← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 21

Sashe 10

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan mun sha cacar baki kusan mintuna bakwai, na shawo kanta da kyar, ta sake cika min kwano da tubani, a wannan karon har sun fi wadancan girma domin ba a son ranta ta yi su ba. Na riski Baba Sidi mai jaka zaune akan tsohuwar kujerar katakonsa yana jan carbi, tun kafin na gama yi masa sallama ya dago kai ya dubi kwanon dake hannuna cikin fara'a, kamar karamin yaron da ya yi ido biyu da alewa mai tsinke. "Tsohon alkawari a karo na biyu, lallai Nas ka kyauta min." Ya ce sa'annan ya mika hannu ya karbe kwanon daga hannuna tun ma kafin na ajiye shi da kaina. Sidi mai jaka bai jira komai ba, sai kawai ya bude kwanon tubanin ya fara juya tubanin da yan yatsunsa bayan wani dan lokaci ya tabbata da cewa sun juyu yadda ya ke so don haka sai ya can ku wani kato ya jefa cikin bakinsa sannan ya dubeni. "Nas, ina fatan dazu kana biye dani a labarin da na fara baka." Cikin sauri na gyada kaina. "Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas ya shiga bandaki ya fara karanta wasikar Ummi harma take cewa dashi tana son ganinsa a daren washe garin ranar Sidi mai jaka ya gyada kai da murmushi. "Wani lokaci ina son mutum mai saurin rike al'amura a cikin kwakwalwa nan da nan ba tare da mantuwa ba." Na dubeshi da murmushi a karo na farko na ce. "Ai kuwa in ka dauke labarai babu abin da kwakwalwata ke iya rikewa domin koda sunan mutane in ba dadewa muka yi da kai ba sai ka yi ta zuwa ina kiranka da kai!" Sidi mai jaka ya fashe da dariya sannan ya canko wani katon tubani ya sha ya ji jajur dashi ga girma kamar dankali ya miko min. "Ungo wannan Nas jefa a bakin ka." Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. "Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi...TSOHON ALKAWARI-9 . "Ungo wannan Nas jefa a bakin ka." Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. "Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi har ya fi na dazu." Na dada girgiza kai. Sidi mai jaka ya zunkuda kafada, "Ka cuci kanka Nas, ni duk abincin duniya ban ga abin da zai zo a na biyun tubani ba a gare ni. Ya sake tsikaro guda ya jefa a bakin salatinsa sannan ya juya ya dubeni idanunsa na zubar hawaye kamar kuturu. "Nas, zaren labarin dana fara baka labari dazu ya kare iyakarsa kenan." Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. "Haba Baba Sidi, kai fa ka ce dani Ummi ta ce tana son ganinsa washe garin ranar, kuma yanzu ka ce dani wai zaren labarin ya kare." Sidi Mai Jaka ya yi murmushi "Haba Nas kai fa yanzu mun zama jiki sai dai ka fadawa wani ni, sanin kanka ne idan na ce da kai zaren labari ya kare to ya kare din tabbas, dole ne sai na sako sabo sannan na jona ma shi da bakin wannan tsohon labarin da na saka. Ya dan yi shiru, sannan ya sunkuyar da kai. Nas ina son ka dauki zuciyarka cancak ka maishe da ita can wani lokaci, kuma wani zamani mai dan tsayi na a kalla shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Na dubi Sidi mai Jaka cikin mamaki bani da abin cewa dan haka sai na gyada kai na ce dashi "Na mayar." Sidi Mai jaka ya ce "Yauwa Nas haka nake so da kai." * * Shekaru ashirin da biyar da suka wuce wani dogon mutum fari siriri buzu-buzu balarabe-balarabe, ya sauka a garin nan dauke da yar tabarmarsa ta kaba akai yana neman inda zai sauka. Ba don komai ba kuwa sai don lokacin da ya sauka a garin nan cikin dare ne tare suke da matarsa ita ma kusan irin kirar su daya to sai dai kuma kyakkyawa ce ta gani a fadawa sarki. Wannan mutum dogo fari siriri babu komai a cikinsa sai hanji domin rabonsa da abinci kwana biyu kenan haka ma matarsa. Haka nan kuma yadda cikinsa yake hakanan aljihunsa yake, karaf babu ko karfanfana. Mutanen guda biyu mace da mijinta suka shigo birni, mijin na gaba dauke da tabarmar kaba, ita ko matar na biye dashi a baya dauke da wasu tsummokarai da ita kanta bata san amfaninsu ba. Me yiwuwa dai tana dauke da tsummokaran ne don cika umarnin mijinta, babu mamaki kuma sabo da yi ne wai gawa da gatsine. To koma dai mene ne wannan mutane dauke suke da muguwar yunwa ga kishi ga gajiya, ga babu tabbacin gurin kwana, sannu a hankali suna yawo cikin birni tsakanin manya- manyan gine-gine na alfarma can sai matar ta jefar da kayan tsummokaran dake kanta ta durkusa, ta rike ciki. "Wallahi...mai gida ni na gaji." Ta ce cikin wata irin bakuwar Hausa. Mutumin ya ajiye tabarmar keson dake kansa sannan ya dubi dankareren gidan dake gabansu wanda ke ci reras da fitulu kamar rana. Ya dubi matarsa cikin tsananin tausayi. "Ban ga laifinki