Sashe 13
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sake dawowa zuciyarsa dan haka sai ya dago kai ya dubi Ummi da Murmushi ya ce. "Ummi kenan. Ina za ki ne na ga kin caba kwalliya haka?" Ummi ta dube shi da murmushi sannan ta ce. "Ina zani, ko dai ina zamu, bikin taya murnar ranar haihuwar wata kawata zaka rakani." Abdulmalik ya dubeta cikin mamaki ya ce. "Kin manta ne cewa ina da jarrabawa ta karshe a makaranta, kin san ina bukatar karatu." Ummi ta yi sauri ta rufe fuska cikin dariya. "Oh! Dan Allah Yaya Abdulmalik ka yi hakuri, wallahi mantawa na yi ashe kana da jarrabawa gobe." Abdulmalik ya mike tsaye. "Mu je na raka ki sai na dawo." Ummi ta mike tsaye ta dube shi ta ce. "Wallahi nima dan muna bala'in mutunci ne da MABRUKA da ba zan je ba tun da kaima ba za ka ba." Abdulmalik ya yi murmushi. "Ai ba komai. Yaushe zaki dawo?" Ummi ta lumshe idanu ta dan daga kai sama. Abdulmalik ya kurawa wasu siraran zane guda uku da suka yiwa kyakkyawan wuyanta kawanya. "Nan da karfe tara na dare zamu dawo."*** . Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce ina fatan kana fuskantar inda labarin ya dosa da kyau? Na gyada kai cikin sauri. "Ina fuskanta." Sidi Mai Jaka ya ci gaba. A daren ranar da Ummi ta dawo daga walimar bikin zagayowar haihuwar Mabaruka ne to Abdulmalik ya fara ganin canjin yanayin karara a fuskar Ummi Karfe tara na dare da yan mintuna ta dawo, Abdulmalik ya ji shigowarta babban falo dan haka sai ya ji wani farin ciki ya lullubeshi domin tuntuni ya matsu da ya ga ta dawo domin baya iya yin sama da sa'a biyar bai ganta ba Wani sa'in ko a makaranta yake sai ya yi ta bugo mata waya duk bayan sa'a guda dan kawai ya ji muryarta Don haka sa'ar da ya ji motsin dawowar Ummi sai ya ajiye takardun bokon da yake karantawa ya lumshe idanu yana jiran shigowarta domin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru babu motsin UmmiTSOHON ALKAWARI-12 . Domin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru, babu motsin Ummi sannu a hankali har mintuna talatin suka shude bata shigo dakin ba. Abdulmalik ya mike tsaye cikin tsananin damuwa da mamaki domin a iya saninsa da Ummi ko kayan jikinta ba zata sauya ba sai ta zo gare shi su yiwa juna Sallama Cikin sauri Abdulmalik ya fita daga dakinsa ya ratsa ta falo ya nufi dakin Ummi. Abdulmalik ya dan kwankwasa kofar dakin a tausashe sannan sai ya yi sallama ya shiga. Ummi na kwance akan gado, sanye da kayan da ta fita da su walimar, ko cire su bata yi ba, ta kurawa saman dakin idanu bata ko kiftawa kamar mai kallon allon sinima. Abdulmalik ya tsaya cak a tsakiyar dakin kamar an dasa shi, ya kurawa Ummi idanu cikin tsananin mamaki da kaduwa domin ya fahimci ashe Ummi bata san ma ya shigo dakin ba. "Ummi..." Ya sake maimaitawa a karo na biyu kamar mai biya karatu. Ummi ta juyo firgigit ta tashi zaune akan gadon. Ta dubi Abdulmalik. "Tunanin me ki ke yi haka?" Ummi ta dubeshi da murmushi. "Ka yi hakuri don Allah Abdulmalik wallahi ban san ka shigo ba." Abdulmalik ya matsa kusa da ita ya zauna daga can nesa da ita a bakin gadon ya kura mata idanu. "Na ji shigowarki, ina ta jira ko za ki zo, ba ki zo ba shi ne na ce bari ni nazo da kaina na gani ko lafiya." Ummi ta sunkuyar da kai sannan ta yi ajiyar zuciya kana ta dago kai da murmushi ta dubi Abdulmalik ta ce. "Lafiya lau Yaya Abdulmalik bala'in gajiya na yi." Tun kafin ta gama fada Abdulmalik ya san karya take yi, domin alamun damuwar dake fusakarta tamkar bakin rubutu ne akan farar takarda. Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta sosu, bai ji dadin abin da ta fada ba, domi a duk iya tsayin zamani, tun ranar da aka haifeta ya fara daukarta, har zuwa yau bata taba fada masa karya ba sai yanzu. Abdulmalik ya dubi Ummi cikin shakka, ya girgiza kai ya ce. "Kada ki ce haka Ummi, ba gajiya ba ce kawai ke damunki akwai matsala ta daban." Ummi ta dubeshi da wani fatalwan murmushi akwai alamun kunya a fuskarta ta ce. "Gaskiya ne Abdulmalik wallahi akwai abin dake damuna, ka kuma yafe min dan Allah ka san ban taba yi ma karya ba sai yau..." Ta dan yi shiru tana murmushi sannan sai ta dada da cewa. "Yau din ma kunya ce wallahi ta sa ni yin karya." Abdulmalik ya yi ajiyar zuciya kana ya dubeta cikin shauki ya ce. "Na yafe miki Ummi...ai kin san duk laifukanki a gurina yafaffune har ma da wanda ba ki yi ba." Ummi ta yi dariya ta sake sunkuyar da kai Abdulmalik ya sake nazarin fuskar Ummi cikin damuwa ya ce. "Fada min sirrin dake zuciyar ki Ummi me ke damun ki ne?" Ummi ta dauke kai gefe guda na tsawon lokaci, haka nan a duk iya tsayin wannan lokaci akwai alamun murmushi-murmus hi da kuma damuwa-damuwa a fuskarta. Shi dai Abdulmalik ya kura mata idanu cikin mamaki bai tari numfashinta ba. Tsawon lokaci, sannan Ummi ta juya ta dubeshui, ta ce bakinta na rawa. "Yaya.....Abdul malik...wallahi irin abin da nake yawan karantawa ne a cikin littattafan labarai na Hausa ya faru a kaina." Abdulmalik ya ji gabansa ya fadi ras! Ya dubi Ummi. "Me ki ke nufi." Ummi ta dauke kai gefe guda a kunyace ba tare da ta hada idanu da shi ba ta ce. "Wallahi...wani na gani a gurin liyafar nan naga ya burge ni." Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta harba. "Har yanzu ban fahimce ki ba Ummi, waye wani, kuma ya burge ki kamar ya ya." Ummi ta sake dariya ta ce. "Yaya Abdulmalik ji na yi wallahi ina masifar kaunarsa a zuciyata, a yanzu din nan haka ji nake yi kamar mun dade da sanin juna." Ta dan yi shiru ganin Abdulmalik bai ce wani abu ba sai ta dada da cewa "Za ka yi mamaki idan na ce da kai Mabaruka ce kawai ta turani na yi kiransa." Abdulmalik ya dago kai ya dubeta da murmushin karfin hali, amma a badini tuni har zazzabi ya rufe shi "Ummi kenan. To yanzu ya ya za ki yi kenan? Kin ga mutum kin ce kina sonshi amma ba ki san ko wane ne shi ba ba ki san inda yake ba baki san ko da sunan shi ba." Ummi ta matso kusa da Abdulmalik ta ce "Ma'aikacin otal din da aka yi liyafar ne, na ji Mabaruka ta kira shi da suna ANAS!" Abdulmalik ya sunkuyar da kai Ummi ta dubeshi cikin damuwa. A tunaninta halin da ta tsinci kanta ciki ne ke damun Abdulmalik domin ta san irin yadda yayan nata Abdulmalik ke matukar sonta don haka sai ta ce dashi a tausashe "Ka da ka dami kanka Yaya Abdulmalik na san duk abin da ya shafe ni kai ya shafa. Ni dai abin da nake so shi ne ka tayani don Allah mu same shi ka ga kaunarsa" Ta dan yi shiru sannan sai ta dubi Abdulmalik ta ce "Kana jin kuwa zai iya kaunata?"*** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni da murmushi sannan ya dubi tubanin Tubanin dake gabansa cikin damuwa domin tuni ya hadiye sama da kashi uku bisa hudun tubanin A zuciya ta na ce kai wannan tsoho da cin tsiya yake domin na tabbata yawan tubanin da ya hadiya tun daga rana zuwa yanzu ya ishi katti goma su ci su koshi amma sai gashi shi kadai duk ya hadidiye su kamar rumbu "To Nas ka ga abin da nake fada maka tun farko ko? Sai da na ce da kai ni ne mai saka labari kamar injin saka, na hade ma shi guri guda, gashi kuwa sannu a hankali na nuna maka alakar zarurrukan labarin guda biyu." "Haka ne Baba Sidi." Na ce dashi Sidi mai jaka ya canko wani katon tubani mai kama da dankali ya gutsiri rabi, sauran ya fado a cikin kwanon Sidi mai jaka ya dubeni ya ce. "Nas, wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin, yanzu abin da ya rage shi ne na gaggauta na daura ma bakin zarurrukan labaran guda biyu kafin nan da sallar magariba, domin bana son labarin ya kai mu har bayan sallar magariba." Na yi sauri na gyada kai na ce. "Ni ma ai na fi son haka." Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. "To Nas, bari yanzu ne zan koma kan wancan tsohon zaren labarin da muka bari lokacin da zamu tafi sallar azuhur, inda mauka baro Anas yana karatun wasikar da Ummi ta bashi." Ya dubeni ido da ido. "Ka tuna da gurin?" Na gyada kai na ce. "Kwarai kuwa, ba inda ka ce har ma yana jiyo kukan matarsa Mabaruka ba daga cikin bandakin?" Sidi Mai jaka ya fashe da dariya yace. "Nas kenan, da ace yadda kake rike labari a kwakwalwarka haka nan kake rike karatu da ba karamin malami za a yi ba wata rana, to sai dai kuma na fahimci kamar kwakwalwarka ta fi iya rike labari fiye da komai." Nima sai na fashe da dariya, na ce. "Baba Sidi kena." Sidi mai jaka ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Nas, dauki zuciyarka cancakat ka mayar da ita cikin bandakin nan, inda muka baro Anas dazu yana karatun wasikar da Ummi ta bashi." "Na mayar." Na ce dashi. Yauwa Nas. Anas ya ci gaba da juya takardar a hannunsa, zuciyarsa dauke da abubuwa guda uku masu kama da kishiyar juna. Ka ga na farko dai akwai farin ciki, domin Anas bai san abin da zai iya kwatanta farin cikinsa da kalmar Ummi ba, inda tana kaunarsa da kanta. Na biyu akwai tsana mai tsanani cikin zuciyarsa, domin a yanzu duk duniya babu abin da ya tsana kamar matarsa Mabaruka. Domin tuni Anas ya riga ya san wannan mummunar gurguwa ita kadai ce katangar karfen dake tsakaninsa da babbar masoyiyarsa Ummi. Abu na uku kuwa dake dafe a zuciyar Anas shi ne tsananin fargaba,