Sashe 14
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
don Anas ya tabbata sai dai ya zabi tsakanin mummunan aski da sa kai a wuta, domin muddin ya ci gaba da mu'amula da Ummi, rabuwarsa da Mabaruka ta zo kenan, shi ko ya san a yanzu koma me yiwuwa har abada Mabaruka ita ce babbar rumfar da ta rufe kansa da inuwa ta yi masa katanga da zafin ranar talauci. Wadannan abubuwa guda uku su suka hadu suka cunkushe zuciyar Anas, don haka yana nan bandakin yana maimaita karatun wasikar Ummi har sai da ya karanta ta sau kusan talatin. Bai tashi komawa dakin kwanan su ba sai da ya tabbata a lokacin Mabaruka ta gama fushinta ta yi barci. Anas ya nufi dakin kwanansu cikin sanda, a lokacin kusan biyu da rabi ne na dare. Ko kusa ko alama baya son ya sami Mabaruka ido biyu bata yi barci ba, domin Anas ya gama gajiya da ita, kai hatta muryarta baya son ji. Murya daya ce kawai ke yawo cikin kwakwalwarsa muryar Ummi. Anas ya yi boyayyiyar ajiyar zuciya sa'ar da ya tura dakin kwanan nasu ya shiga. Domin ya ga a cikin duhu yake. Tabbas ta yi barci, Anas ya ce cikin zuciyarsa Sannu a hankali ya sauya kayan dake jikinsa sannan ya lallaba ya haye bisa gadon ba tare da ya yi wani kwakkwaran motsi ba ya kwanta haka nan bai ma yarda koda jikinsa ya taba jikinta ba Anas ya yi lamo kamar ya mutu gashi dai baya ko motsi amma idanunsa a bude yake garau Zuciyarsa dauke da hoton kyakkyawar surar Ummi Yana nan kwance zuciyarsa fari fat lokaci guda kuma yana tunanin hanyar da zai bi a gobe ya gujewa Mabaruka domin ya sami damar ganawa da Ummi Anas na nan cikin wannan haki can sai ya ji agogo ya buga karfe daya sannan ne fa ya ji abin da yasa gashin jikinsa mimmikewa tsaye "Anas." Muryar Mabaruka ta ratsa duhun dake dakin ta daki dodon kunnensa. Anas ya zabura cikin kaduwa Bai taba tsammanin Mabaruka ba barci take yi ba. "Mab...Mabaruka ...dama ba barci ki ke yi ba." Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a sanyaye cikin karayar zuciya. "Ya zan iya barci Anas bayan kana fushi dani." Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi.TSOHON ALKAWARI-13 . "Ya zan iya barci Anas, bayan kana fushi dani." Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi. Don haka sai ya yi karfin hali ya ce. "Ki yi hakuri Mabaruka...wann an duk wani al'amari ne na rudin shaidan." Ga mamakin Anas sai ya ji Mabaruka ta yi wani irin nannauyan ajiyar zuciya, sannan sai ta juyo shi ta rungume shi ta kankameshi ta ce. "Ka yafe min Anas, ka kuma manta da duk abubuwan da na fada ma na bakaken maganganu, wallahi masifar kaunarka da kishinka ne suka sani..." Ta yi shiru tana numfashi sama-sama daga nan bata kara cewa komai ba, a haka barci ya dauke ta hannayenta kankame da jikin Anas babban masoyinta a duniya. Shi ko Anas, yadda ya ga rana haka ya ga dare bai runtsa ba. Ga dai Mabaruka rungume da shi cikin shaukin bege, amma shi ji yake yi kamar a rungume yake da kaya. Washe gari da safe suna karin kumallo sai Anas ya fuskanci duk da yake dai ba cikin fushi Mabaruka ta tashi ba amma babu alamar walwala sosai a fuskarta haka nan da kyar ta kai abinci sau biyu bakinta. Ka bi ta a hankali dan samari wannan gurguwa ita ce babbar inuwar rayuwar ka Wata zuciya ce ke baiwa Anas Shawara Wata zuciya ce ke baiwa Anas shawara. Anas, ya mike tsam daga inda ya ke ya koma kusa da Mabaruka ya zauna, sannan ya dauki yan siraran hannayenta ya rikesu a tausashe ya sa alamun damuwa na karya a fuskarsa, sannan sai ya matsa da bakinsa kusa da kunnen ta ya ce. "Mabaruka...me ke damunki ne, na ga duk kamar ba kya cikin walwala, ko har yanzu fushin ki ke yi dani? Ba na nemi afuwar ki yafe min ba?" Mabaruka ta langabe kai duk da yake dai bata yi masa murmushi ba, to amma fuskarta ta nuna alamun jin dadin tarairayar da ya yi mata. "Anas, wallahi zuciyata ce ke cikin fargaba." Anas ya dubeta cikin mamaki, sannan ya matse hannayenta a cikin nasa ya ce. "Fargabar me kuma, Mabaruka? Kina da kudi da duk wani jin dadin duniya da ki kebukata, tun da dai Allah ya hore miki dukiya, haka nan kuma kina da ni, ga ni kusa da ke, to mene ne kuma na fargaba?" Mabaruka ta dago kanta ta dubi Anas cikin mamaki ta ce a sanyaye. "Ina da kai fa ka ce?" Anas ya gyada kai ya ce. "Kwarai kuwa kina da ni, ni ba mijinki ba ne?" Mabaruka ta dan lumshe idanu sannan sai ta bude su ta dubi Anas. "Ka ga ni kuwa fargabar da nake yi gani nake yi kamar kwace min kai za a