← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kansa babu hula, ko shakka babu shi ne ya yi kama da mamalakin dankareren gida. Dogon mutumin dake tsaye, ya dubi mutumin a tsorace, domin ya tabbata kashinsa ya bushe a tsammaninsa kamashi zasu yi a matsayin barawo ko mahaukaci. Tun kafin su karaso gurin mutumin sai ya ji maigidan nan na cewa sauran masu gadin. "Wai wani mutum ne da matarsa anan kofar gidan suke neman taimakon abinci a gurin Abdulmalik shi ne na fito da kaina gara mu je mu gani ko wane irin mutum ne, duniyar nan yanzu ba abin yarda ba ce." Dogon mutumin ya zube gaban mai gidan ya gaida shi. Maigidan ya dubi dogon mutumin ya ce. "Malam kaine me neman taimakon abinci?" Mutumin ya gyada kai ya ce. "Ni ne ranka ya dade, wallahi zuwan mu kenan garin nan ni da matata, ga ta can a bayan yunwa ce ta kayar da ita ta kasa tafiya kuma tana da ciki wata uku, wannan shi ya takurani nake neman wannan abinci kafin Allah ya bani masauki, domin mu ba mutanen wannan kasa ba ne yaki ne ya koromu gudun hijira." Kalamin dogon mutumin ya karya zuciyar maigidan, nan da nan sai ya ji tausayinsa ya kamashi, musamman ma daya ji tare suke da matarsa kuma tana da ciki wata uku. Wannan shi ya fi tayar masa da hankali. Domin yau shekarunsa ashirin da yin aure, tun daya auro matarsa Hajiya Sa'adatu basu sami damar haihuwa ba sai bayan shekaru goma suka haifi Abdulmalik, tun daga kansa kuwa basu kara samun koda batan wata ba har zuwa wannan lokaci. "Yanzu ina matar taka take?" Dogon mutumin ya nuna can bayansa ya ce. "Ga ta can yallabai" Mai gidan ya dubi masu gadinsa guda uku ya ce. "Ku je dashi ku taho da matar, ku sameni a tsakar gida." Sannan sai ya kama hannun Abdulmalik suka shige farfajiyar gidan ma'abociyar shuke-shuken da kamshin furanni. Ba'a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da.TSOHON ALKAWARI-10 . Ba'a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da dogon mutumin da kuma matarsa Hindatu. Suna isowa sai mutumin da matar tasa suka zube gaban alhaji suka sake gaidashi. Mai gidan ya dubi tsohon sojan nan mai gadinsa ya ce. "A kaisu dakin nan na kusa da injin bada wuta su kwana a ciki yanzu zan sa a kawo musu abinci ina son kuma a lura dasu kaji ko?" Tsohon sojan ya rusuna ya ce "An gama alhaji" Sannan sai ya dubi dogon mutumin da matarsa ya ce. "Ku biyoni mu tafi." Ramammun mutanen guda biyu kyawawa suka bishi a baya, gami da godiya. Mai gidan ya bisu da kallo cikin tausayi yana tunanin abin da ya kamata ya yi domin taimakonsu. "Wallahi baba mutanen abin tausayi ne dubi matarsa da kyar take tafiya" Mutumin ya dubi dansa Abdulmalik ya gyada kai, bai ce komai ba. Sidi mai Jaka ya yi shiru sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ina fatan kana biye dani akan wannan dogon zaren labari" Na gyada kai cikin kaguwa na ce. "Ina biye da kai baba Sidi, sai dai kuma ni wannan labarin duk jinsa na ke yi kamar sabo daman har yanzu ban ji alakarsa da wannan ba" Sidi Mai Jaka ya dubeni da murmushi sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya cafka daya ya jefa abakinsa ya dube ni. "Nas kenan, amma dai yanzu ai ka isa ka baiwa wani labari, sanin kanka ne in har na sako sabon zaren labari to ko shakka babu in Allah ya yarda sai na hade shi da wancan na baya, shi yasa ba ka gane alakarsu ba, to amma ka jira sannu a hankali lokacin da zaren labarin zai rikida ya koma kan wancan su hade da juna ba zama ka sani ba" "Haka ne, ina to sauraronka" Sidi Mai Jaka ya dada jefa tubani daya a baki ya ce "Dadina da kai kenan Nas, iya sauraron labari, ba ka gajiya da saurare" Na fashe da yar dariya. To ai labarin naka ne wani sa'in dole ma a saurareka domin sai kayi kamar kayi gabas da mutum sai an jima can sai a sameka a yamma" Baba Sidi ya fashe da dariya sannan ya dube ni ya ci gaba da cewa. "Nas, tun daga wannan rana da mai gidan ya sauki dogon mutumin nan da matarsa basu kara barin gidan ba, har sai da ta Allah ta kasance a kansu." Na dago kaina na dubi Sidi mai jaka cikin sauri na ce dashi. "Kada kace na tari numfashinka baba Sidi, ina da tambaya." Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki. "Me kake son tambaya." Na dubeshi na ce. "Ni tun da ka fara bada sabon zaren labarin, kake ta ambaton wani dogon mutum, da kuma mai gidan daya sauke su, gashi dai ka siffanta su, kace sunan matarsa Hindatu, sunan dan mai gidan daya sauke su Abdulmalik, to shi dogom mutumin da mai gidan ya ya sunansu?" Baba Sidi ya dan yi shiru na dan lokaci sannan sai ya dubeni da murmushi ya ce. "Wani lokacin mutane kan bani mamaki, wai idan kana basu labari dole ne sai ka fadi sunan mutunen," Sidi mai jaka ya danyi shiru sannan sai ya ce. "Sunan dogon mutumin Saifullahi, mai gidan kuma Alhaji Kabiru. Nas ina fatan ka gamsu." Na gyada kai na ce "Eh, ci gaba" Sidi mai jaka ya dora daga inda ya tsaya. Washegarin ranar da Alhaji Kabir ya sauki bakin, tayi mutukar faran tawa bakin rai, domin yasa masu gadin gidansa sun bincikesu daga karshe suka gane cewa lallai da gaske yan gudun hijira ne kuma ya ki ne ya koro su. Dan haka sai Alhaji Kabiru ya ce a ci gaba da basu abinci, daga nan har zuwa ranar da matar Saifullahi zata haihu. To amma duk da haka sai da alhaji Kabir ya gana da masu gadinsa a sirrance ya ce suna fa kula da bakin nan, domin mutum na yau ba abin yarda bane domin sai ka dauko mutum daga rana ka sashi a inuwa, shi ko ya tura ka cikin wuta Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki A haka Saifullahi da matarsa Hindatu suka zauna cikin farin ciki, a karshen watan da suka sauka a gidan ne to wasu sangartattun yan fashi suka ziyarci gidan alhaji Kabir A ranar da yan fashin suka zo tun karfe hudu na yamma ake tafka ruwan sama haka nan yan fashin basu tashi zuwa ba sai ana daf da fara sallar asuba lokacin suka karaso ko shakka babu sun rigaya sun gama sanin abin da za su yi dan haka cikin ruwan sanyi barayin su goma sha tara kamar tururuwa suka cafke masu gadin buzaye cikin ruwan sanyi yayin da tsohon sojan nan ya yi kokarin kawo musu turjiya hakan shi yasa cikin ruwan sanyi suka danne shi suka yi masa yankan rago kai tsaye kuma suka wuce inda Alhaji Kabir yake shi da iyalinsa. "A can bangaren hadiman gidan Saifullahi ya ji idanunsa sun bude ya farka daga nannauyan barci sannan sai ya ji jikinsa ya fara rawa babu gaira babu dalili cikin sauri ya taba matarsa Hindatu. . Matar ta mike zaune cikin firigice, ta dube shi a tsorace da yake har yanzu razanar ya ki bata gama saketa ba. "Me...nene?" Saifullahi ya dubi matarsa ya ce. "Ji na yi haka kawai idanuna sun bude, duk yadda aka yi wani mugun abu ne ke shirin faruwa a gidan nan." Ya dan yi shiru yana saurare kamar zakara. "Dauko min damarar layuna da guraye na." Cikin sauri na mamaki ga macen dake da ciki wata uku da kuma magagin barci jikinta, ta mike ta nufi inda tsummokaransu suke ta mika masa jakar gurayen. Cikin yan mintuna Saifullahi ya daura gurayen, sannan ya mike tsaye. "Bari in je in gani." Hindatu ta dubeshi da murmushin karfafa gwiwa ta ce. "To, Allah kiyaye bacin rana Allah bada sa'a." Saifullahi ya juya cikin sauri ya fice daga dan dakin. Hindatu ta bishi da kallo, ko kusa ko alama bata fargabar komai, domin ta yi imani da cewa in dai ba karfin kaddarar karar kwana ba, babu abin da zai sami maigidanta, ta riga ta san sirrin dake tattare da gurayen, ta ga yadda suka ratsa ta tsakanin sojojin yan adawa akan iyakar kasarsu, suka tsallako ba a gansu ba, ba a kuma samesu koda da alburushin bindiga guda daya ba duk kuwa da irin barin wutar da ake yi. Saifullahi ya matsa wata katuwar laya mai kamar makami da ke kwibinsa na hannun dama. Sannan ya nufi cikin gidan, ya tabbata a lokacin in ba Allah ba, ko ifiritu bai isa ya ganshi ba. Saifullahi ya hangi barayin daya bayan daya har su goma sha tara sun mammakale a loko-loko guda biyar daga cikinsu tsaye a kofar babban dakin shakatawar gidam. Saifullahi ya zaro wani bakin guru daga kugunsa wani dogo mai kamar maciji ya zagaya barayin dashi har sau biyu, nan da nan barayin suka sankare a gurin basa ko motsi kamar itatuwa. Saifullahi ya barsu a gurin, sannan ya ringa bin barayin daya bayan daya yana zagaya su da gurun ba tare da sun ganshi ba har sai da ya kamar dasu baki daya, sannan sai ya nufi kofar falon, ya zagaye barayin ya kwankwasa kofar dakin shakatawar a hankali. Shiru-shiru bai ji motsin komai ba, Saifullahi ya dada kwankwasa kofar da karfi, har sau goma. Tswon lokaci, sai ya ji kamar motsi an nufo kofar a hankali kamar a tsorace. "Alhaji ni ne...Sanifullah i." Saifullahi ya ce cikin tattausar muruya. "Saifullahi...l afiya ina masu gadin?" Saifullahi ya tausasa murya ya ce. "Yan fashi ne suka kama su, sun kuma kashe tsohon soja." Alhaji Kabir ya rike numfashi a tsorace. "Yanzu ina barayin?" Ya tambaya a tsorace. "Gasu anan waje duk na kama maka su." "Kai kadai Saifullah?" "Kwarai kuwa ai ikon Allah ya fi da haka." Tsawon lokaci, bai fito ba, can sai ya leko a hankali a tsorace sannan sai ya ja da baya saboda mutanen da ya gani guda biyar duk a sankare kamar itatuwa. "Kada ka ji tsoro Alhaji, kana iya fitowa, babu abin da zasu iya har sai idan na ga dama da ikon Allah, sannan
Chapter 11 · 0% Book details