ya dubeta a rude ya ce. "Ban fahimce ki ba ranki ya dade?" Mabaruka ta yi masa murmushi ta maimaita. "Ka je ka sake kayan dake jikinka ka kuma jirani a waje, idan an tashi zan turo a yi min kiranka ina son magana da kai." Kusan awa daya da rabi ya shafe zaune karkashin wata dukurkusar bishiya mai kama da ta dabino dake farfajiyar otal din yana jiran tsammani zuciyarsa cike da tambayoyi sama da guda dari. Amma manya-manyan tambayoyin da suka fi damun zuciyarsa sune; shin mene ne dalilin ganawa dashi? Shin laifi ya yi mata? To ai kuwa har murmushi take yi masa sa'ar da take bayanin. To mene ne dalilin da zai sa ta ce ya sake kayan dake jikinsa? Babu mamaki ji ta yi kamar jikina yana wari. Anas ya ce da kansa. Duk da yake dai sa'ar da ya baro wurin liyafar sai da ya yi ta shinshina jikinsa domin ya ji ko wari yake yi, to amma har zuwa wannan lokacin da yake sake kayan dake jikin nasa Anas bai gamsu ba, lokaci- lokaci sai ya sunsuna hannun rigarsa kana ya duba agogon. Sa'a daya da rabi kenan yana zaune a gurin yana jira. Tab! Anas ya yamutse fuska cikin damuwa. A karo na farko a rayuwarsa ta harkar mata sai ya ji ya fadi babu nauyi domin a tarihinsa wata mace bata taba sashi ya yi jiranta daidai da na mintuna biyar ba, sai dai ita ta jirashi. Amma sai gashi yau tarihin ya sauya, wai Anas da kansa ne yake zaman jiran wata nannadaddiyar gurguwa mummuna mai dogon hanci da fadi kamar nakiya, lallai duniya juyi-juyi! Wannan tunani shi ya sa Anas ya saki wani tattausan murmushi a cikin duhun daren da ya fara shigowa sannan ya dada jingina bayansa a jikin bishiyar da yake zaune, ya share gumi daga goshinsa a zuciyarsa ya ce. "Kada ka damu Anas, a da can kyawawan mata sun yi jiranka, a yanzu kuwa kai ne kake jiran mummuna da kudi, ko ba komai dai ba talaka kake jira ba. Abin ya kan baiwa Anas mamaki, wata sa'ar ma har dariya idan ya tuna da cewa wai daya daga cikin matan da ta fi kowace kudi a Afirka yake jira! Anas na nan a zaune yana ta sake-sake bai ji zuwanta ba sai muryarta ya ji a bayansa ta ce. "Ka zo wai tana kira". Anas ya juya firgigit domin ganin mai zazzakar muryar. Daya daga cikin kyawawan matan nan ce ke tsaye a kansa. Da yake ita kadai ce a wurin sai Anas ya sami damar kare mata Kallo sosai. Budurwar dake tsaye a kansa doguwa ce fara, kyakkyawar gaske mai hasken fata. Budurwar za ta yi kimanin shekaru goma sha takwas, ko sha tara me yiyuwa ma ashirin, abu ne mai wuya ka iya fadin shekarunta kai tsaye, domin kyawun fuskarta ma'abociyar annuri da kwarjini sun isa su sa duk wani mai iya hasashen shekaru cikin rudani. Budurwar tana da manyan idanu farare tas! Wadanda duhun dare bai hana Anas ganin fararen idanun ba, wani abu da ya so tsayarwa Anas numfashi shi ne kundukukinta mai annuri gami da shafaffiyar mararta wacce ta bayyana a fili sakamakon tsukakken dinkin bakar shaddar dake jikinta. Kafarta fara sol gwanin sha'awa cikin bakin takalmi. Anas a zuciyarsa ya ce da za a barshi ko da daidai da na dakika guda ne ya sumbaci kafarta da babu abin da zai hana shi ya bada albashinsa na wata guda. . "Tana ina?" Anas ya tambaya cikin karfin hali zuciyarsa na