← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 21

Sashe 8

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka ke zuwa aiki a sati." Anas ya ji zuciyarsa ta harba, ko a lokacin da yake yawon banzan sa, babu abin da ya tsana a rayuwarsa irin mace mai naci, wacce zata makale masa kamar cingam ta hanashi shan iska. Sidi mai jaka ya dago kai ya dubeni da murmushi sannan ya ce "Nas, wata uku su Mabaruka suka yi cikin farin ciki, daga wannan kuma basu kara samun koda dai dai da sa'a daya ba ta farin ciki, domin a safiyar wata rana ne Mabaruka ita da kanta ta yi sanadiyar kawo karshen duk wani farin ciki nasu! Wata rana da safe aka yi sa'a Anas ya farka tun da asussuba, koda yake ba farkawar Allah da Annabi bace. Anas na kwance kawai sai ya ji idanunsa sun bude. Abin ya ba shi mamaki dan haka sai ya dubi agogo. Karfe hudu na asuba agogon ya nuna. Anas ya tashi zaune cikin mamaki, ya dubi Mabaruka gurguwa kwance a kusa da shi a takure kamar kunkuru tana ta barci abinta, mummunar fuskarta a yatsune. Anas ya dauke kai zuciyarsa na wasi-wasin dalilin da ya sashi farkawa a wannan lokaci. Tsawon lokaci yan zaune akan gadon, sannan ne to maganar Mabaruka ta fado masa. "...bana son wata mace ta mallakeka a duniya idan bani ba..." Wani zazzafan gumi ya barkowa Anas, sa'ar da ya tuno da wannan kalami nan da nan ya sake duban mummunar fuskar Mabaruka. A zuciyarsa ya ce cab! Ba zata yiwu ba duk kyawawan matan dake duniyar nan na rasa wacce zan kare rayuwata da ita sai wannan! Anas ya share gumi sannan ya dada kallon Mabaruka tsigar jikinsa ta dauki rawa....TSOHON ALKAWARI-7 . Sannan ya dada kallon Mabaruka, tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole ne na sami hanyar da zan rika zagayawa gari ni kadai, ya ce cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi baiwa Anas tsoro da al'amarin Mabaruka shi ne ya fahimci tana da bala'in Kishi. Sau da yawa idan suna tafiya a mota da taga ya dauke idanunsa gefe guda ya kalli inda mata suke sai ta kalleshi ta ce. "Me kake kallo?" Anas ya kan ji zuciyarsa kamar za ta fashe saboda haushi. Me take nufi ne da zata hana shi kallon kyawawa bayan duk da tarin miliyoyin kudin nan nata yar karamar yarinyar dake talla a gefen tituna ta fita fasali Bayan da wannan kuma akwai wata rana da yamma wata kawar Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci Mabaruka Lokacin da ta samesu zaune suke cikin tangamemen lambun shakatawar gidan Anas yana karantawa Mabaruka wani littafi na hausa wai shi SIRRINSU. Tun kafin Mabaruka ta gama gaisawa da Amal ta kura masa idanu. Anas ya lura da irin kallon da take yi masa, dan haka sai ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kamar yana kallon littafin da yake karantawa duk kuwa da cewa a fakaice kallon kyawawan kafafunta yake yi ta kasan littafin. "Tashi ka koma daga ciki kadan bamu guri zamu gana, idan mun gama zan sa a kirawoka." Mabaruka ta ce dashi, Anas ya mike tsaye simi-simi kamar tunkiya ya wuce cikin gidan zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi matukar kona masa rai, to amma tunda dai an saye shi ya yarda ya amince babu abinda zai iya domin kowa ya sayi rariya ai ya san ta zub da ruwa. Idan har akwai abu daya da Anas ya tabbatarwa da zuciyarsa shi ne ba zai taba yarda ya batawa Mabaruka rai ba, domin ya san hakan na nufin rabuwa da ita, shi ko ya san a yanzu ya gama sabo da jin dadi kum... "Anas." Ya juyo firgigit sa'ar da muryar Mabaruka dake kwance kusa da shi ta katse tunaninsa. Mabaruka ta dubi agogo, sannan ta yi mika ta dubi Anas cikin mamaki ta ce. "Lafiya na ganka a zaune haka tunda asussuba." Ta dan yi shiru sannan sai ta miko siraran hannunta ta shafi bayan Anas. "Ko ba ka da lafiya ne?" Ta rikoshi ta mike zaune, nannadaddun kafafun da Anas ya tsana fiye da komai a jikinta suka fito fili. Anas ya girgiza kai. "Kaina ne ya ke dan sara min...amma na san nan da dan lokaci zai bari daman lokaci- lokaci yakan yi min haka." Mabaruka ta dubeshi cikin shakka da mamaki ta ce. "Ina jin rashin yawan motsa jiki ne..." Ta dan yi shiru, sannan sai ta ce ya kamata na hada mana wata hadaddiyar liyafa ta shakatawa a gidan nan, ina ganin haka zai sa ka dan warware, kuma kamata ya yi bayan liyafar mu tafi kasashen turai hutu, domin tuntuni ya kamata ace mun tafi mun yi (honey moon) dinmu a can, dadin da bana ji sosai ne ya hana." Ta dan yi shiru tana duban fuskar Anas "Ko kuwa ya ka gani." Anas ya ji wani dadi ya lullubeshi domin tabbas ya san irin liyafar miloniya me take nufi ko shakka ba ya yi za a tara zuka- zukan mata kyawawa, abin da idanunsa suka fi kaunar gani fiye da komai a duniya. Don haka sai Anas