Sashe 16
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
in ji kamar na hadiyi duwatsu." "Dan ma ka saba cin sa." Na ce dashi a kagauce domin na matsu na ji yadda za a yi. Sidi mai jaka ya dafa cikinsa da busassun yan yatsunsa gami da dan runtse, idanu sannan sai ya dubeni ya ce. "Sannu a hankali Nas, Anas ya tuko motar zuwa inda suke ya tsaya, lokaci guda kuma ya sauke gilasan motar. Cikin sauri Ummi ta nufo gindin tagar motar, Abdulmalik na biye da ita a baya, a lokaci guda kuma ya ji wani matsanancin bakin ciki ya lullube shi Na shiga uku ya ce a cikin zuciyar sa, Ashe Anas din shima kyakkyawa ne." "Anas..." Mabaruka ta kira sunansa a kunya ce. "Ummi..." Shima ya kira sunanta, sai dai har yanzu zuciyarsa na bugawa domin bai fahimci matsayin saurayin dake biye da ita a baya ba. Ummi ta lura tun da ta zo gurin idanun Anas akan Abdulmalik suke don haka sai ta yi sauri ta dube shi ta ce. "Anas...ga Yayana Abdulmalik ba ku gaisa ba." Sannan sai ta juya ta dubi Abdulmalik da faffadan murmushi ta ce. "Yaya Abdul...ga Anas dina da nake baka labari yau dai Allah ya hada ku." Cikin sauri gami da ajiyar zuciyar jin dadi abin da ta ce, Anas ya bude kofar motar ya fito, sannan ya mikawa Abdulmalik hann. "Yaya barka da yamma." Samarin biyu suka cafke hannun juna, kana suka dubi juna ido da ido, Abdulmalik ya riga ya san matsayin Anas a gurin Ummi, to sai dai shi Anas bai san matsayin Abdulmalik ba a gurin Ummi, duk da yake dai ta ce dashi wai Yayanta ne, akwai wani abu a yanayin fuskar Abdulmalik da ya jefa shakka cikin zuciyar Anas, tabbas abin ya jefa shi cikin kaduwa, domin irin yanayin da yake gani a fuskar Abdulmalik, ya sha ganinsa a fuskokin gomomin samarin da ya sha kwace musu yan mata a baya, to amma da yake a yanzu bashi da wata kwakkwarar hujja abar dogaro, sai ya dubi Abdulmalik ya kuma cewa. "Ya ya ayyuka...ko kuma ya ya karatu zan ce..." "To, karatun dai...ai har yanzu yayan naka dalibi ne." Abdulmalik ya ce a karo na farko. Aka sake yin shiru na yan mintuna, Ummi na kallon Anas, shi kuma na kallon Abdulmalik, Ummi ce ta fara bata shirun. "Yaya...Abdulma lik yau dai Allah ya hadaku da Anas din da nake baka labari." Ba na fatan na kara haduwa da shi. Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya ce a fili. "Malam...Anas, ta sha bani labarin ka...ga shi sai yau Allah ya hadamu." Ya dan yi shiru yana duban Ummi kana sai ya ce. "Daman zuwa na yi mu gaisa da wanda kanwata ke so...ni zan koma, gara na barku ku dan zanta." Yana gama fadin haka sai ya fara juyawa da baya. Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta.TSOHON ALKAWARI-15 . Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta. Yaya Abdulmalik jininsa bai hadu da na Anas ba. Ta kuma fadi cikin zuciyarta, sannan sai ta ce a fili. "Yaya Abdulmalik...ta fiya za ka yi tun yanzu?" "Eh mana, ai gara na ba ku waje ku yi hirar ku...na sa kannena a gaba?" Ya fadi gami da jeho wani takurarren murmushi. To sai dai kuma ba Anas ba wanda tuni daman ya gama fahimtar Abdulmalik, hatta Ummi ta gane cewa murmushin yake ne tabbas ta san yayanta yana cikin damuwa. "Sai an jimanku..." Abdulmalik ya kuma fada sannan cikin sauri ya juya ya nufi gidan su. Suka zuba masa idanu har sai da ya shige cikin gidan ba a samu wanda ya ce kala ba. Ummi ta yi ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar da fuskarta akan kirjinta cikin yar damuwa. "Ya ku ke da shi?" Anas ya tambayi Ummi yana dubanta cikin zargi, wani bakin kishi na kokarin tsaga masa zuciya. "Yayana ne." Ummi ta bashi amsa kai tsaye lokaci guda kuma ta kalleshi ido da ido. Anas ya dubi fuskarta na tsawon lokaci yana nazari a cikin duhun daren, abin ya bashi mamaki domin a yadda ya ga tana kallonsa da karya take yi ba za ta taba iya hada idanu da shi ba. To amma me ya sa kyakkyawan saurayin mai hancin larabawa yake irin wannan dabi'a haka kamar wanda yake tsakiyar kogin begen Ummi? Tambayar kenan da Anas ya kasa amsawa kansa. "Kina nufin yayanki na uwa daya uba daya ko kuwa dai kawai yaya ne na yan uwa." A wannan karon Ummi ce ta dube shi da wani tattausan murmushi ta ce. "Oh...Anas kenan, lallai na fahimci kai ma kana da kishi kamata." Ta dan yi shiru lokaci guda kuma ta dafa kofar motar dake bude da hannunta na hagun ta dubi Anas ta ce. "Ka da ka bari kishi ya hana mana jin dadin hirarmu ta farko da kai." Cikin sauri Anas ya sassauta