harbawa, lokaci guda kuma ya mike tsaye. "Zo mu je na kai ka inda take." Budurwar ta ce dashi. Babu alamun bakin ko farin ciki a fuskarta. Budurwar ta juya tana rausaya. Anas ya bi ta a baya kamar tunkiya. Sannu a hankali suna tafe har ta kawo shi filin da ake fakin da motoci na ota din. Anas ya godewa Allah, domin har suka isa wurin bai hadu da ko ma'aikacin otal din kwaya daya ba, domin sun dade da yi masa muguwar lambar yawan mu'amala da mata. To amma duk da haka sai da Anas ya raya a zuciyarsa cewa inama su hadu da Sabi'u, domin abin alfahari ne ya ganshi da wannan zukekiyar. Sa'ar da suka kawo farfajiyar sai Anas ya lura duk kusan tarin motocin nan sun baje, sauran da suka rage basu fi guda ashirin ba kawai. Anas na bin dudurwar a baya har ta zo dashi jikin wata mota katuwar (Jeep) Shudiya. Tun kafin su karasa kofar motar ta bude sannan sai muryar Mabaruka ta ratsa kunnensa. "Sannu da zuwa lallai ka cika alkawarinan mabaruka ce zaune a bayan motar ita kadai, sannan a gidan gaba akwai direba wani dogo ne, fari bafulatani. Mabaruka ta dubi kyakkyawar budurwar ta ce. "Na gode Ummi, sai goben kenan idan kin zo. Budurwar ta yi murmushi a karo na farko ta dubi Mabaruka ta ce. "To Mabaruka, Allah maimaita mana, sai da safen, bari in yi sauri ga su fati can a mota suna jirana." Sannan ga mamakin Anas sai ta juya gare shi ta haske shi da murmushi ta ce. "Malam sai da safe." Ta juya cikin sauri ta bar wurin. Anas ya bi ta da kallo, a zuciyarsa yana cewa kai lallai kudi ma dai wallahi banzaye ne domin basu san inda ya kamata su je ba. Koda ya kwatanta kyawun Mabaruka Miloniya da budurwar, sai ya ga tamkar ka kwatanta alli da bakin gawayi ne. "Ga shi har dare ya fara yi." Muryar Mabaruka ta katsewa Anas tunaninsa. Anas ya juya firgigit sannan ya saki wani fatalwar murmushi ya ce. "Ranki ya dade gani." Mubaruka ta kura masa idanu na tsawon lokaci, akwai murmushi a fuskarta. "Da za ka kirani da sunana Mabaruka ina gani zai fi" Anas ya dan rankwafa cikin girmamawa to amma ba ita yake girmamawa ba, miliyoyin kudin da ya ji labarin ta mallaka yake girmamawa. "To ranki...Mabaruk a." Mabaruka ta fashe da yar dariya. "Ka kuwa iya fadar sunan" Anas ya ji wani daddadan kamshi sai hurowa yake daga cikin motar. A iya tsawon lokacin da ya yi yana aiki a otal din ya sha jin kamshi iri-iri daga jikin yan birni da masu hannu da shuni da yan kwalisa masu kunan bakin wake da yan kuru, amma a duk cikin su bai taba jin kamshin da ya kai koda rabin wanda ke hurowa daga motar Mabaruka ba. "Idan ba za ka damu ba, ba zan kuma takura maka ba, zan so ka shigo motar nan mu tafi tare da kai." Mabaruka ta ce da Anas tana duban fuskarsa. Anas ya dubeta cikin tsananin kaduwa ya ce baki na rawa. "Mu tafi...ina?" Mabaruka ta dubeshi da murmushi. "Gidana nake son mu tafi tare da kai domin akwai maganganun da nake son mu tattauna da kai masu muhimmanci" Anas ya dubi nannadadun kafafunta kana ya dago kai ya ce. "Har yanzu ban fahimce ki ba" Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce. "Duk abin da zan fada ma anan ba zai gamsar da kai ba, shi yasa nake so na tafi gidana da kai inda zamu