ya dubeta cikin sauri ya ce. "Kwarai kuwa haka za a yi liyafa ba lallai kin zo da dabara." Suka fashe da dariya, sannan Mabaruka ta dora kanta bisa cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa kusa da tata, abin da Anas ya yi matukar tsana, ta ce. "Anas wai don Allah me ka fi kauna fiye da komai a duniya?" Anas ya dubeta cikin mamaki domin tambayar ta zo masa a bazata, kadan ya rage ya ce da ita kyawawan mata, to amma da yake tsohon kwararre ne a sanin tarkon mata ya fahimceta don haka sai ya dubeta da tattausan murmushin yaudara ya dada rungumota a kirjinsa ya ce. "Abin da na fi kauna a duniya ki ke son ki sani?" Mabaruka ta gyada kai cikin murmushi. Anas ya dubeta a tausashe duk kuwa da cewa zuciyarsa kamar ta tsage saboda haushi ya ce. "Ke na fi kauna fiye da komai a duniya." Mabaruka ta lumshe idanu cikin tsananin farin ciki Tun da take a duniya bata taba jin kalamin da ya faranta mata rai kamar wannan ba. Wani zazzafan hawaye na farin ciki ya yi sartu akan fuskarta. *** Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen tubanin karshe ya jefa a bakinsa, ya dubi kwanon cikin takaici, sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar yadda Anas ya yi tsammanin tun farko haka ta kasance domin duk kusan kala-kala ta kyawu na mata babu wadda ba a hada a wurin ba. Liyafar ta sami halarta mata kyawawa ashirin da uku, maza goma kacal wadanda mafi yawa ma daga cikinsu duk Anas ya girmesu. Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a tangamemen lambun shakatawar, aka saki kidan dujal yan mata da samari masu karancin kunya suka fara tikar rawa. A can gefe guda gindin wata katuwar lema fara, Mabaruka gurguwa ce da angonta Anas, ta caba kwalliya ta gani ta fada, to amma a wurin Anas kukun dake rabon abinci ma a wurin tafi Mabaruka kyawun fasali. . A daidai lokacin da liyafa ta yi liyafa ne to zazzakar murya mai kama da sarewa ta daki dodon kunnen Anas Nan da nan ya ji numfashin sa ya dauke ko shakka ba ya yi ya san mai muryar. "Yaya Mabaruka ki yi hakuri don Allah wallahi unguwa muka je sai yanzu na sami damar karasowa." Mai zazzakar muryar ce ke magana sa'ar da ta matso kusa da su cikin sauri. Anas ya kura mata idanu cikin tsananin shauki, zuciyarsa na harbawa, rabonsa da ganinta tun ranar da ya fara haduwa da ita. In ba dan muryar ba da zai yi wuya ma ya ganeta domin ta dada tsayi kadan ta dan kara kauri haka nan kyawunta ya dada bayyana a fili har daukar idanu fuskarta ta ke yi. Anas ya yi mamakin ganinta matuka. Budurwar mai zazzakar murya ba wata bace da ta wuce Ummi, budurwar da ta kirawo wa Mabaruka Anas a ranar da suka fara haduwa a wurin liyafar bikin haihuwar Mabaruka. Sidi Mai jaka ya dan yi shiru sannan ya dubeni ya ce. "Nas, ina fata ka tuna ta?" Na gyada kai cikin kaguwa domin na fahimci kamar ma yanzu ne labarin tsohon zai fara dadi. Sidi mai jaka ya ce "Yawwa Nas, sannan ya ci gaba. Mabaruka ta dubi budurwar cikin farin ciki sannan ta ce. "Ba ki da kirki Ummi kada ma ki yi kokarin wani kare kanki, idan yanzu kin zo a makare, to me ya hana ki zuwa liyafar aurena?" Ummi ta rufe fuska cikin dariya, sannan a karo na farko sai ta dubi Anas da tausasshen murmushi ta matsa kusa da shi ta durkusa ta ce. "Yaya Anas ina wuni..." Anas ya ji wani dadi marar misaltuwa ya kwarara cikin zuciyarsa. Cikin sauri ya tausasa murya ya ce. "Lafiya lau...Ummi!" Idan ya yi kuskurensa na farko kenan kiran sunan nata da ya yi. Ummi ta dubeshi cikin mamaki ta ce. "Ashe ba ka manta suna na ba." Murmushin Anas ya fadada. "Ai...tun...tun ..." Ya yi shiru sanda ya lura Mabaruka ta sunkuyar da kai ta mance dasu. Anas ya mike tsaye jikinsa na rawa ya dubi Mabaruka ya ce. "Darling bari in dan zagaya na barku ku gana." Nan da nan fuskar Mabaruka ta washe domin zamansa da Ummi shi take tsoro. "Kwarai kuwa gara ka bamu wurin domin muna son mu yi sirrinmu na mata." Anas ya mike ya nufi cikin farfajiyar lambu inda samari da yan mata ke ta sheke ayarsu, babu wanda ya kula dashi, domin ba a sanshi ba matar aka sani, sai yan tsirarun da suka sami damar halartar liyafar aurensa ne ke gane shi, suma shekeke suke gayar dashi, domin sun san shi ba kowan kowa bane ya dillalin kashi. Anas bai iya tsayawa cikin jama'a ba, sai ya zagaya can bayan lambun ya nemi karkashin wata inuwa mai yawan bishiya ya zauna. Bayansa jingine da bishiyar, daga inda yake zaune yana iya jiyo kida na tashi gami da hayaniyar samari da yan mata. Anas ya lumshe idanunsa, sannan wutar kauna da bege ta fara kona cikin zuciyarsa. Ko shakka ba ya yi kaunar Ummi ta fada zuciyarsa, tun sa'ar da ya fara ganinta irin begenta ya shuka kansa
Chapter 8 · 0% Book details