← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 21

Sashe 6

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsananin kaunarsu a gare ta. Mabaruka ta tashi cikin jin dadi, da gata marar misaltuwa, ga ta dai gurguwa amma duk satin duniya sai ta hada hadaddiyar liyafa, wani sa'in kuwa sai ta tara guragu irinta, ta sa su bi layi a kofar gida, ita ko a yi ta turata akan keken guragu na musamman tana raba musu kudi, tufa, ko abinci. Kudi ba matsalar Mabaruka bane, domin mahaifinta Alhaji Faruk biloniya ne, ya gama tara mata su gashi kuma ita kadai ce bata da ko kani guda daya. Wata rana Mahaifinta ya taba cewa da ita. "Mabaruka, duk abin da ki ke so ki yi da kudi ki yi kawai kar ki ji tsoron komai ki yi ta kashewa tun da dai naki ne. Ki godewa Allah da ya yi ki gurguwa da uba biloniya." Mahaifin Mabaruka ya mutu tana da shekaru ashirin da hudu a duniya, sakamakon wani mummunan hadarin jirgin kasa da ya ritsa da shi a kasar Indiya. Mahaifin nata Faruk ya bar duniya da bakin cikin har Allah ya karbi ransa bai ga mijin yar sa abar kaunarsa Mabaruka ba. Sau da yawa ya kan so ya tambaye ta shin ko ta sami saurayi To amma idan ya tuna da yadda take ita ba kyau ba a fuska hakan nan ga ta gurguwa sai ya yi shiru domin ko kadan bai san ya yi abin da zai sosa mata rai Duk da haka nan sau da yawa ya kan yi alfahari da ita domin ta yi matukar kama dashi musamman ma tababben hancinsa mai kamar begila. Sa'ar da mahaifinta ya rasu, sai duk kusan kamfanunnukansa da makudan kudinsa gami da sauran muhimman kadarorinsa suka koma karkashinta. Cikin kankanin lokaci ta zamo tabani ka ga sarki, ga ta dai gurguwa kuma mummuna, amma fuskarta ta fi komai kyau ga duk wanda ya santa a zahiri da badini ba don komai ba kuwa sai don dimbin arzikinta. Lokacin da mahaifin Mabaruka ya cika shekaru hudu da rasuwa, sai mahaifiyarta Aliya ta yi kiranta wata rana da yamma ta ce da ita. "Mabaruka kina tunanin aure kuwa?" Mabaruka ta sunkuyar da kai cikin taraddadi, domin ta san tun da take wani saurayi bai taba dubanta a matsayin ta burgeshi ba, sai dai ya dubeta a matsayinta na macen da ta fi kowa arziki a cikin matan Afirka. "Ina yi." Ta ce da mahaifiyarta kanta a sunkuye. Aliya ta dubeta cikin tausayi, domin ta san ko ita da ta sha miya a duniya ta fi Mabaruka kyan gani a fuska. "In dai kin sami wanda ki ke so sai ki sanar dani, kin ga ke kadai nake da ita a duniya, shi yasa nake matukar son na ga jikokina a duniya tun ina da sauran numfashina." Mabaruka ta yi shiru tana sauraren mahaifiyarta, yanayin fuskarta a birkice. Ita kanta ta san mummuna ce, sau da yawa in ta kalli madubi sau daya ba ta son ta kuma kallo a karo na biyu, amma ta kan gode Allah da ya yi mata dimbin dukiya. Aliya ta yi nazarin fuskar yar ta na tsawon lokacin sai ta ga duk hankalinta ya tashi. Ta san abin da ke damunta dan haka sai ta dubeta da murmushin karfafa gwiwa ta ce. "Kada ki damu da yadda Allah ya yi ki Mabaruka, abin da nake so ki kula shine kina da dukiya, kin san kuwa a wannan zamanin ba ta da na biyu." Ta dan yi shiru tana nazarin fuskar Mabaruka. "Ina fatan kuna fahimta ta?" Aliya ta ce da ita tana dubanta ido da ido. Mabaruka ta girgiza kai a sanyaye. Akwai alamun kwalla a idanunta. To amma bata bari mahaifiyarta ta gane ba domin ta san hakan na iya tayar mata da hankali. "Abin da nake so da ke Mabaruka shi ne ki duba ki waiga, ki hanga da idanunki, duk fadin garin nan, idan kin hango namijin da ki ke so, ki ka ga ya kwanta miki a rai ko wane ne shi ki yi kokarin ki shawo kansa ya zo nan gida gurina!" Mabaruka ta dubi mahaifiyarta cikin kaduwa ta ce. "Mama...ya ya za a yi na iya kawo shi har gida? Sai dai in shi ne ya ganni ya zo ya ce yana sona." Aliya ta dubeta gami da dariya. "Mabaruka kenan. Na fahimci har yanzu ba ki san irin yadda mutane suka dauke ki bane. To bari in fada miki duk kasar nan ke ake labari saboda tsabar kudin da ki ka gada. Duk da yadda ki ke ganin ki din nan ki ke raina kanki kin fi karfin raini, domin kudinki ya wanke duk wani nakasu naki. Saboda haka ina son ki sani cewa babu wani da namiji da za ki kirawo a girin nan ya ki zuwa gare ki ko shi wane ne, domin kina da babban makamin da ya fi nukiliya tasiri, dan in ba kudi babu zancen nukiliya balle aikinsa." Aliya ta dan yi shiru tana duban fuskar Mabaruka sannan sai ta daga hannu ta nuna fuskarta ta ce. "Na baki daga nan zuwa sati guda duk namijin da ki ka