yi, rabuwarmu ta zo." A wannan dan takin lokacin da take kalamin sai Anas ya ji tausayinta ya sake kama shi a karo na biyu. Tabbas ya san batunta gaskiya ne, domin tuni ma in dai batun soyayya ne an riga an raba su, abinda ya rage tsakaninsa da ita a yanzu shi ne auren kaddara. "Ka da ki ce haka Mabaruka, bai kamata ba irin wadannan kalamai marasa dadi suna fitowa daga bakin ki." Anas ya dauke kai gefe guda fuskarsa cikin damuwa. Da ace za ka ga fusakarsa a lokacin, mutum sai ya rantse da Allah cewa abin da yake fada har zuciyarsa haka nan yake. Mabaruka ta yi wata kwakkwarar ajiyar zuciya ta dubi Anas. "Ba ni lemo na sha." Anas ya mike cikin sauri ya tsiyayo mata tacaccan lemo cikin kofin alfarma sannan ya zauna kusa da ita kana ya dan janyota jikinsa ya kara mata kofin a bakinta Cikin farin ciki mara misaltuwa Mabaruka ta fara shan lemon kadan-kadan har sai da ta shanye gaba daya. Abin ya baiwa Anas mamaki domin bai taba ganin ta yi haka ba. Amma ga Mabaruka hakan da ta yi akwai dalili mai karfi dalilin kuwa shi ne rabon da Anas ya yi mata irin wannan tarairaya tun daren amarcinsu na farko "Lemon ya ishe ki ko na karo miki?" Anas ya tambayi Mabaruka a tausashe Mabaruka ta dubeshi da murmushi a karo na farko ta girgiza kai "Ya ishe ni." Ta dan yi shiru sannan sai ta ce "Ina ma ace kullum haka muke da na fi kowa farin ciki a duniya" Anas ya sunkuyar da kai gami da murmushin yake shi kansa kunyar hada ido yake yi da ita domin a zuciyarsa cewa yake yi ina ma wannan tarairayar da yake yiwa Mabaruka ace Ummi ce Abin da Mabaruka ba ta sani ba shi ne duk wannan tarairaya da Anas ke yi mata kokari yake yi ya sami hanyar da zai bi ya sulle ya ziyarci Ummi "Daga yanzu zan manne ma kamar cingam duk inda za ni muna tare." Kalaman Mabaruka suka fado zuciyarsa Anas ya ji gumi ya fara tsiyaya ta bayansa duk kuwa da cwa wayewar gari kenan kuma koda ma babu sanyin iskar safiya akwai na na'urar sanyaya daki. "Tunanin me ka ke yi Anas?" Mabaruka ta tambayeshi babu zato babu tsammani ashe duk abin da yake yi tana lura da fuskarsa Adaida lokacin ne to wata dankareriyar karya ta darsu a zuciyar Anas ya riga ya san ita ce damar sa ta karshe ta samun damar zuwa gurin Ummi dan haka sai ya dubi Mabaruka ya ce a tausashe. "Kin san ina da abokai a cikin gari da yawa wadanda rabon da mu gana dasu tun kafin na aureki shi yasa ki ka ga na shiga cikin damuwa saboda ina fargabar kada su ga kamar dan na sami canjin rayuwa ne shi yasa na watsar da su." Mabaruka ta dan yi shiru na lokaci tana kallon kofin da ke gabanta. Zuciyar Anas ta fara harbawa da karfi, yana jiran ya ji abin da za ta ce, ya san idan ta ki amincewa bashi da damar ganin Ummi, haka nan kuma idan tare zasu fita nan ma bashi da damar zuwa gurin Ummi kenan. Tsawon lokaci, sannan Mabaruka ta dubeshi a tausashe ta ce cikin murmushi. "Kuma ka ki ka sanar dani tun dadewa ko tsorona ka ke ji?" Ta dan fashe da dariya. Jin haka shi ya sa Anas ya washe baki har kunne, zuciyarsa kamar ta fasa kirjinsa saboda doki. Anas ya dada rungumo Mabaruka. "Ya ya zan ji tsoron matata?" Wannan abu da ya fada shi ya kara narkar wa da Mabaruka zuciya, cikin sauri ta dubi Anas. "Yaushe za ka je ku gaggaisa da abokan naka?" Anas ya yi sauri har zai ce yau, sai wata zuciya ta ce dashi bi a hankali Anas, wannan nannadaddiyar matar ta fi ka wayewa. "Duk lokacin da ki ka ce Mabaruka haka za a yi, in ma kina ganin za ki iya jure shiga gargada da kwari da tudu irin na unguwanninmu na yan Allah baku mu samu sai mu tafi tare ki rakani, domin ba na son rabuwa da ke." Mabaruka ta dage kai cikin murmushi, sannan ta girgiza kai ta ce. "A'a ni ba zan iya shiga gargada ba, kana ganin ma so nake yi mu tafi london hutu, amma rashin doguwar tafiya a jirgi ya hanani" Ta dan yi shiru. Zuciyar Anas sai harbawa take yi yana jiran ya ji abin da za ta ce. "Anas." Ta kira sunansa a sanyaye. "Na'am, Mabaruka." Anas ya amsa cikin kwararren murmushinsa na mayaudara. Mabaruka ta ce. "Idan ka tafi kamar karfe hudu na yamma sai yaushe za ka dawo?" Anas ya dan yi jim sannan sai ya dube ta, ya ce. "In ba dan abokan nawa suna da yawa ba da sai in ce dake karfe takwas ma ina gida, to amma me yiwuwa na kai har wajen tara." Ya dubeta ido da ido. "Babu damuwa?" Mabaruka ta kama hannunsa cikin farin ciki ta gyada kai ta ce. "Na kara ma awa daya, amma kada ka wuce karfe goma, domin ko ruwa ba zan sha ba sai ka zo