Sashe 20
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ta yi rubutu akan tafin hannunsa sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta, ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin ta nufi dakin mahaifiyar Abdulmalik domin ta fasa kwai. Abdulmalik ya bude idanu a daidai lokacin da Ummi ta fice daga dakin kana ya dubi tafin hannunsa sai ya ga Ummi ta rubuta YAYANA MIJINA ! . Sidi mai jaka ya ja doguwar hamma ya kuma karawa sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya ce "Nas na fa gaji." Na dube shi cikin kasuwa na ce "Ka da dai ka ce min karshen labarin kenan?" Sidi mai jaka ya girgiza kai ya ce "Ba karshensa ba kenan amma saura dan kadan saurara na karasa maka sai mu watse" Na ce to, Sidi mai jaka ya dube ni kana ya ci gaba. Washe garin ranar karfe takwas daidai dan kabu-kabu ya sauke Anas a kofar gidan su Ummi idanunsa sai zubar da ruwa suke kamar tsohon kuturu domin rabonsa da ya hau kabu-kabu tun kafin satin da zai hadu da Mabruka Anas ya aika yaro zuciyarsa cike da farin ciki duk kuwa da sauyin rayuwa da ya same shi na gaggawa cikin sa'a ashirin da hudu kacal A daren jiya bai yi barci ba duk kuwa da cewa a dakin otal ya kwana amma dakin bai kai ko da rabin dakin kwanansu da Mabruka ba * A can cikin gida Ummi ta dubi Abdulmalik ta ce. "Mutumin ka ne, don Allah zo mu je ka labe daga bakin kofa ka ji yadda za mu kare da shi." Cikin murmushi Abdulmalik ya dube ta ya ce. "A'a, kada mu koma kamar yara kanana mana, ke dai je ki ku gama da shi ina nan." Ummi ta dube shi da dariyar zolaya ta ce. "Kai dai tsoro ka ke kada su Mama su ganmu tare, to mene ne kuma bayan sun san komai." "Sun san me?" Abdulmalik ya tambaya a tsora ce. "Takardun da ka rubuta suna gurin mama..." Ta fashe da dariya, da haka ta fice ta bar shi anan baki bude. Anas ya ji wani farin ciki marar misaltuwa ya lullube shi, sa'ar da ya hango kyakkyawar fuskar Ummi ta leka kofar gidan cikin sauri ya tareta da faffadan murmushi. "Hajiya Ummita." Ummi ta dube shi shekeke ta ce. "Ranka ya dade...yau a kasa ka zo ina motar?" Anan ne to Anas ya gama karkade dan sauran abin da ya rage na kaunarsa dake zuciyarta. "Wannan marar mutuncin gurguwarce ta kwace motar...kin san fa mun rabu da ita jiya da daddare saboda ke." Ummi ta dube shi cikin takaici ta ce "Kana nufin ka saki Mabaruka?" Anas ya gyada kai "Mene ne to amfanin zama da nacacciya. Matar da za ta hanaka walawa." Ummi ta kura masa idanu, yanzu kam ta tabbata duk abin da Hasiya ta fada akan wannan saurayi mai kyawun dan maciji gaskiya ne. Ummi ta dubeshi ido da ido ta ce. "Amma bai kamata ba ace ka saki Mabruka, dubi fa son da na ga tana yi maka Anas yanzu kai ko tausayinta ba ka ji?" Anas ya fashe da tattausar dariyar da ya sha satar zuciyar yan mata da ita ya ce. "Don me zan tausaya mata bayan tana son ta raba ni da ke." Ummi ta sake dubansa ta ce "Anas, wai me ya sa ka ke kaunata?" "Saboda kina da masifar kyau Ummi, ko ke ba kya ganin kanki ne." "Shi kenan abin da ya sa ka ke kaunata?" Anas ya gyada kai sannan ya dube ta ya ce "Ke fa me ya sa ki ke kaunata?" Ummi ta dube shi na tsawon lokaci kana sai ta dauke kai gefe guda ta ce "A da dai saboda kana burge ni ne kawai idan na dubeka shi yasa nake sonka." Anas ya dubeta cikin mamaki ya ce "A yanzu fa?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Ka daina burge ni Anas, kai bari in fada maka ma infact na tsaneka domin ka fiye son kanka." Anas ya ji wani abu kamar tafasasshen ruwa ya fara wanke masa fuska. "Ummi in wasa ne wannan ki ke yi dan Allah ki bari Ummi domin yana iya sa ni hauhawar jini." Ummi ta girgiza kai ta ce "Ban taba yin wasa da kai ba, wadanda suka sha wasan da kai dai sun yi, irin su wadannan." Ta zaro hoton da Hasiya ta ba ta, ta mika masa. Anas ya karba hannu na rawa, nan da nan sai ya ji kwalla na kokarin kwace masa. "Haba Ummi, yanzu wannan yar iska ce za ta rabani da ke'" Ummi ta kuma girgiza kai ta ce "Ka da ka sake daukar alhakin baiwar Allah wanda ka dauka a da ma ya ishe ka wallahi babu ruwanta a cikin wannan zance." Anas ya yaga hoton dake hannunsa gida biyu a fusace yace. "To idan ba ita ba ce me ya sa za ki ce kin tsaneni Ummi? Me ya sa! Na dauka ke ki ka rubuto min a takarda kina kaunata ??"TSOHON ALKAWARI-19