Sashe 15
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka ba ni." Ta dan yi shiru tana duban Anas, suka yiwa juna murmushi. "Idan za ka fita sai ka dauki motata shudiyar lexus din nan, kada abokan ka su raina min kai!" *** Sidi mai jaka ya dubeni babu ko saurarawa ya ce. A can gidan su Ummi, Abdulmalik ya tsinci kansa cikin damuwar da bai taba shiga irinta ba, domin kwanansa guda cur) babu dare ba rana, yana ta faman rubutu ne. Na dubi Sidi mai jaka cikin mamaki. "Rubutun me kuma?" Sidi mai jaka ya ce. "Saurareni da kyau ka ji dalili." Ka ga Nas, tun ranar da Ummi ta halarci liyafar gidan Mabaruka, inda ta baiwa Anas yar rubutacciyar wasika, tana komawa gida sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin dan uwanta Abdulmalik. "Yaya Abdulmalik." Ta kira sunansa tun daga kofar dakin cikin doki da farin ciki. Abdulmalik ya dago kai cikin damuwa ya dubi kyakkyawar fusakarta domin ya san labarin da ta zo dashi ba zai taba faranta masa ba. Daman tun da yamma kafin ta tafi sai da ta sameshi ta ce. "Yaya Abdulamalik...M abaruka ta gayyace ni liyafa a gidanta." Abdulmalik ya boye kunar zuciyarsa ya dubeta da murmushin da bai kai zuci ba. "Ki ce yau kin sami damar ganin mutumin na ki." Ummi ta sunkuyar da kai. "Uhm, shi da ma yake da mata, ni na san ma ai zai yi wuya in zai kulani." Abdulmalik ya ji zuciyarsa kamar za ta fashe. "Namiji ai na mace hudu ne." Ummi ta gyada kai ta ce. "Yanzu yaya Abdulmalik idan mun hadu da shi ya ya zan yi?" Abdulmalik ya dube ta ya ce. "Duk da yake dai nima ba sanin irin al'amuran soyayyar nan na yi sosai ba, to amma ina ganin tunda dai ke mace ce, ba za ki rasa dabarar da za ki bi ba wajen nuna masa cewa kina kaunarsa. Sai dai kuma ki bi a hankali kada babbar kawarki ta kamaki kina kokarin sace mata miji." Suka fashe da dariya, A haka suka rabu. Wannan shi ya sa lokacin da ta dawo sai ta shiga dakin cikin farin ciki ta zayyanawa Abdulmalik duk abin da ya gudana tsakaninta da Anas "Yaya Abdul kana jin zai zo gobe din kuwa?" Abdulmalik ya ji murmushinsa ya fara daukewa "Me zai hana, tun da dai idan aka yi la'akari da abin da ki ka ce shima ashe ya dade yana kaunar ki" Ummi ta yi tsalle a tsakar dakin ta dire cikin farin ciki ta ce. "Wallahi Yaya Abdul ba ka ga yadda na ruda shi ba jikinsa har rawa yake yi" Abdulmalik ya cije baki sannan ya dage kai. Ummi ta daina tsallen da take yi ta dube shi cikin damuwa. "Yaya Abdul...ba ka da lafiya ne na ga kana cije baki?" Abdulmalik ya dubeta. "Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe" Ummi ta dube shi cikin.TSOHON ALKAWARI-14 . "Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe" Ummi ta dube shi cikin damuwa. "Bari in dauko ma magani" Abdulmalik ya yi sauri ya girgiza kai. Sannan ya yi mika. "Ina tsammanin gajiya ce ta yi min yawa, na san idan na sami isasshen barci zan warware zuwa safe" Ummi ta kura masa idanu cikin damuwa na tsawon lokaci. "Bari to na tafi na barka ka huta, domin zuwa na yi mu yi bankwana, na kuma fada ma cewa gobe ne da daddare muka yi dashi zai zo...in dai zai zo din" Ta mike tsaye. Abdulmalik ya dubi kyakkyawar fuskarta. "Ina taya ki fatan alheri Allah ya sa ya zo din" Ummi ta yi murmushi ta ce. "Ameen Yaya Abdul, Allah ya karbi addu'arka, wallahi yau da kyar zan yi barci" "Ai ba ke kadai ba" Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa. "Sai da safe Yaya Abdulmalik." Ummi ta ce da faffadan murmushi. Sannan sai ta fice daga dakin. Tana fita sai Abdulmalik ya kifa kai akan cinyarsa, ga mamakinsa sai ya ji wani zazzafan hawaye ya fara kwaranya akan fuskarsa. Yana nan zaune har karfe biyun dare ta gota barci bai samu ba, domin Abdulmalik ya riga ya san cewa idan ya yi lako-lako yana ji yana gani kwado zai leko daga tafki ya yi masa kafa ya koma. Tabbas idan ya yi wasa yana ji yana gani Ummi, abin da ya fi kauna fiye da komai a duniya za ta sulale ta tsakanin yan yatsun ikonsa. A lokacin ne to dabarar ta fado zuciyar Abdulmalik. A kullum zuciyarsa kan fada masa cewa hanya daya ce kawai zai bi ya magance wannan bala'i dake kokarin afka masa. Ita ce ya kira Ummi ya yi mata bayanin cewa ita fa ba yar uwarsa ba ce ta jini, ya kuma yi mata bayanin irin yadda ta shige zuciyarsa. To amma kashedin mahaifinsa shi ke taka masa birki. Wata zuciyar ta kan ce dashi me zai hana ka sanar da mahaifiyarka halin da ake ciki. Kunya ba za ta bari ba. Ita ce amsar da Abdulmalik ke fadawa zuciyar tasa. Yana cikin hakan ne to ya kasa barci, kawai sai dabara ta fado masa Abdulmalik ya dauko littafin rubutu, mai shafi dari da sittin, ya dauki biro ya fara rubuta labarin tun farkon haduwarsa da marigayi Saifullahi mahaifin Ummi. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi "Nas, wannan labari da Abdulmalik ya rubuta shi ne sanadiyyar duk wani labari da nake baka a halin yanzu." "Kamar ya ya kenan, ban fahimce ka ba Baba Sidi?" Na ce dashi. Sidi mai jaka ya ce. "Za ka fahimce ni ne, amma sai nan gaba, kai dai rabu dani na karasa labarin nan, na ga magriba ta karaso, bana son labarin nan ya kaimu har bayan isha." ya dauki tubani ya jefa a baki sannan ya ci gaba. Washe gari tun kafin magariba Ummi ta shiga wanka, ba ita ta fito ba sai karfe shida da rabi. Bayan ta yi sallah sai ta shiga kwalliya, sai da ta shafe sa'a guda tana kwalliya. Bayan ta gama shafe-shafe da feshe- feshen turare, sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin Abdulmalik domin tun da safe suka yi dashi cewa shi ne zai rakata hirar, domin Ummi ta ce dashi ba ta son a san alakar a cikin gida har sai Anas ya zo a kalla sau uku. "Har kin shirya kenan?" Abdulmalik ya dubeta cikin karaya. Ummi ta yi murmushi ta dubeshi ta ce. "Dubanni da kyau Yaya Abdul...dan Allah na yi kyau? Idan ban yi ba fada min na yi sauri na sake shiga kada ya zo ban gama shiryawa ba." Abdulmalik ya kurawa kyakkyawar halittar idanu. Ba wai yana kallon Ummi bane don ya ba ta amsar tambayar da ta yi masa ba, yana kallonta ne da idanun bege da tsananin shaukin ina ma ace shi ya mallake zuciyar ta baki daya. Kai wannan Anas da sa'a yake a duniya. Abin da ya fi damun Abdulmalik da kuma bashi mamaki shi ne, wai shin shi wannan Anas din kamar ya ya yake, wane irin kyawun siffa ce dashi, ko kuma Ilimi, ko kuma dadin baki, da har wannan kyakkyawar ta mace da tsananin kaunarsa. "Ya ya ka ganni Abdulmalik, na yi kyau?" Zazzakar muryar Ummi ta sake ratsa kunnen Abdulmalik. Ya yi ajiyar zuciya ya ce. "Kin yi kyau wallahi sosai ma kuwa." Ummi ta yi tsalle cikin murna ta ce. "Har na ji dadi wallahi, tashi to mu tafi." Abdulmalik ya mike tsaye da kyar kamar ya hadiyi tabarya sannan ya ce. "Idan momi ta tambaye kin inda za mu ki ce da ita kanti zamu je siyayya." *** Karfe takwas saura kwata na yamma Anas ya shigo titin a cikin katuwar motar shudiya kirar Lexus yana tafe yana bin wakar kidan turawa abinsa cikin farin ciki da wannan rana. Tun da ya auri Mabaruka bai taba samun yanci irin na wannan rana ba. Ga shi dai daman tun ranar da ya aureta ya yi tsalle ya fice daga kurkukun talauci ga motocin hawa sai wacce ya zaba ga sutura Kusan kullum sai ya sa sabon kaya na yamma daban na safe daban. Ga aljihunsa a cike taf da mikakkun takardun kudi na kashewa, amma duk a banza bai jin dadinsu ba don kome ba kuwa sai dan wannan nacacciyar gurguwa kamar yadda ya kirata, wacce ke manne da shi kullum kamar cingam. Dan haka a yanzu da ya shigo cikin titin sai ya dubi kujerar motar dake hannun damansa cikin farin ciki domin yau Allah ya raba shi da cingam, lokaci guda kuma sai ya dubi takardar da ke hannunsa na dama, yayin da hannunsa na hagun kuma yake sarrafa matukin motar. Tabbas titin ne. Anas ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya dada kallon takardar kwatancen da Ummi ta bashi, kana ya sake dago kai yana nazarin jerin gidajen dake gurin yana kokarin hangen mai lamba ashirin daga cikin su. A daidai lokacin ne to hasken fitilar motarsa ta hasko masa abin da ya sa yar autar hantar cikinsa kadawa. Sannan sai ya fara musu da zuciyarsa, kai wannan ba ita ba ce, ya ce da kansa, sa'ar da ya hangi kyakkyawar hallitar tsaye a jikin katangar wani sabon gida da ba a gama ginin sa ba. Ita da wani saurayi ne kyakkyawa dogo fari mai dogon saje da dogon hanci mai doro daga tsakiya sai ka ce hancin Larabawa. Anas ya ji wani bakin kishi ya turnuke zuciyarsa sa'ar da ya tabbata lallai Ummi ce ba wata ba. Abin da ya fi bata masa rai shi ne saurayin da ke tsaye da ita shima kyakkyawa ne, duk da yake dai Anas bai ga alamun saurayin ya zo da mota ba, to amma a yanayinsa babu alamar talauci ko kankani a jikinsa. Sannu a hankali ya ja birki ya tsaya a daf da su kana sai ya rage hasken fitilar motar kadan ya dada nazarin fuskar Ummi. Abin ya bashi mamaki, domin ya lura da cewa sun juyo inda yake, sun zubawa motar idanu. Sidi mai jaka ya yi shiru, kana ya sheka wata uwar hamma ya dubeni a yatsine ya ce. "wato Nas, tubani na da dadi, amma tsiyata da shi saurin sa mutum barci, ga shi da sa cikin mutum ya yi nauyi wata sa'ar sai