Sashe 7
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya dubi mummunar fuskar Mabaruka na dakika uku sannan ya sunkuyar da kansa. "Na...kalleta.. ." Aliya ta yi murmushi "Anas, abin da ya sa na ce ka dube ta shi ne, domin ka ajiye hotonta a cikin zuciyar ka, domin ita ce matar da za ka aura." Anas ya dago kai cikin tsananin kaduwa, "Hajiya...ban fahimce ki ba?" Aliya ta dubeshi da murmushi. "Sannu a hankali za ka fahimce ni ka kuma fahimci dalilin da ya sa na ce da kai ita za ka aura." Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "Da farko dai ina son ka sani cewa ni ce na sa Mabaruka na ce da ita duk namijin da ta gani ta ji ya kwanta mata a rai ta kawo min shi.....TSOHON ALKAWARI-6 . "Abu na biyu kuma shi ne tun da aka haifi Mabaruka bata taba neman wani abu ta rasa ba, shi yasa to na ce da kai ita za ka aura, domin kaunarka ce ta sa ta kawo min kai." Anas ya ji kamar an dora masa buhun alhaki a tsakiyar kansa, domin ko mosti baya iya yi zaune yake ya yi mutuwar tsohuwa sai idanunsa ne ke ta kifkiftawa kamar idanun barawon akuya, to amma zuciyarsa na kai kawo. Cab! Na auri gurguwa mummuna! Ai da na auri wannan ma gara na auri uwar domin ta fita komai da komai.Anas ya share gumi sa'ar da zuciyarsa ta tuno masa da cewa wannan mummunar gurguwar fa da ake kokarin cusa masa, sunanta KUDI! "Anas." Aliya ta katse tunanin sa. Anas ya dago kai ya dubeta. "Ina son ka bani hankalin ka nan." Anas ya dube ta ido da ido ya ce. "Ina jin ki." "Idan ba ka san wannan yarinyar dake gabana ba bari in fada ma. Ka ga duk fadin kasar nan babu wata mace da ta mallaki kashi daya bisa hudun dukiyar da ta mallaka haka nan ita ce mace ta biyu a kudi a cikin duk matan Afirka Da mun biya ta mutane da tuni an aure ta ko dan a amfani kudin da take dashi, to amma kuma ni na fi son ta zabi wanda take so da kanta." Aliya ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. "A yanzu kai ta gani ta ke so shi ya sa ta kirawo ka gare ni. Anas ina so ka auri Mabaruka domin auren ta alheri ne a gare ka." Ta sake yin shiru a karo na biyu sannan sai ta dubeshi ta ce. "Nawa ake biyanka a wannan busasshiyar otal din da kake aiki?" Anas ya hadiyi yawu da kyar kwakwalwarsa sai juyawa take yi cikin kokon kansa. "Du...dubu takwas!" Aliya ta dubeshi ta fashe da dariya ta ce. "Dubu takwas! Kyakkyawan saurayi kamarka a dubu takwas? Ko kuwa kullum ne ake biyanka dubu takwas din? Anas ya girgiza kai. "Wata-wata ake biyana." Idanun Aliya suka zazzaro waje cikin tsananin kaduwa. "Wata guda a dubu takwas." Cab! Allah rufa asiri." Ta yi shiru na dan lokaci sannan ta sake duban Anas. "Idan yanzu na baka manajan daya daga cikin kamfanunnukanta albashin naira dubu dari biyu ya yi ma...a wata guda nake nufi." Anas ya ji zuciyarsa ta harbo da karfi kamar kibiya tana kokarin fasa masa kirji, dubu dari biyu! Tun da yake bai taba tsammanin zai sami dubu hamsin ma ba a duniya lokaci guda. "Ya...yi min." Ya ce da kyar domin makogwaronsa ya bushe. Aliya ta yi murmushi sannan ta ci gaba da cewa. "Ka je gida ka turo iyayenka domin nan da sati guda za a daura muku aure. Ina son kuma ka sani cewa daga yanzu duk inda kake so a duniya za ka iya sa kafar ka, haka nan ban da albashinka, duk karshen wata na yi maka alkawarin naira dubu dari daga cikin ribar da nake samu karshen wata a kamfanina na atamfa, sannan a matsayin kyauta ta musamman da zan yi ma a matsayin ka na angon yata zan saya ma wannan busasshiyar otal din da kake aiki a ciki, in sa a rugujeta a sake gina ma ita, in ya so sai ka zabi sunan da ka ga ya dace ka sa mata." Aliya ta yi shiru tana numfasawa, sannan sai ta mike tsaye ta dubi Anas ta ce. "Ka yarda zaka aure ta?" Anas ya ji kamar katanga ta fado masa a tsakiyar baya. Abu daya da ya tabbatarwa kansa shi ne in duk za a bashi duniyar nan domin ya kaunaci wannan mummunar gurguwa ba zai taba iyawa ba, to amma da albashin naiura dubu dari biyu a wata, da naira dubu dari a sama da kuma kyautar otal din da za a bashi, ya tabbatar ko da Mabaruka kuturwa ce sai ya aureta. Cak! Yau na zama miloniya cikin sa'a guda... Ya ce cikin zuciyarsa, koda ya tuna da cewa lagwada otal za ta zama tasa sai ya ji wani zazzafar gumi na farin ciki ya zubo masa tuntuni ya dade yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai rama wulakancin da manajan otal din ke yi musu, sai gashi a banza yanzu dama ta samu a bagas. Wani busasshen murmushin mugunta ya subucewa Anas nan da nan ya dauki alkawarin cewa duk ranar da ya mallaki ota din sai ya tikawa dan dukurkushin manajan dundu a tsakiyar baya. "Anas!" Aliya ta katse masa tunani "Tunanin me kake... Baka amince bane?" Anas ya girgiza kai cikin sauri sannan ya ce. "Kin ce cikin sati za a daura auren ni ko yanzu naira dubu takwas ce daidai a aljihuna ita ma ta albashin da aka biyani ce dazu da yamma." Aliya ta yi murmushi sannan ta ce "Tun da ka amince ina kai ina fargabar kudi, nan gidansu ka zo." Ta dan yi shiru sannan sai ta ce. "Kana jin naira miliyan goma zata isheka fara shirye-shirye kafin zuwa jibi". Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe ya dube ta a rude. "Miliyan goma kika ce ko kuwa dubu goma." Aliya ta fashe da dariya sannan ta dubi yarta Mabaruka wacce ke gefe ta yi tagumi tana sauraronsu ta ce "Miliyan goma na ce ko sun yi ma kadan a kara ma?"**** Sidi mai jaka ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici duk yawan tubanin nan ya hadiyesu baki daya saura kwaya uku kacal cikin kwanon. "Nas ga labari ya dauko dadi gashi kuma tubanina ya zo Gangara. Irin wannan abin shi yakansa wani lokacin na ji duk na tsani bada labari domin tubanin nan tamkar mota ce da man fetur idan babu shi ka san ban cika abin kirki ba". Sidi mai jaka ya yi shiru yana kallon cikin kwanon tubanin sannan ya dubeni fuskarsa a murtuke. "Kamata ya yi ka karasa min zuwa sallar Azuhur, idan na koma gida sai na sa kakata ta sake yi ma wani tubanin." Nan da nan fuskar Sidi mai kaja ta washe. "shi yasa nake son ka NAS. Domin daga na yi motsi sai ka gane abin da nake nufi." ya dan yi shiru, sannan sai ya ce, bari a gurguje na kulla maka wani sabon zaren labarin da wannan, domin naga kamar lokacin sallah ya kusa." Sidi Mai Jaka ya tsikari tubani na ukun karshe ya jefa a baki sannan ya dubeni. Nas, ina son ka dauka cewa tuni har an daura auren Anas da Mabaruka gurguwa." "Na dauka." Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubeni, sannan ya ci gaba. Wato Nas, watanni biyun da suka biyo bayan bikin Anas sun yi matukar jefa Anas a cikin sabon yanayi. Lokacin da Anas ya bar gidan su Mabaruka bai tsaya ko ina ba sai wurin iyayensa, jikinsa na rawa ya ce da su aure zai yi. Lokacin da labarin auren nasa ya watsu a cikin dangi sai aka yi ta zuwa ana taya mahaifansa murna, domin duk garin babu wanda bai san ko wacece Mabaruka ba. Da yawa daga cikin mahassada suka yi ta zunde, tsegungumi da gulma, suna cewa wai in ba lalacewa ba ina kyakkyawa kamar Anas ina auren gurguwa mummuna. Wasu daga cikin masoyansa sun taya shi murna, domin sun san duk da dai bai yi dacen mata ba, to amma ya yi bankwana da talauci har abada, wannan a gurinsu ya isa abin farin ciki, domin a tunaninsu Anas ya gama samin kwanciyar hankali da nutsuwa. To kamar yadda suke tunani NAS hakanan ta kasance a cikin watanni biyun da suka biyo bayan bikinsu, domin Anas ya sami hutun da bai taba tsammani ba a iya tsawon rayuwarsa. Da farko dai da yake daman shi ba damuwa ya yi ba da wani addini ba kullum kwanan duniya Anas baya tashi daga barci sai karfe goma sha daya na safe, sannan ne zai tashi ya yi wanka, sannan ya nufi wurin aiki. Zamantakewarsa da Mabaruka ta bashi mamaki, domin ya sami Mabaruka macece mai iya dadin magana, da tarairaya, duk kuwa da cewa gurguwa ce, wani sa'in sai su tafi bakin (Swimming pool) su yi ta wasa da katuwar bal marar nauyi, Mabaruka na zaune akan kujerarta a bakin ramin ruwan, shi ko yana ciki, idan ya jefo mata, sai ta cafe ta jefa masa. Wani sa'in kuwa sai Anas ya dauketa a mota su yi ta yawo a cikin gari suna bin guraren shakatawa abinsu da yake Anas gwanin ban dariya ne, sai ya yi ta yi Mabaruka tana dariya. Wannan ita tasa sau biyu ko uku kawai Anas ke zuwa gurin aiki a sati. "Kada ka dami kanka Anas da yawan zuwa wurin aikin nan kudi ne, muna dashi albashinka kuma ko kaje ko baka je ba dole ne a baka." Mabaruka ce ke cewa Anas haka a wata safiya suna karin kumallo. "Anas, zamanka kusa dani ya fi min zuwanka aiki, domin ni har kullum idan na dubeka sai na ji zuciyata ta yi fari tas, dan haka ne bana son rabuwa da kai koda dai dai da kankani...domin ..." Ta dan yi shiru tana duban Anas. Anas ya dube ta sa'ar da ya ji tayi shiru. "Domin muma me...?" Mabaruka ta dube shi. "Domin bana son wata mace ta mallaki zuciyarka a duniya idan bani ba, shi yasa ka ga na ce ma sau biyu kawai za