ba HINDATU, ai kin yi ma kokari." Ya dan yi shiru idanunsa akan katon gidan dake gabansu. "Gashi wannan gidan ma kamar babu kowa a cikinsa, da sai in karasa na barato mana dan abin da zamu sa a bakinmu." Matarsa Hindatu ba ta ce komai ba, maimakon hakan ma sai ta kwanta a kasa ta dora kanta akan kullin tsummokaran ta kurawa sararin subhanahu idanu. Hankalin mijinta ya dada tashi, ya san cewa dadin ta yunwa ce kawai, duk wannan mai sauki ne, domin sun riga sun saba da jin yunwa, tun sa'ar da yaki ya barke tsakanin buzaye yan tawaye da gwamnatin kasarsu basu kara samun damar wani jin dadin rayuwa ba. Koda yake can ma ba wani cikin kwakkwaran jin dadi suke yi ba, to amma akalla dai kafin barkewar yaki suna da kwanciyar hankali wannan da sauran matsalalo halayyar yaki marasa adadi su suka sa wadannan mutane sabo da duk wata irin wahala, a cikinsu har da ma jimirin yunwa. Dan haka abin da ya sa hankalin mijin matar nan Hindatu ya tashi shi ne, ya san tana da juna biyu, akalla zai kai wata uku. Tun sa'ar da ya ki ya barke suka fita gudun hijira mutumin ya fitar da ran cewa matarsa zata sami damar haife cikin, kullum kwanan duniya cikin zullumi yake, yana sauraron zubewar cikin, amma cikin ikon rabbana har zuwa wannan lokaci matar bata ko taba ciwon kai ba ballantana a yi zancen zubewar cikin sai yanzu da ta fadi a gabansa ta ce dashi ta gaji ga kuma muguwar yunwa. Dogon mutumin ya mike tsaye sannan ya sake duban matarsa cikin damuwa kana ya dubi sararin samaniya sai ya ga tuni ya hade da gajimare an kuma fara rugugin aradu haka nan Walkiya sai haskawa take yi wal- wal kamar tana daukar hotonsu. "Sannu Hindatu dan jirani kadan na karasa kofar gidan can me yiwuwa idan nayi sa'a ko masamu wani ya taimakomu da abin da za mu sa a bakinmu." Hindatu ta runtse idanu sannan ta budesu cikin karfin hali ta dubi mai gidanta ta ce. "Kada ka damu je ka gani, Allah baka sa'a." Cikin sauri na ban mamaki idan aka yi la'akari da rama da kuma bakar wahalar dake jikinsa mutumin ya nufi kofar gidan kai tsaye kirjinsa na harbawa. Har sa'ar da ya kai ga tangamemiyar kofar me kamar kofar gari bai ga motsin ko da halitta daya ba a duk tsawon kwararo sai wasu karnuka guda uku dake can karshen kwararon suna ta faman haushin babu gaira babu dalilin kamar sun yi ido biyu da aljan. Mutumin ya matsa kusa da kofar ya tsaya cikin shakka, domin bai san abin da ya kamata ya yi ba Shin buga kofar zai yi ko kuwa sallama zai yi. To idan ma ya yi sallama wa zai ji shi? Ya tambayi kansa. Yana nan tsaye cikinsa na kugi kamar tukunyar talge, sai ya ji kamar dagacan sashen hagu na katuwar kofar ana tabata. Mutumin ya yi sauri ya dan ja da baya lokaci guda kuma ya dubi bangaren hagu na jikin kofar. A lokacin ne to ya fahimci ashe a jikin katuwar kofar akwai wata yar karamar kofa daga hannun hagu wacce akalla mutum guda zai iya wucewa ta ciki, wannan yar karamar kofa ita ce ake motsawa ba a ko dade ba sai ta bude. Wani dan matashin yaro fari kyakkyawa ma'abocin kyawun sutura da cikar hallita ya fito daga cikin gidan sannan ya kurawa dogon mutumin idanu baya ko kiftawa. Dogon mutumin ya dubi yaron, sai ya rasa ma me zai ce masa. Domin da ido mutum na iya tsammanin dan saurayin yaron ya kai shekara goma sha uku ko sha hudu, to amma a gaskiyar al'amari yaron shekarunsa goma cif-cif da kwana biyu, domin shekaran jiya-jiya din nan aka yi bikin cikar shekarunsa goma da haihuwa. "Sannu Malam." Yaron ya ce da mutumin cikin ladabi. "Yauwa dana, sannunka dai." Ya dan yi shiru sannan sai ya dubi yaron ya ce. "Da Allah dan samari idan da hali taimakon abinci nake nema duk kankantarsa, wallahi mu baki ne bamu san kowa ba, ga matata can kwance akan titi, yunwa ce ta hanata tafiya" Yaron ya dubi mutumin na dan tsawon lokaci, a zuciyarsa yana tunanin ja da baya a guje ya rufe gida domin me yiwuwa mutumin nan dake tsaye a gabansa mahaukacine, dubi fa kayan dake jikinsa, koda yake dai irin kayan da yake gani ne jikin buzayen dake gadin gidansu, to amma shi wannan nasa sun ji jiki da yawa. "Ka ce abinci kake so?" Yaron ya tambaya. Mutumin ya gyada masa kai sannan ya dada da cewa. "Ko da kadan ne wanda zan bawa matata da Allah a taimaka min, so nake na bata ta dan ci mu yi gaba" Yaron ya daga kai ya dubi hadarin da ya mamaye sararin samaniya, sannan sai ya dubi mutumin cikin tausayi ya ce. "Ina zuwa" Cikin sauri ya shiga cikin gida. Ba a dade ba sai ga yaron tare da masu gadin gidansu mutum uku biyu buzaye daya tsohon soja, hakanan kuma da wani mutum dogo kakkaura wankan tarwada sanye da babbar riga amma
Chapter 10 · 0% Book details