← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 21

Sashe 19

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

matarsa. Tsawon lokaci suna nan haka a kwance ba sa ko motsi cikin bacin rai, can sai Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a tausashe. "Anas..." "Na'am." Anas ya amasa bayan jinkirin kusan minti guda. "Ban ji ka ce komai ba ko ba ka farin ciki da dan da zan haifa ma" Anas ya ji kamar Mabaruka ta soka masa kibiya a tsakiyar zuciya. Shiru na yan dakiku, Anas bai amsa ba. "Anas...ba ka ce komai ba!" Mabaruka ta ce cikin wata irin shakakkiyar murya tana shirin fashewa da kuka. "Me ki ke so in ce dake?" Anas ya ce da ita a fusace. Hakika tuni ya gama yankewa zuciyarsa shawara shi fa ya gaji da wannan daurin talala da mulkin mallaka. Cikin kaduwa da jin abinda ya ce Mabaruka ta turar da hannunsa ta dan dago kai ta dubi fuskarsa a cikin dan hasken fitilar dakin dake ajiye akan wani teburi na alfarma. "Anas...ba ka kaunata ko?..." Anas ya yi shiru na yan dakiku bai amsa ba sannan sai ya tashi zaune ya ce. "Mabaruka ya kamata mu fuskanci gaskiya, sanin kanki ne tsakani da Allah cusa min ke aka yi...ba wai bana kaunarki bane amma..." "Ya isa haka!" Mabaruka ta daka masa tsawa cikin wata karyayyiyar murya. "Ba sai ka karasa ba Anas, na yarda tabbas ba ka kaunata." "Ka da ki zarge ni, ki zargi mahaifiyarki Mabaruka da kuma ke kanki." Aka sake yin shiru na yan mintuna. "Ummi ce ko?" Mabaruka ta bata shirun da wannan tambaya. "Ba zan boye miki ba Mabaruka...wall ahi duk duniya babu wacce nake kauna kamar ta. Mabaruka ta ji kamar ya watsa mata wuta a doron zuciya. Wani abu mai kamar amai ya zo ya toshe mata makogwaro. "Anas...mu sawwake wa juna ina ganin shi zai fi ko?" "Kwarai kuwa...nima da niyyar da na zo kenan." Cikin sauri kamar da wasa sai Anas ya lalubi aljihunsa ya zaro takardar da tun a cikin mota ya rubuta a lokacin da zai yi fakin da ita a gareji. Hannunsa na rawa ya mika mata ya ce baki na rawa. "Na sake ki saki biyu." Mabaruka ta karbi takardar ta karata a kirjinta, kana ta lumshe idanu, ga mamakin Anas, sai ya ga ta dubeshi ta ce. "Don Allah taimaka ka kaini falo." Anas ya ciccibeta, cikin damuwa domin tausayinta ya gama lullube zuciyarsa, to amma babu abin da zai iya akan hakan. Lokacin da ya ajiyeta, sai ta dube shi ta kuma cewa. "Dan Allah koma daki ka jirani." Ta dan yi shiru sannan sai ta kuma cewa "Za ka bari gari ya waye ko yanzu za ka fita?" Anas ya dubeta a rude sannan ne to fa dimbin asarar da zai dibga ya darsu a zuciyarsa, tabbas ya san ya rabu da masifa ya fada masifa. Domin a gurinsa Mabaruka masifa ce, haka kuma rabuwa da ita ma na nufin sake shiga cikin masifar talauci Koda yake dai ai ina da yan kudi a banki da gida da mota da kuma otal din da mahaifiyarta ta bani Anas ya fadawa kansa "Duk abin da ki ka ce haka za a yi in ba kya son ganina yanzu ma sai in tafi" Mabaruka ta danne kukan dake kokarin kufcewa daga makogwaronta. "Dan jirani a dakin to ina zuwa" Anas ya koma cikin dakin ya zauna gami da ajiyar zuciya Ga mamakinsa sai ya ji tamkar an dauke masa wani katon kaya mai nauyin tsiya daga doron bayansa Sannan ne to ya jiyo sautin muryar Mabruka daga cikin falon tana yiwa Mahaifiyarta waya Tsawon mintuna talatin Anas na nan zaune yana jran dawowar Mabruka gurguwa lokacin ne ya juyo sautin injin mota an shigo farfajiyar gidan Cikin sauri Anas ya mike a rude ya nufi taga ya leka. Tun kafin ya gama bude labulen tagar ya hangi dogon direban gidansu Mabaruka ya budewa Hajiya Aliya kofar katuwar (Jeep) din nan baka ta fito jikinsa na rawa Anas ya nufi falon inda Mabaruka take Anas ya sameta zaune akan kilishin dake mamaye da tsakar dakin kan talfon din rike a hannunta ta kwantar da kanta akan kujerar dake daf da ita gaban rigarta sharkaf da hawaye "Me ya kawo mahaifiyarki kuma cikin wannan maganar? Don me ba ki fada min ita za ki kirawo ba?" Mabaruka ba ta dago kai ba balle ma ta kalleshi sai ta ce a sanyaye "A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU ƘARE."TSOHON ALKAWARI-18 . "A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU KARE." Kofar babban falon ta bude Hajiya Aliya ta shigo a fusace bata ko damu da ta zauna ba sai ta dubi Anas ta ce "Tun da ka sake ta me kuma ka ke jira sai ka fice ka bar mata gidanta." Babu kunya, babu tsoro sai Anas ya dubeta ya ce "Gidanta ko gidana? Na dauka ke ki ka fada da bakinki kin bani gidan nan?" Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce Duba bayan ka wannan shine Yarima Gangariya na mallaka masa wan nan gida kuma daga zarar ta haihu za'a daura musu aure Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce "Kai dai jahili ne wallahi Anas kai ka taba gani inda aka baiwa mutum kyautar gida babu shaidu kuma babu takardu? Ko ka taba ganin inda aka baiwa mutum kyautar otal babu shaidu kuma babu takardu?" Anas ya ji wani zazzafan gumi ya karyo masa Hajiya Aliya ta dubeshi ido da ido ta ce "Ka yiwa kanka matsiyaci sai ka koma cikin talaucin ka motar da na baka na kwace kayata domin daman duk takardunta yana hannuna haka ma gidan da kuma otal din da na baka duk na kwace su. Daga yanzu ba kai babu karbar ko kwabo daga kamfanunnukanmu matsiyaci." "Bai kamata ki yi min haka ba?" Anas ya ce cikin kaduwa domin a shashancinsa bai taba tunanin haka ba. "Ba ka da hankali Anas tashi ka fice min daga gida. Rufeshi zamu yi a cikin daren nan in koma da yata gida ka yi ma sa'a wallahi da yan kudin da suke bankinka ma sai na yi hanyar da za su salwanta...amma ka yi sa'ar ta." Ta dan yi shiru tana duban Mabruka. "Ita ce ta ce na kyale ma kudin da ke cikin ma'adanin ka. Sai ka fice Allah ya bamu alheri." Anas ya dubi Mabruka a rude sannan sai ya juya zuwa cikin dakin. Ba a dade ba ya hado kayan sawarsa a cikin jakunkuna guda uku ya ratayo su da kyar sannan ya dubi Mabruka ya ce. "Na gode Mabruka." Sannan sai ya fice daga dakin. Wani abin mamaki shi ne tun da Mabruka take da Anas, bai taba fada mata kalmar da ta amince da ita har zuciyarta ba sai wannan godiyar da ya yi mata. Koda Anas ya nufi farfajiyar gidan sai dogon direban nan ya tare shi, ya karbi biyu daga cikin jakunkunan uku ya ce. "Mabruka ce ta ce duk inda ka ke son zuwa na kai ka." Anas bai san menene mutunci ko so ba sai yanzu. Abin mamaki sai ya ji hawaye ya yi sartu akan kuncinsa. Koda direban motar ya fara tafiya da su sai Anas ya yi ajiyar zuciya. A kalla dai ko da na rasa arziki ina da wacce na fi kauna da so a duniya Ummi! Anas ya ce da kansa. "Yallabai ina zan kai ka?" Anas ya dubi direban a rude sannan yace. "Bari in tuna"**** Ummi ta ji hawaye ya yi sartu akan kundukukinta sa'ar da ta gama karanta takardun. Hawayen da ke zuba a yanzu hawayen bakin ciki ne da farin ciki. Bakin cikin shi ne ya ya ma za a ce wai wadannan mutane da tun da ta fara budar ido su take gani a ce wai ba mahaifanta bane yayin da kuma farin cikin shi ne yanzu ta fahimci tana da damar mallakar abin da ta dade tana kauna tun da ta zo duniya. Haba gaskiya fa ta ji ba ta san rabuwa da shi tana bege da shaukin son zama da shi ashe ba dan uwanta ba ne na jini. Ba ta ji shigowarsa ba sai inuwarsa ta gani a kanta. Ta juya a razane, sai suka yi ido biyu da Abdulmalik. Nan da nan sai ya yi murmushi sannan ya mika mata wani farin kyalle ya ce a tausashe. "Goge hawayen ki." Ummi ta ji kunyarsa ta rufe ta, ta kasa hada ido da shi, kanta a sunkuye ta karbi kyallen gami da ajiyar zuciya. "Abdulmalik, me ya sa baka fada min ba tuntuni...kuma dan Allah wannan abin da ka rubuta min gaskiya ne?" Abdulmalik ya dubeta da murmushi ya ce. "Na taba fada miki karya?" Ummi ta yi sauri ta girgiza kai. "Kuma na ji kin kira sunana kai tsaye na dauka ni yayanki ne ko kin fasa yayan da ni?" Ummi ta rufe idanu a kunya ce ta ce "Ni na isa, ai har abada kai Yayana ne kuma..." Ta yi shiru ba ta karasa ba. Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce. "Karasa mana kuma me?" Ummi ta fara wata sassanyar dariya. "Ni ba zan karasa ba." "Allah sai kin karasa." Abdulmalik ya ce cikin dariya. Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba, ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce. "Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa." Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa, sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi ta yi rubutu akan tafin hannunsa, sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin. . Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce "Karasa mana kuma me?" Ummi ta fara wata sassanyar dariya. "Ni ba zan karasa ba." "Allah sai kin karasa." Abdulmalik ya ce cikin dariya Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce "Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa." Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi
Chapter 19 · 0% Book details