gani ya yi miki ki yi kokarin ki kawo min shi nan.. Nan da rana ya ta yau kenan.... Ranar da ta yi daidai da cikarta shekaru ashirin da takwas a duniya! Mabaruka ta ji wani zazzafan gumi ya fara lullubeta. Tambayar da ta fi damun zuciyarta shi ne, shin a cikin mako guda ya ya za a yi ta sami saurayin da ta ke so, ta kuma iya jawoshi har gida! Sidi Mai jaka ya yi shiru anan, sannan ya dubeni da murmushi ya ce. "Nas, ka ga abin da nake fada ma ko? Ai daman sai da na ce da kai kayi hakuri da sannu zan hade ma bakin zaren labarin biyu na daure. Gashi kuwa na daure ma su kamar yadda na yi maka alkawari." Na dago kaina gami da ajiyar zuciya "Haka ne." Na ce dashi "To ya ya kuma bayanin can inda muka baro, inda Mabaruka ta ce da Anas ya shiga mota su tafi." Sidi mai jaka ya dubeni ya yi murmushi ya ce. "Nas kenan, na dai fuskanci ka fi son can daya bangaren labarin ban yi mamaki ba a matsayin ka na saurayi dole ne labarin soyayya da kudi ya burge ka." Sidi Mai jaka ya yi shiru kana ya tsikari tubani guda ya jefa a baki ya dubeni idanunsa na zubar da ruwa kamar kuturu saboda masifaffen yajin dake cikin tubanin "Nas, ina son ka kaddara a cikin zuciyarka cewa ga Mabaruka da Anas nan zaune a cikin tangamemen falon gidansu Mabaruka suna fuskantar mahaifiyarta Aliya "Na kaddara." Na ce dashi cikin sauri domin na gama kaguwa na ji yadda za ta kasance. Sidi mai Jaka ya goge hawayen dake zuba daga idanunsa sannan ya ci gaba. Daga lokacin da katuwar (Jeep) din ta ajiye su Anas da Mabaruka a farfajiyar gidan zuwa lokacin da suka ratsa akalla Falo Bakwai ANAS YA GAMA FITA DAGA HAYYACINSA domin a iya tunaninsa bai taba imani da cewa akwai gidan da ya kai na su Mabaruka tsaruwa ba a duk fadin garin. Gashi dai Anas ma'aikacin otal ne, haka nan otal din ita ce uwa ga duk wata otal dake fadin garin wajen kayatuwa, amma sa'ar da ya ga irin tsari da ni'imar da aka shirya a gidansu Mabaruka sai ya ga duk darajar otal din ta zube a gurinsa, ta koma tamkar kango a zuciyarsa. A tunanin Anas ya dauka irin kayatattun gidajen nan da ya kan gani a finafinan Turawa, ba za a iya taba samunsu anan ba sai a kasashen turawan, domin abu ne mai wuya ace irin yadda almajirai ke cika tituna taf da barace-barace da kuma tarkacen marasa aikin yi da talakawan dake ta sintirin neman abinci sau daya a rana a titunan Najeriya, wai za a sami mai arzikin da har zai iya gina irin wannan! Hakika Anas ya yi masifar kaduwa sa'ar da ya shiga gidansu Mabaruka domin bashi da maraba da irin wadanda yake gani a finafinan turawa. Anas ya yi imani da cewa da ace za a dauke shi a cikin barci bai sani ba a jefashi a gidan, idan ya farka ya ganshi ciki babu abin da zai hana ya ce aljannu ne suka dauko shi suka kawo shi London. Lokacin da suka isa babban falon gidan karfe takwas da yan mintuna. Sa'ar da Aliya ta shigo dakin tuni har Anas ya zabi bangare guda na daga tarin kujerun dake dakin ya lume a ciki, to sai dai kuma duk wanda ya ganshi ya san a bala'in tsorace yake, domin a rabe yake a gefe guda ya yi fakare baya ko kwakkwaran numfashi kamar jikakken zakara. Aliya ta matso zuwa tsakiyar falon, ta dubi Anas da tattusan murmushi. "Ina son ka saki jikinka Anas ka dauka a zuciyarka cewa nan gidan ku ne." Anas ya ji gabansa ya fadi ras! Rabon da da wani ya ce dashi nan gidansu ne, tun ziyarar sa gidan wata budurwarsa Safiya wadda iyayenta suka so su makala masa ita, da kyar Anas ya samu ya tsere, domin a duk fadin duniya abokan gabarsa guda biyu ne, talauci da aure! Aliya ta nemi kujera ta zauna. Daga inda take zaune tana fuskantar su Anas, hakan nan ta lura da cewa Anas duk a rude yake tuni har ya faera zubar da gumi duk kuwa da ni'imar rabar dake kwararowa dakin. A zuciyarta, Aliya na cewa lallai abin ma zai zo da sauki tunda ma ya gama tsorata dani, don haka sai ta kalli Anas kai tsaye ta ce. "Ina fatan ta fada ma dalilin da ya sa ta kawo ka gidan nan?" Anas ya dubi Mabaruka a rude, Mabaruka ta yi masa murmushin yake, sannan ta sunkuyar da kai a kunyace a zuciyarta tana cewa, oh! Yau na shiga uku za a tursasa mutum ya aure ni ba tare da yana kaunata ba. Ganin Anas ya yi shiru sai Aliya ta dube shi ta ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?" "Sunana Anas...." Ya ce bakinsa na rawa. Aliya ta sake duban kyakkyawar fuskarsa ta ce, "Ina son ka dubi yarinyar nan da kyau ya ta ce." Anas ya dago kai cikin kaduwa
Chapter 6 · 0% Book details