Sashe 17
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a wannan lokacin baya iya ganin komai sai Ummi. "Ummi ni zan tafi...sai yaushe kenan?" Ummi ta dubi fuskar Anas sai ta ga duk ta jike da gumi nan da nan ta fahimci halin da ya ke ciki. "Oh...na san fa ashe tana can tana jiranka ko?" Anas ya sunkuyar da kai "Ummi tun da na yi aure ban taba samun farin ciki kamar na yau ba...dan haka ina rokonki da ki yi shiru da bakin ki kada ki bata min farin cikina na wannan rana ta farin ciki." Yana gama fadin haka sai ya shiga motar ya rufe kofa sannan ya sako kansa ta tagar motar ya ce. "Ummi tun da nake ban taba kaunar wata mace a duniya da gaske har zuciyata ba sai a kanki." Ummi ta dan rankwafa kadan ta ce "Na yarda da kai Anas...sai yashe za ta sake bamu ranar haduwa?" "Wa ki ke nufi? ban fahimce ki ba." "Matarka mana Mabaruka na yi mamakin ma yadda aka yi ta barka kazo." Anas yaji kamar ta watsa masa wuta a fuska. "Ba ta isa ta juya ni ba Ummi duk lokacin da naga dama zan iya zuwa gurin ki." ya dan yi shiru sannan sai ya ce "Ki jira ni zan zo jibi" A haka ya tuka motar ya fice daga layin Ummi ta bi motar da kallo ga mamakinta sai ta ji gaba daya ma ta shiga cikin rudani domin a da kafin ya zo ta dauka idan ya zo ba za ta iya rabuwa dashi ba sai da kuka saboda tsabar kaunar da take yi masa amma a yanzu ta shiga wasi-wasin zuciya, bata san mene ne dalili ba. A can cikin motar Anas ya ji hawayen bakin ciki ya fara sartu akan kuncinsa Shin ya ya abubuwa zasu zama haka ne ya ya aka yi duk sa'a ta ta kwace min, don me yar iskar nan Hasiya za ta yi min haka. A da kafin Anas ya zo ya dauka zai bar gurin Ummi dauke da farin cikin da bai taba jin irinsa a duniya ba To amma a yanzu wani karamin digo na kalanzir ya riga ya fada a cikin kokon ruwan shan kaunarsa ya kuma ji a jikinsa cewa in ba wani abu daga Allah ba dan digon kalanzir din nan sai ya gurbata dukkan illahirin dandano na ruwan shan kaunarsa A karo na farko tun bayan da ya girma sai Anas ya fara kokarin yin addu'a to sai dai kuma har sa'ar da ya fara hangen fitulun lantarkin da ke makale a jikin katangar gidan Mabaruka gurguwa bai iya tuno koda addu'a daya ba *** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya harari kwanon tubanin da ke gaban sa ya mika busassun yan yatsunsa guda uku ya cafko wani katon tubani mai siffar kwado ya dago shi sama yana nazarinsa sai da ya dade a haka sannan ga mamakina sai na ga ya mayar da tubanin cikin kwanon ya dubeni cikin nadama ya ce "Nas cikina ya gama cika amma har yanzu bakina na muradin ci gaba da taunar tubanin nan." "Haka ne" na ce da shi "Ci gaba Baba Sidi na matsu in ji karshen labarin nan...sai na ji duk ma ka dada ruda labarin." Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya.TSOHON ALKAWARI-16 . "Ci gaba Baba Sidi, na matsu in ji karshen labarin nan...sai na ji duk ma ka dada ruda labarin." Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya ya dubeni ya ce. "Ai Nas zararrukan labarin ma sun zo karshe...bari na yi sauri na saka maka na karshe sai mu hadasu da sauran zararrukan labarin mu daure." "Haka ne." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin cikin takaici ya yi kamar zai dauki daya sai dai ya sauya shawara ya dubeni ya ce. Nas, tun karfe takwas na daren ranar da Anas ya tafi gurin Ummi, Mabaruka ta caba kwalliya, sannan ta sa hadiman gida suka shirya musu kayan shaye-shaye da tande-tande na musamman. Shiru-shiru karfe tara ta wuce babu Anas babu labarinsa, wannan shi ya sa Mabaruka gurguwa rarrafawa gaban dan gajeren madubin da aka yi mata na musamman ta dubi mummunar fuskarta a jiki sai ta ji kamar ta fashe da kuka, domin ta lura duk kwalliyar da ta yi ta damalmale. Cikin sauri ta rarrafa zuwa bandakinta na musamman ta kuma kwashe mintuna talatin tana wanka gami da shafe-shafe da goge-goge, fitowarta ke da wuya daga bandakin sai tangamemen agogon azurfa wanda mahaifiyarta ta bata ya dauki rurin karfe goma na dare. "Na shiga uku." Mabaruka ta fada a fili kai ka dauka tare suke da wani a dakin "Me ya tsayar da Anas ne har yanzu?" Mabaruka ta tambayi kanta, Nan da nan sai ta ji jikinta ya dauki rawa, zuciyarta ta fara harbawa sannan sai ta fara zargin kanta da wauta. Dan me zan bar shi ya tafi shi kadai? Ta kuma tambayar kanta to sai dai wannan karon Mabaruka na da amsar tambayar cikin zuciyar ta. Anan sai Sidi mai jaka ya dan yi shiru yana kallona, sannan sai ya ce. "Nas akwai wani sirri da Mabaruka take son sanar da Anas tun kusan kwanaki uku da suka shude amma yar rashin jituwar da suka samu a daren da aka yi liyafar nan shi ya sa ta boye masa. "Wanne sirri ne wannan?" Na tambayi Sidi mai jaka. "Bi ni a hankali Nas, ni ma zakin mazallako ne kawai da daga ciki yana rokon uba kwabo shi ya sani azarbabin fada ma, amma da sannu zan kawo ka kan zancen, kai dai bani aron hankalin ka mu koma kan zaren labarin da muke. "Na baka." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dan faki idanuna sannan sai ya mika hannu ya zaro tubani guda ya jefa a bakinsa kana ya ci gaba da cewa. "Abin da ya sa Mabaruka ta bar Anas ya tafi shi kadai shi ne ta san cewa Anas fa ba kaunarta yake yi ba ko kankani, ita ce dai ke kaunar sa, haka nan ta tabbata muddin ta uzura da manne masa, to za ta sa ya kuma tsanarta a cikin zuciyarsa wanda hakan na iya kawo sanadiyyar rabuwarsu. Duk da irin kuri da cika baki da mabaruka ke masa cewa idan ba zai iya ba ya ajiye mata duk dukiyarta ya bar mata gidanta, babu abin da Mabarukan take tsoro da fargaba irin rabuwa da Anas, domin ta san idan ta rabu da shi tana iya haduwa da cutar da za ta kawo ajalinta a kusa, wannan dalili shi ya sa duk da tana zargin karya Anas yake yi ba gurin abokansa za shi kawai ba Mabaruka ta kyale shi ya tafi shi kadai, tare da fatan me yiwuwa idan ta bashi yana yan walawa shi kadai yana iya dan kaunar ta ko daidai da kwayar zarra ne, haka nan tare da karfin gwiwar cewa idan ya dawo zata fada masa abin me yiyuwa zai iya sa shi farin cikin da dole ne ma ya tarairayata ko da bai so ba. Wannan shi ya sa Mabaruka ci gaba da kwalliya tun magriba har zuwa karfe goman dare bata gama ba. "Bari in sa wannan shudiyar rigar me yiwuwa ta burgeshi, na ga ran nan da na sa irin ta kamar yana satar kallona." Mabarua ce ta ci gaba da zance da kanta sa'ar da take kokarin sa rigar. Bayan ta gama sai ta sake rarrafawa zuwa gaban madubi ta kuma duban kanta a karo na goma sha uku. Abin da ta gani ya dan faranta mata rai babu dai yabo babu fallasa, domin ba katon goshinta ba kawai, hatta dan tababben hancinta mai kamar kataura ya dan mike sakamakon matsar da ya sha a hannunta, haka nan fuskarta na dan sheki, to sai dai kuma ta fuskanci kamar hoda ta so ta yi mata yawa a fuskar Wannan ya sosa mata rai, dan haka a fusace sai ta mika hannunta zuwa kan gado ta janyo wani abu da take tsammanin me yiwu rigarta ce, da zummar ta yi sauri ta goge hodar dake fusakarta domin duk sosunan kwalliyar sun hade da kalolin hodoji iri-iri sun baci. Janyo abin ke da wuya sai ta ga ashe wandon Anas ne. Cikin farin ciki sai ta kara wandon mijin nata akan fuska, sannan ne fa kudundunnaniyar takardar fara ta fado daga cikin aljihun wandon. Mabaruka ta ji gabanta ya fadi ras, tun kafin ma ta dauki takardar. Hannunta na rawa ta dubi takardar cikin tsananin zargi sannan sai ta jefar da wandon gefe guda ta dauki takardar ta fara karantawa.... . ".....Ni ce Ummi." Mabaruka ba ta iya maimaita karatun takardar a karo na biyu ba, sai ta kifa kai a jikin gadon ta fashe da kuka mai karfin gaske wanda har rawar da gangar jikinta ke yi ta sa gadon shima ya dauki rawa Kofar dakin ta bude a hankali sannan Anas ya shigo fuska a turbune shigowarsa ke da wuya sai ya tsaya turus kamar wanda ya ji shi cikin fasassun duwatsu a cikin duhun dare. "Ku...kukan me ki ke yi Mabaruka ba gani na dawo ba." Mabaruka ta dago kai jiki na rawa cikin kuka ta ce. "Mene ne amfanin dawowar ka tsohon mayaudari! Ai sai ka koma can gidan su Ummin ka kwana a can...!" Ta kara fashewa da kuka. "Ban fahimci abin da ki ke nufi ba." Anas ya ce cikin shakka, domin bai san munafukin da ya fada mata daga gidan su Ummi yake ba. "Ya za a yi ka fahimce ni, tun da ka tsaneni! Ba ka kaunata!! So kake na mutu da bakin cikin kaunarka ko Anas?" Hakan da ta fada sai Anas ya ji tausayinta ya kamashi. Ga mamakinsa sai ya ga Mabaruka ta rarrafa inda ya ke tsaye ta rike kafafunsa cikin kuka ta ce. "Anas....don Allah ka yi min rai ka kaunace ni ko da daidai da na kwana daya ne... Haba Anas don ka ga ni mummuna ce...dan ka ga ni gurguwa ce....shi ne kake son kashe ni." Ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji kwalla ta zo idanunsa, cikin sauri ya durkusa a gabanta ya dafe kanta. "Daina kuka Mabaruka bari in yi miki bayanin