← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abin da ke zuciyata." "Ba sai ka yi ba Anas, na ri ga na sani...ni dai ina rokon don Allah ka kauna ce ni kada ka sa bakin ciki ya kashe ni, ni da danka da ke cikina!" Anas ya ji kamar an zunguri zuciyar sa da allura. "Wanne dana ki ke nufi a cikinki?" Ya tambayeta a rude. Mabaruka ta dada kankameshi sannan ta fashe da kuka ta ce. "Anas tun shekaran jiya na ke son fada ma likita na ya sanar da ni ina da ciki wata uku!"*** Na dubi Sidi mai jaka a rude nace "Haba Baba Sidi ya ya tun dazu ka ke labarin nan amma ba ka ce tana da ciki ba sai yanzu?" Sidi mai jaka ya dubeni da busasshen murmushinsa ya ce. "Nas ke nan, abin da ba ka sani ba shi ne idan na fada maka tun dazu cewa tana da ciki ai na ragewa labarin dadi, haba Nas kai sai ka ce ba marubuci ba. Bari in sako maka zaren labari na karshe sai in hadasu da wannan na kulla ko ma kai ga karshen labarin nan." "Haka ne." Na ce dashi ba musu. Yauwa Nas, ta yanzu ina son ka sa a zuciyar ka cewa ga Ummi nan ta fito daga dakinta a rude, wannan kuwa fitowa da ta yi a washe garin ranar da Anas ya zo mata zance ne. Ummi ta dubi dan karamin agogon da ke sanye a santalelen hannunta, karfe hudu da mintuna biyar agogon ya nuna. Cikin sauri sai ta nufi kofar dakin Abdulmalik ta kuma kwankwasawa, a karo na goma sha takwas a ranar. Shiru ba a amsa ba, Ummi ta dada rudewa. Shin ina Yaya Abdulmalik ya tafi ne tun da sassafe har yanzu bai dawo ba. Abin da ya dada tayar mata da hankali shi ne a daren jiya sa'ar da ta shigo gida bayan sun rabu da Anas, ba ta tsaya a ko ina ba sai dakin Abdulmalik, domin tana da tambayoyi masu yawan gaske da take bukatar amsarsu. Lokacin da ta isa kofar dakin sai ta hango wutar dakin a kunne take, to sai dai kuma kamardakin a rufe. Me yiyuwa har ya yi barci. Ummi ta ce a ranta, to amma sa'ar da ta matsa kusa da kofar dakin sosai, sai ta ji motsi a cikin dakin kamar ana taba takardu. "Salamu alaikum." Umma ta yi sallama lokaci guda kuma ta tura kofar dakin. Ga mamakinta sai ta ji kankam kofar dakin a rufe take. "Yaya Abdulmalik bude min na dawo" Ummi ta ce Shiru ba a amsa ba "Yaya Abdulmalik." Ta sake kiran sunan a karo na biyu "Ina jin ki Ummi..ki bari sai gobe ma hadu" Ummi ta ji gabanta ya fadi nan da nan ta ji jikinta ya dauki rawa kamar zazzabi zai rufe ta Wannan shi ne karo na farko da yayan nata ya fara fushi da ita amon muryarsa ya fadi sakon da ke zuciyarsa "Yaya Abdulmalik..me na yi maka? Ka bude min mana" "Babu abin da ki ka yi min Ummi ta fi dakinki kawai ma hadu gome...yanzu wasu yan rubuce- rubuce nake yi bana son a dame ni" ummi ta ji kamar ya watsa mata wuta Cikin kunan rai ta jingina bayanta a jikin kofar dakin idanunta suka fara ambaliyar kwalla na mintuna biyu sannan a hankali sai ta nufi dakinta domin ta tabbata ba zai bude mata kofar ba Tana zuwa dakinta sai ta fada akan gadonta ta fashe da kuka tabbas jinin Abdulmalik bai hadu da na Anas ba Ummi ta fada a ranta*** Na dubi Sidi mai jaka a rude na ce A wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata "Ki bi a hankali Yaya Ummi kardai....TSOHON ALKAWARI-17 . A wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata "Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada a tarkon sa ba" Shin ko abin da ta fada gaskiyar ne, shin ko Yaya Abdul Shima ya san halin Anas ne shi yasa yake fushi da ni. Ummi ta kuma tambayar kanta, sannan sai ta dada fashewa da kuka, a haka barci ya dauketa. To amma kafin barcin ya saceta sai da ta yiwa kanta alkawarin cewa in dai har alakarta da Anas ne ya batawa Abdulmalik rai, to babu mamaki za ta rabu da Anas duk kuwa da irin kaunarsa da take yi, domin da ta bakantawa yayanta Abdulmalik gara ta rabu da abin da take kauna. Washe gari da sassafe, tana idar da sallah sakamakon makara da ta yi da bata tashi da asuba ba, sai ta nufi dakin Abdulmalik cikin sauri ta tura kofar dakin babu ko sallama sai ta ji kofar a rufe. Cikin sauri ta juya da baya a kidime ta nufi dakin mahaifiyarsu. "Mama ina Yaya Ya tafi?" "Ya fita tun da duku-duku nima ban san ina za shi ba, ya dai ce dani ba zai dawo ba sai can yamma. Tun daga wannan lokaci Ummi ke ta faman safa da marwa daga dakinta zuwa dakin Abdulmalik har zuwa yanzu babu shi babu alamarsa. Hawayen bakin ciki ya yi sartu akan kumatunta. Ummi ta yi sauri ta goge sannan ta nufi dakinta ta zauna a bakin gado