fuskarsa duk kuwa da cewa har yanzu zuciyarsa tafasa take yi. "Ki gafarce ni Ummi, masifar sonki ce ta yi min yawa a cikin zuciya, irin yadda nake kaunar ki ko kuda ya sauka a kanki sai na yi kishi da shi...to ballantana kuma wannan kyakkyawa da ki ka ce wai yayanki ne." Ummi ta fashe da wata zazzakar dariya, wacce sautinta ya sa wasu yan gajerun samar dake can gefe guda suna jiran fitowar tasu budurwar suka juyo cikin sauri suka kalli bangaren da su Ummi da Anas suke. "Kai Rabe...ka ji wata cika tana dariya kamar ana busa sarewa." "Ummi kenan." Daya saurayin ya ce da abokin sa "Duk unguwar nan babu cikar da ta kai haduwar ta, ba ka ganin gashinta daga nan har sheki yakeyi kamar madubi, to don ma da daddare ne da rana ce in ka kalli gashin kanta sai ya dauke maka idanu." "Allah mutumi na...to ko barin wannan kucakar zamu yi mu koma can mu gwada sa'ar mu." Daya saurayin ne yake fadawa Rabe haka. "Rufawa kanka asiri." Rabe ya ce da saurayin. "Ummi me shegen girman kai kamar ibilishiya tun da nake ban taba ganinta da wani saurayi ba sai yau...kuma in ban da rigimarka ma ina kai ina Ummi? Zoben dake danyatsanta guda daya fa sai ya yi ma dinkin sallah karama da sallah babba har sau uku, kuma ya bar ka da ya canjin kashewa...samar i yan hutu ma masu kafafu hudu da iya kwalisa ba ta sauraresu ba sai kai mai katon kai da fadi kamar faranti." "Ka ga bana son iskancin banza...kai din kyau ne da kai ko dan ba ka kallon madubi." Saurayin ya ce da Rabe a kufule. A daidai lokacin da Rabe ya fara kokarin mayar da martani ne to, kofar wani gida ta bude sannan wata yar gajeriyar budurwa fara ta fito cikin sauri ta nufi inda su Rabe suke, ko da ta zo giftawa ta kusan inda su Ummi suke, sai ta tsaya turus ta Kalli Anas sama da kasa sannan ta dauke kai ta dubi Ummi ta ce. "Yaya Ummi ina wuni." "Lafiya kalau Hasiya...ya ya ki ke?" "Lafiya nake." Shiru Hasiya ta dan yi sannan sai ta sake duban Fuskar Anas ta ce. "Lalatacce mayaudari nan kuma ka dawo?" Anas ya ji gabansa ya fadi sannan zuciyarsa ta harzuka ya dubi budurwar a kidime yana kokarin tuna inda ya san ta. "Ai ba za ka iya tunani ba mayaudari tun da muna da yawa a gaban ka." Tana gama fadin haka sai ta juyo ta dubi Ummi ta ce. "Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada tarkon sa ba." Tana gama fadin haka sai ta juya gami da cewa. "Bari in je in fatattaki wadancan yan iskan...duk sahunsu guda da wannan da yake gabanki, kar ki yarda da shi mai kyan dan maciji ne."***** . Ummi ta yi sororo a rude tana kallon Anas yayin da shi kuma Anas ya dubeta a tsorace baki na rawa ya ce. "Ummi...wannan kuma wacce mahaukaciya ce?" Ummi ta yi ajiyar zuciya a kidime kana ta ce. "A iya sani na dai tana da hankali." Ta dan yi shiru, sannan sai ta dauke hannunta daga kan kofar motar. "Daman kun dade da sanin juna ne kai da ita?" Cikin sauri Anas ya girgiza kai "Ko kusa ko alama ni ban ma taba ganinta ba wallahi sai yau." Ga mamakinsa sai ya ga Ummi ta zunkuda kafada sannan ta haskake shi da murmushi ta ce. "Me yiwuwa wani ne mai kama da kai ya taba yaudarar ta na san halin Hasiya wani sa'in rudaddiya ce." "Yauwa ko da na ji fa" Anas ya ce gami da ajiyar zuciya, sannan ya share gumi lokaci guda kuma ya yi sauri ya sauya zancen da cewa. "Ummi wai don Allah uwa daya uba daya ki ke da Abdulmalik." "Ummi ta fashe da wata sassanyar dariyar jin dadin ganin Anas yana kishi a kanta. "Har yanzu dai ba ka yarda ba kenan." "A'a ba wai ban yarda ba ne...amma ni abin ne yake bani mamaki, ni sai na ga kamar shima sonki yake." Ummi ta girgiza kai ta ce. "Anas, wallahi yayana ne, uwa daya uba daya, ni dai abin da nake tunani me yiyuwa wani abu ne daban yake damunsa ko kuma ganin zai tafi ya bar ni ni kadai ka san tun muna kanana bama rabuwa tare muke duk inda zamu tafi yawan lokuta ma barci ne ke rabamu to ka san ban taba yin saurayi ba sai a kanka ina jin abin da yake damunsa kenan." Anas ya karkada yan makullayen dake hannunsa ya ce, "Na yarda da ke Ummi." Sannan sai ya hango inda su Hasiya da samarinta suke tsaye gabansa na faduwa, haka nan wani zazzafan gumi ya fara sartu akan doron wuyansa tabbas sai yanzu ya tuno ta. A daidai lokacin ne to ya dubi agogo sai ya ga ashe har goma na dare ta wuce. Sannan ne to ya ji gaba daya duniyar nan ta yi masa bakinkkirin. Mabaruka ce ta fado a ransa kwata-kwata ganin kyakkyawar fuskar Ummi ya gama mantar da shi komai