Sashe 2
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TSOHON ALKAWARI 1 . Nazir Adam Salih (Nas) . A ranar ashirin da takwas ga watan Afrilu na shekarar Milladiyya ta dubu biyu da guda hudu wacce ta yi daidai da ranar Laraba na tashi a rude, kwakwalwata a cunkushe domin sama ko kasa na nemi sabuwar basirar da zan yi rubutu na rasa. Tun misalin karfe goma nake zaune na sa littafin a gaba ina kallo har zuwa karfe goma sha biyu na rana kwakwalwata ba ta zo min da komai ba sai tunane- tunane marasa amfani. Ina nan dai zaune cikin akurkin dakina ni kadai da biro a hannu sai jujjuyashi nake yi kamar sigari daga karshe dai na tabbata ta kare min dan haka sai na ajiye biron na mike tsaye gami da mika kuma cikin damuwa. "Me ke damuna ne?" Na tambayi kaina ko da idanuna suka kai ga shafin littafi na ga ko alif ban rubuta ba sai na yiwa kaina murmushi, maganar makaranta littattafaina ta fado min sa'ar da suke cewa wai ta qare min, lokacin da na kasa fito musu da cigaban ALJANI YA TAKA WUTA da kuma BINDIGAR KWALI NA BIYU lallai ga dukkan alamu suma da gaskiyarsu tabbas ta kare min tunda dai gashi na sa littafi a gaba na kasa rubuta komai tsawon sa'o'i biyu. . Na gama hakura, na fito kofar gida kenan sai na hango wata yarinya dauke da fanteka da kwanuka a samanta abin tsautsayi ta zo tsallaka kwata kenan sai kafarta ta zame, fantekar a cike take da danwake, wannan shi ne ya yi sanadiyyar barkowar wani zazzafan gumi a kan goshina, zuciyata ta fara harbawa, sakamakon abin da na tuna, tabbas na san inda zan je na samo labari. Na sake duban dunkule-dunkulen dan wake burjuk a kasa sai ta tuno min da TUBANI ina tuno da tubani sai na tuno da dattijo SIDI MAI JAKA A cikin sauri na nufi gidan wata kakata, na yi sa'a kuwa na sameta a gida. Bayan mun gaisa sai na ce da ita. "Tubani nake son ki yi min." Ta dubeni cikin dariya ta ce "Ka ci gidanku ja'iri dan nema, kai a zamaninku ana yin tubani ne? Sai dai jefi-jefi." Na dubeta gami da sa alamun nutsuwa a fuskata na ce. "Dan Allah ki yi min wallahi da gaske na ke yi, fada min duk abubuwan da za a saya sai na baki kudin..." . Bata sami damar suturta tubanin nan ba sai bayan karfe biyu. Bayan na gama sallar Azuhur sai na ga ta bade tubanin da yaji sosai, domin na riga na san Sidi Mai Jaka zai yi matukar farin ciki da hakan, na sa ta dada kwarara masa mai, sannan aka zuba min shi a cikin kwano. Karfe biyu da kwata na isa gidan Sidi Mai Jaka dake bakin kasuwa. Abin da ya fi damuna shi ne tun sa'ar da muka rabu da shi shekara biyu da suka wuce ban kara zuwa wurinsa ba. . Ina isa kofar gidan sai na leka zauren cikin doki, gabana na ta faduwa domin kada na yi zuwan banza ko baya nan. Ga mamakina Sidi Mai Jaka na nan zaune akan kujerar katakonsa, carbi a hannunsa, haka nan akwai lofe a gefensa a ajiye bisa wani farin buzu. Sidi Mai Jaka ya dago kai muka yi ido biyu, ko dakika biyu ba a yi ba ya shaida ni. . "A'aha, yaushe a gari inji ma ki bako Nas, ashe daman kuna duniya?" Na dubeshi da dariya. "Baba Sidi kuma tsofaffi ba ku bar duniya ba ballantana mu." Sidi Mai jaka ya fashe da wata shakakkiyar dariya. Na dubi Sidi Mai jaka kallon tsaf, kana idanuna suka yo nazarin zauren. Ko kusa ko alama babu wani canji a kamannin Sidi Mai jaka ko kuma zauren gidan. Wani abin dadin mamaki kuma shi ne, tsohuwar rigar nan dake jikinsa mai kamar rariya, ita ce dai har yanzu bai sake wata ba, na yi mamakin karfin hali irin na wannan rigar, domin sa'ar da na fara ganinta shekaru biyu da suka wuce ban taba tsammanin zata sake wata guda a duniya ba ta fatattake ba. Har yanzu katon farin tabaron nan nasa na nan daraf akan hancinsa. . Jikinsa kuwa sa'ar da na dubeshi sai na fara tunanin me yiwuwa tun bayan rabuwata dashi a shekara biyu wankansa bai fi sau uku ba, me yiwuwa ma sai dai ko alwala. Amma fa duk da wannan al'amari na Sidi Mai jaka ina matukar girmamashi. Shekaru biyu da suka wuce, wannan tsoho Sidi mai jaka dogo fari yankwanannen tsoho, kansa fari fat, da furfura, farin gemu da fuska ma'abociyar fadin goshi ya taba bani labarin wata malamar asibiti TANI da wasu yan fashi. . Sidi mai jaka ya dubi kwanon dake hannuna cikin farin ciki yace. "Ko shakka ba na yi wannan alkawarina ne na TUBANI ko?" Na ajiye kwanon a gabansa lokaci guda kuma na matsar da lofen dake kan farin buzun na zauna na dubeshi cikin murmushi. "Tabbas ka canka tubaninka ne." . Fuskar Sidi Mai jaka ta washe, cikin nutsuwa ya mika hannu ya dauko wata butar roba, ya guntsi ruwa a bakinsa ya kuskure bakinsa ya fesar a jikin bango. Kana ya janyo kwanon tubanin nan ya bude ya fara kallonsa cikin nutsuwa. "Nas, ina me yi maka albishir da cewa wannan kyauta ta tubani da ka kawo mini tamkar wani dan mukullin labari ne da na dade ina son na baka to sai dai kuma shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka." "Haka ne." Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo.... .TSOHON ALKAWARI--> 2 . Shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka." "Haka ne." Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo.... Sidi Mai jaka ya birkita manya- manyan tubanin, sannan ya dauki tsinke, ya tsiraki wani kato ya tura a baki, nan da nan idanunsa suka fara zubar da hawaye saboda yaji.Ko wace ce ta yi ma tubanin nan, ba karamin kwarewa ta yi ba Nas." Sidi mai jaka ya ce dani. Na gyada kai. Sidi mai jaka ya cire farin tabaron dake idanunsa ya sa hannun rigarsa ya goge idanunsa sannan ya dubeni ya ce."Nas kune samari yanzu idan aka ce ka yi auren jari za ka yi?" Na dubeshi cikin mamaki na girgiza kai na ce."Ya danganta da irin macen...koda yake dai ni a gaskiya baya bani sha'awa, ni na fi son auren da muke kaunar juna don Allah." Sidi mai jaka ya dubeni ya kyalkyale da dariya ya ce.Abin da Anas mijin Mabaruka gurguwa kenan ya kasa fahimta." Na dubeshi a karo na biyu "Wa yekuma Anas mijin Mabaruka gurguwa?" Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani ya jefa a bakinsa."Shi ne labarin da nake son na baka Nas ban saniba ko kana da sha'awar irin wadannan labarai na irin wadannan mata masu matukar son kansu a duniya fiye da kowa?" Na yi shiru na dan lokaci ina juya, abin da ya ce cikin zuciyata. A gaskiya ni a son zuciyata na fi son a bani labarin yan ta'adda irin wanda ya bani shekaru biyu da suka wuce, to amma da yake ni yanzu ta riga ta kare min dole ne na saurari komai domin bani da zabi. Wa ya sani ma ko wannan ma ya fi wancan labarin dadi."Zan so kuwa na ji labarin wannan gurguwa, wace ce ita'" Na tambayeshi, Sidi mai jaka ya yi dariya ce."Bi ni a hankali Nas dadina da kai gaggawa sannu a hankali zan fara saka ma zararrukan labarin ina kulla maka su kamar yanda gizo-gizo ke sakar gidansa" Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan ya ci gaba."Ita wannan gurguwa mai suna Mabaruka ba a taba samun wata mace a zamanin ta mai arzikinta ba, miloniya ce a fagen kudi, to sai dai kuma wani ragin jin dadi da ta samu shi ne gurguwa aka haife ta" Sidi mai jaka ya juyo ya dubeni."Nas, domin ka fahimci zaren labarin nan da kyau, dole ne na ajiyar zaren labarin gurguwa mabaruka, na koma na dauko ma hoton Anas" Na dago kai a kagauce na kalle shi."Ka ce kuma da labarin gurguwa za ka ba ni." Sidi Mai jaka ya gyara tabaronsa kana ya tsikari tubani guda ya jefa a bakin salatinsa."Dole ne mu fara da zaren labarin Anas, in kuwaba haka ba Nas, ba za ka taba fahimtar labarin nan ba" Na gyada kai cikin fahimta."Yauwa Nas, ina son ka dauki zuciyarka ka mayarda ita cikin wata mashahuriyar otal." Na dubi Sidi mai jaka cikin kaguwa na ce dashi "Na mayar""Yauwa" Ya ce dani sannan ya fara.**** "To Nas ga Anas nan a cikin dakin karbar baki na otal din yana zagayawa cikin farin ciki da annashuwa domin aljihunsa a cike yake da albashinsa na wannan watan"Sidi mai jaka ya yi yar atishawa sannan ya ce."Kafin na ci gaba bari na baka hoton Anas. Ka ga Nas Anas dogo ne wankan tarwada mai kyawun fuska na ban mamaki. Domin an ce ba mata kawai ba hatta maza idan Anas ya zo wucewa sai sun kalleshi sun yaba da halittar Ubangiji. Wani karin abin burgewa kuma gareshi shi ne duk irinsuturar da ya sa sai ta karbeshi cif-cif kamar daman da ita aka haifeshi. Wannan da kuma iya zancensa da tarairaya shi ya sa dimbin mata suke kaunar Anas kamar su hadiyeshi. Wani abu da zai baka mamaki Nas, shi ne Anan ba wai yan mata bane kawai ke son sa, hatta dattijan mata ma suna kaunarsa sau da yawa masu budurwar zuciya daga cikinsu kan yi kokarin su kaiwa Anas cafka musamman ma dattijan zawarawa attajirai. Wani sa'in Anas ya kan kula su ba don komai ba kuwa sai don dan abin hasafin da sukan bashi.Daya daga cikin abin da Anas ya fi kauna a rayuwarsa shi ne hira da kyawawan mata, sau dayawa Anas ya kan tsinewa talauci sau daruruwa cikin zuciyarsa, domin a cewarsa shi ne ya shiga tsakaninsa da kyawawan mata masu aji. Duk da yake dai kyawunsa kan janyo ra'ayin kyawawan mata, to amma Anas bai taba gamsuwa ba domin shi ya riga