ta kurawa kofar dakin nata idanu cikin takaici. Wannan shi ne lokaci mafi tsayi a rayuwarta da ta taba zama ita kadai ba tare da dan uwanta Abdulmalik ba a kusa da ita. Tana nan zaune ta zubawa kofar dakin nata idanu tana jiran ta ga ta inda Abdulmalik zai bullo, sai aka yi sallama. Da farko muryar mahaifiyarta ta fara ji daga waje tana cewa. "Ki shiga tana ciki." Cikin sauri Ummi ta goge hawayen da ke kumatunta ta mike tsaye, a daidai lokacin da ta ji an sake cewa. "Salamu alaikum." Sannan sai ta ji an nufo kofar dakin. Ummi ta dubi Hasiya sa'ar da ta shigo dakin. "Sannu da zuwa Hasiya dama wallahi ina son ganin ki." "Ni ma son ganin naki ne ya kawo ni Yaya Ummi." Hasiya ta ce lokaci guda kuma ta zauna a bakin gadon ta dubi Ummi. "Ga ni me ki ke son yi min?" "Ke ma ai kin sani." Ummi ta ce tana dubanta "Wai dan Allah abin da ki ke fada min jiya a gaban wannan saurayin nawa gaskiya ne?" Hasiya ta fashe da dariya ta ce "Oh! Yaya Ummi kenan, ta wallahi kima daina kiransa da suna saurayin ki...don kin ga nima din nan babu irin abin da bai fada min ba amma daga karshe ya koma kan wata kawata Samira..wallahi sai da na yi rashin lafiya da kyar Allah ya yaye min masifar kaunar sa daga zuciyata na huta." "Wai ki na nufin ki ce saurayin ki ne da?" Ummi ta tambaya. Kina shakka kenan to bari ki ga zahiri." Hasiya ta bude cikin jakar da ke kan cinyarta sannan ta zaro wani hoto ta mikawa Ummi, "Kalli wannan." Ummi ta zurawa hoton idanu cikin kaduwa. Tabbas Anas din ta ne, shi da Hasiya a bakin otel din da suka yi liyafar bikin zagayowar ranar haihuwar Mabaruka gurguwa, abin da ya fi kona mata rai a hoton shi ne, hannun Anas na hagu dare-dare yake akan kafadar Hasiya. Hannun Ummi na rawa ta mikawa Hasiya hoton. "Ungo abin ki." Hasiya ta girgiza kai ta ce "Ki rike shi a gurinki, idan ya dawo ki nuna masa hoton ki tambaye shi me ya sa bai aure ni ba." Hasiya ta mike tsaye ta ce "Bari in karasa gida Yaya Ummi...daman daga unguwa nake shi ne na ce bari in biyo ta nan domin ba zan bari wannan kyakkyawan macijin ya sake saran yar uwata mace ba. Sai an jima." Da haka ta fice daga dakin ta bar Ummi cikin kaduwa dauke da hoton a hannunta, ba tare da ta iya yi mata ko da rakiya ba. Bayan ta kalli hoton na mintuna biyar sai ta mike tsaye, sannan ta daga karkashin matashin kanta ta jefa hoton, kana sai ta mike cikin sauri ta nufi dakin Abdulmalik domin ta sake dubawa ko ya dawo. Tana zuwa kofar dakin sai ta sake turawa babu sallama domin a tunanin ta idan ta yi sallama Abdulmalik ya ji muryarta me yiyuwa ba zai bude ba, zuciyarta na harbawa das! Das!! Das!!! Ta shiga dakin, tana shiga sai ta yi turus, Abdulmalik baya cikin dakin. Sannu a hankali ta shiga dakinta jikinta na rawa sannan ne to ta hangi tarin takardu farare an cikesu da rubutu akan wani dan teburin gilashi dake kusa da gadon Abdulmalik, sannan sai idanunta ya kai ga wata takarda fara kwaya daya jal akan gadon a jikinta an rubuta kamar haka;- Masoyiyata Ummi ki karanta takardun dake kan teburin nan domin amsoshinki duk suna cikin takardun..." Hannunta na rawa ta dauki takardar ta juyata a hannunta sannan sai ta dauki sauran takardun dake kan teburin jiki na rawa ta zauna akan gadonsa ta fara karanta wani abu mai kama da almara..labarin wadansu mutane da yaki ya korosu suke gudun hijira. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce "Ina fatan dai kana biye dani Nas?" "Kwarai kuwa Baba". "Yawwa Nas, to bari mu koma kan wancan tsohon zaren labarinmu inda muka bar Anas a durkushe a gaban matarsa Mabaruka gurguwa. Sidi mai jaka ya yi shiru sannan sai ya sake zarar wani katon tubani ya jefa a bakinsa ya dubeni ya ce. "Ba zan iya hakura da cin tubani ba Nas, sai dai tumbina ya fashe Tsawon dakika talatin Nas, Anas yana durkushe a gaban Mabaruka cikin tsananin kaduwa yaya ma za ta bari ta yi ciki? Anas ya tambayi kansa, wani bakin ciki ya lullube zuciyarsa. A haukan Anas ya gama imani da cewa babu makawa Mabaruka mummunan jariri ko jaririya za ta haifa masa a matsayin dansa. Wannan tunani shi ya sa wani zazzafan gumi barkowa akan goshin Anas. Cikin karfin hali Anas ya ciccibi Mabaruka ya kwantar da ita akan gado sannan ya kwanta a kusa da ita ya yi shiru, domin kwakwalwarsa lokacin ba za ta iya tunanin komai ba sai na Ummi. A zuciyarsa yana cewa, ina ma ace cikin nan Ummi ce ta yi shi a matsayin
Chapter 18 · 0% Book details