← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sani, akwai irin kyawawan matan da kyawunsa bai isa ya janyo su ba. Wannan ita ta sa Anas ya yi kurda-kurda ya sami aiki a Lagwada Hotel. Duk da yake dai shi ba kowan kowa bane a otal din domin aikinsa ya fi karfi a rabon abinci, wani sa'in kuma ya kan nunawa baki dakunansu su ta hanyar daukar dakon yan jakunkunansu, to amma wannan bata dami Anas ba domin shi burinsa ya cika. Dan wannan ita ce hanya daya jal da zai yi ta ganin kyawawan mata iri-iri, yanda yake so duk kuwa da cewa bashi da ko kwabo. Babban abin farin cikin Anas shi ne ya ga ana liyafa a otal din, musamman ma ta bakin aure, domin tana bashi damar gani kyawawan mata wani sa'in ma har yazanta da su. Anas yana daya daga cikin irin samarin nan marasa zuciyar nema, wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci BULUS ba tare da sun sha wahala ba. Dan haka...... .TSOHON ALKAWARI--> 3 . Wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci bulus ba tare da sun sha wahala ba. . Dan haka Naira dubu takwas din da ake biyan Anas a wata sun isa su sashi farin ciki, tun da dai ba zai iya kokarin samun abin da ya fi haka ba.Anan, sai Sidi mai jaka ya yi shiru ya dago kai ya dube ni."Nas, ina fatan kana fahimtar hoton Anas da nake ta kokarin zana ma" Na gyada kai na ce."Ina fahimta" Sidi mai jaka ya gyara zama sannansai ya ce."Bari to in koma da kai can baya kadan inda nake cewa Anas yana zagaya wa a otal din cikin farin ciki, lokaci- lokaci ya kan shafi aljihunsa a fakaice domin baya son mutane su fahimci cewar dan albashin Naira dubu takwas din aljihunsa yake tabawa. Haka nan shi kuma bashi da imanin da zai iya jurewa daidai da minti gudabai taba aljihunsa ba domin ji yake yi kamar kudin za su zube.Anas ya ci gaba da zagaya wa a dakin karbar bakina otal din ya gaisa da wancan ya yiwa wannan wasa har dai ya kawo daidai kan kanta inda Balaraba mai bada dan mukullan dakuna ke zaune. Anas ya matsa kusa da kantar ya dora hannunsa sannan ya dubi Balaraba da kyakkyawar fuskarsa ya hasketa da murmushi fararen hakoransa suka fito fili."Hajiya Balaraba ya ya garin ne?"Balaraba ta dubeshi da murmushi sannan ta turo biron dake hannunta cikin kunne ta fara juya shi, tana kanne ido."Lafiya lau Anas. Har ka tashi ne?"Anas ya dubi agogo sannan ya dube ta."Da saura dai Balaraba." ya dan yi shiru sannan sai ya ce."Balaraba ba ki ga motsin Halima ba ne?" Balaraba ta girgiza kai."Ban ganta ba, rabona da ita tun jiya da yamma kamar ya yanzu da ta zo neman ka." Balaraba ta ci gaba da susa da biron cikin kunnenta."Anas, wai don Allah yaushe za ka daina yaudarar yayan mutane ne?" Anas ya dubeta da murmushi ya ce."Sai kin shirya Balaraba." Balaraba ta harareshi."Me kake nufi da sai na shirya?"Anas ya shafi kyakkyawar fuskarsa."In har kin yarda za ki aure ni, me zai sa na ci gaba da yaudara? Daman ke ce ai ki ka ki da tuntuni kin amince dani da tuni na yi aure na huta." Balaraba ta kyalkyale da dariya."Oh! Anas Allah ya rufa asiri wallahi wadda bata san ka ba ka cuce ta." Ta dan yi shiru ta sunkuyarda kai.Balaraba bazawara ce, sau uku tana aure tana fitowa. Da yake tana da sakamakon diflomarta a hannu kuma basira ta bace mata maimakon ta yizamanta a dakin miji sai ta nemi aiki a otal, a lokacin watanta takwas kenan da fara aiki. Tun sa'ar da ta fara dora idanu akan Anas ta ji duk duniya babu wanda take kauna sai shi. Balaraba kyakkyawa ce daidai misali, to sai dai kuma bata cikin irin tsarin matan da Anas ke so, domin a cewar Anas duk macen da ta fiye gajarta bata cika kyakkyawa ba ko da kuwa tana da kyawun fuska. Balaraba ta so ta cusa kanta a wurin Anas,to amma irin jeri-jerin matan da kan zo neman Anas tun daga cikin gari har otal din, shi ya gargadi Balaraba ta hadiye maitarta ta yi shiru. To sai gashi kuma yanzu Anas da kansa yana zolayarta da zancen soyayya. Duk da yake Balaraba ta tabbata karya yake sai da kalaman nasa ya faranta mata rai."Balaraba." Anas ya kira sunanta. Balaraba ta juyo frgigit."Tunani n me ki ke yi?" Balaraba ta dago kai ta dubeshi na dan tsawon lokaci sannan sai ta ce."Kana da labarin kayatacciyar liyafar da za a yi yau a otal din nan?" Anas ya dubeta cikin mamaki."Tun jiya na sami labari a wurin Sabi'u amma ni bai ce dani ta hadu ba." Balaraba ta dube shi."Ai kuwa tun..." Kalamanta suka makale a fatar bakinta ba ta karasa ba. Anas ya dubeta cikin mamaki sai ya ga bashi take kallo ba bayansa take kallo. Can wajen kofar shigowa. Anas ya yi mamaki domin duk kusan lokaci guda jama'ar dake cikin dakin tarbar bakin suna surutai suka yi shiru na dan lokaci. Anas ya juyo sosai domin ya ga abin da ke faruwa. A daidai lokacin ne to ya hangesu.Wasu kyawawan mata ne suka shigo kowaccen suta ci kwalliya ta gani ta fada. Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe, sannan sai ya lura daya daga cikin yan matan tana tura kujerar guragu ta farinkarfe akan kujerar a zaune sanye da kayan alfarma masu tsadar gaske, wata budurwa ce gurguwa, za ta yi kimanin shekaru ashirin da bakwai.Koda Anas ya ci gaba da kallon gurguwar da yan matan ke turawa, sai ya yi ajiyar zuciya."Kai amma fa an yi asarar kayan kwalliya." Balaraba ta dubeshi da dan murmushi ta ce."Me ya sa ka ce haka?" Anas ya dan yi shiru sannan ya dada waigawa a karo na biyu ya kalli gurguwar, sannan ya juya ga Balaraba."Kin san ni ban cika shiri da munanan mata ba.Dube ta fa gurguwa mummuna amma kayan jikinta sun fi na kowa tsada, ai dole in ce an yi asarar kayan kwalliya." Balaraba ta fashe da dariya."Kai dai Anas wallahi ba ka da kaico, me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa kuma idan ya so yana iya sa wa ka aure ta......TSOHON ALKAWARI-4 . Me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa, kuma idan ya so yana iya sa wa KA AURE TA." Anasya harare ta."Allah sawwake, kin ga Balaraba ni fa bana son mugun fata, tun da abin na ki haka ne ma ni kin ga tafiya ta." Anas ya juya cikin sauri ya nufi cikin otal din a daidai lokacin ne to ya hango Sabi'u cikin sauri ya matsa gareshi."Sabi'u ka ga wata mummuna da alamun kudi." Sabi'u ya dubi Anas ido da ido, akwai wani yanayi a irin kallon da yake yi da ya sa Anas ya jigwiwarsa ta yi sanyi."Ya ya na ga kana yi min wani kallon uku ahu?" Sabi'u dan lukuti, gajere ma'aboin son sa kayan turawa duk kuwa da cewa ba wani kyau suke yi masa ba, ya gyara tsayuwa sannan ya dubi Anas "Ka san inda kake wage bakinka, in kuwa ba hakaba wata ran za ka kwana a ciki. Shin ka san waccan gurguwa ko wace ce kuwa?" Anas ya girgiza kai ya ce."Fahimtar dani." Sabi'u ya gyara wandonsa wanda ke kokarin sullubewa ya fado."Ni na san ba ka santa ba shi yasa kake kokarin muzantata. To bari in fada ma, ka ga duk munin nan nata, wallahi ba muni bane a gurina, kuma ka ga dai gurguwa ce to ni a gurina kafafunta sunfi naka sau dubu amfani." Sabi'u ya dan yi shiru sannan sai ya dago hannunsa ya dan daki kirjin Anas ya ce."Wannan gurguwa da kake gani ita ce Mabaruka S. Faruk, daya daga cikin matan da suka fi kowacce arziki a matan Afirka." Sabi'u ya ya balligoro ya jefa a bakinsa sannan ya dubi kyakkyawar fuskar Anas da murmushi."Na san ka sha jin labarinta, me yiyuwa a zahiri ma baka taba ganinta ba, to yau gata a otal din ka, bikin cika shekarunta ashirin da takwas a duniya za a yi. Mu kanmu nan otal din ba karamar sa'a muka yi ba, domin da liyafar a Landan za a yi sai Mabaruka ta ce ba za ta iya doguwar tafiya a cikin jirgi ba domin wai juwa kedamunta wannan shi ya sa su zuwa nan, ina fatan ka fahimce ni? Dan haka Anas ina son ka yishiru da bakinka domin otal din nan ta yi muguwar cin riba da liyafar nan da za a yi, idan ka sake manaja ya ji kalamanka akan Mabaruka, na rantse ma har da gemun tsohona ba za ka sake awa guda a gidan nan ba za a sallame ka daga aiki." Anas fuska na tsiyayar da gumi ya dubi Sabi'u a tsorace. Ya mari bakinsa da hannu"Shegen baki yau ya kusan ya janyo min tsiya." Sabi'u ya fashe da dariya ya ce."Zo mu je mu fara shirye- shiryen abubuwan da za su bukata, ka san fa muke da alhakin kula dasu." Sabi'u ya juya cikin sauri Anas ya bi shi a baya da sassarfa kamar doki. A zuciyarsa yana tunani, Mabaruka! Cab! Ai kuwa ya sha jin labarinta ba tun yau ba. Wani abokinsa ya taba cewa dashi. "Anas duk matan kasar nan babu mai arzikin Mabaruka gurguwa, kai bar ma ta kasar nan duk Afirka sai an tona. To amma a tsammanin Anas da ya ji an ce tafi kowacce mace kudi a Afirka ya dauka zai ganta wata kyakkyawa ajin farko, irin matan nan masu shekia fuska kamar madubi irin wadanda duk tsananin duhun dare sai kaga surar fuskarsu saboda tsabar kyau. Abin da Anas ya gani ya sashi kaduwa musamman ma yanzu da aka ce dashi wannan yankwananniyar matar mai tababben hanci kamar begila ita ce Mabaruka gurguwa uwar kudi! Allah mai yadda ya so. Anas ya ce cikin zuciyarsa.Tun karfe biyar na yamma aka fara liyafar farfajiyar otal din babu masaka tsinke duk inda ka duba motoci ne manya-manya masu bawo. Da yawa daga cikin bakin
Chapter 3 · 0% Book details