Sashe 12
Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zasu yi motsi." Alhaji Kabir ya dubi Saifullahi cikin kaduwa. "Jirani to ina zuwa, bari na bugawa yan sanda waya." Mintuna goma bayan haka gidan ya cika da jami'an tsoro. An kame barayin gaba dayansu, tun daga wannan rana sai Saifullahi ya sami cikakken yanci, Alhaji Kabir ya gama yarda dashi, ya kuma bashi shugabancin masu gadin gidansa. Sannu a hankali watanni suka shude, har cikin Hindatu matar Saifullahi ya isa haihuwa, ran nan da safe sai ta fara nakuda, Alhaji Kabir da kansa ya bada mota a kaita asibiti. Kusan sa'o'i biyu suna jiran labarin haihuwa, a cikin masu jiran akwai Alhaji Kabir, matarsa Hajiya Sa'adatu, Abdulmalik da kuma Saifullahi. A cikin wannan sa'ar ne abubuwa biyu suka faru, farin ciki da bakin ciki, domin Hindatu ta haifi wata kyakkyawar budurwa, mai kyawu na ban mamaki, ita kuwa Hindatu Allah ya yi mata cikawa. Tun daga wannan rana Saifullahi bai sake samun lafiya ba. A ranar da za a radawa jaririyar suna, jikin mahaifinta Saifullahi ya matsa, tun da sassafe ya sa masu gadi suka roki Alhaji da ya zo yana son ganawa da shi domin ba zai iya zuwa da kansa ba. Alhaji kabir ya zo dakin mai gadin cikin gaggawa, Saifullahi ya dago kansa da kyar ya dubeshi ya ce bakinsa na rawa.......TSOHON ALKAWARI-11 . "Alhaji, jikina ya tsananta min, haka nan kuma bana jin zan warke daga wannan rashin lafiya tawa." Alhaji Kabir ya matsa kusa da mutumin cikin tausayawa ya ce. "Ka da ka ce haka Saifullahi, ai ita cuta ba mutuwa ba ce" Saifullahi ya girgiza kai ya ce. "Ba zan rayu ba Alhaji, domin na ji a jikina, Shi yasa na kiraka domin na baka abu daya da na mallaka a duniya wanda da shi ne kadai zan iya saka maka abin da ka yi min a duniya" Ya dan yi shiru yana mayar da numfashi. "Alhaji a duniya bani da wanda ya fi ka, na dauke ka a matsayin dan uwa, amini, ka mutunta ni, ka taimakeni a lokacin da nake matukar bukatar taimako" Saifullahi ya tura hannunsa cikin wasu tsummokara dake gefensa ya dauko wata tsohuwar jaka ta bakin yadi ya mikawa Alhaji Kabir. "Wannan shi ne kyautar da zan yi maka ta musamman, guru ne, da layu guda uku. Sirri ne na tsarin kai da mahassada, da su ne Allah ya taimakeni na kama barayin nan" Ya dan yi shiru sannan ya ci gaba. "Ga Yata nan jaririya, na baka ita, ka taimake ni dan Allah ka rike min ita, idan an jima in za a sa mata suna, ka sa mata suna Nana firdausi, domin sunan mahaifiya ta ne" Ya fara tari, sannan sai ya yi karfin hali ya dago ya dubi Alhaji Kabir idanunsa na zubar da kwalla. "Alhaji wannan ita ce alfarmar da nake nema, za ka yi min..?" Cikin sauri Alhaji Kabir ya amsa masa. "Na amince Saifullahi, in Allah ya yarda zan rike ta kamar yar da na haifa a cikina kuma ina fatan ma Allah ya baka lafiya" Washe gari da aka yi sunan Firdausi mahaifinta Saifullahi ya bar duniya, a lokacin kwananta takwas kawai a duniya. Bayan an binne Saifullahi, sai Hajiya Sa'adaru ta fito dauke da kyakkyawar jaririyar ta sami maigidanta zaune a falo shi da dansa Abdulmalik, ta zauna kusa da maigidanta, sannan ta kurawa jaririyar idanu ta ce. "Oh, Allah mai yadda ya so, Allah gwanin iya halitta, ka dubi wannan kyakkyawar halitta, kai wallahi Alhaji ina bala'in son jaririyar nan, ba don komai ba. Sai don irin maraicinta, da kuma kasancewar sunan mahaifiyata ne nima aka sa mata" Alhaji Kabir ya dubi matarsa ya ce. "Ki riketa da kyau cikin aminci da kulawa kamar yadda za ki rike danki Abdulmalik." Hajiya Sa'adatu ta rungume jaririyar ta dubi maigidanta, sannan sai ta dubi kyakkyawar fuskar jaririyar ta ce. "Daga yau kin zama yata, Allah ya raya ki UMMI na" Tun daga wannan rana ne sunan Ummi ya bi wannan jaririya. Sidi mai jaka ya juyo da murmushi ya dubeni. Ni kuma na dubeshi cikin bazata. "Baba Sidi, kana nufin ka ce min wannan jaririyar ita ce Ummi din da Anas ya kamu da ciwon Kauna?" Sidi Mai Jaka ya fashe da dariya ya ce. "Nas kenan, ai daman sai da na fada ma sai na baka mamaki, sannu a hankali zan dawo da kai na jone ma bakin zaren labarin, gashi kuwa tun ma kafin na jone shi din har ka fara ganin alakarsu da wancen tsohon zaren labarin da muka saka" Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. "Wai Baba Sidi kana nufin ka ce ita wannan kyakkyawar Ummi din iyayenta ba ma wata tsiya ba ce a garin nan" Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. "Kwarai kuwa Nas, dan ma ka tari numfashina, domin har yanzu zaren labarin bai kare ba, bari in gama saka ma shi, idan na gama zaka fahimci rudanin dake cikin wannan labari" Na gyara zama na dubi Sidi mai jaka cikin doki na ce "Ci gaba, ina saurare" Sidi mai jaka ya jefa tubani daya a baki ya ci gaba.**** Sannu a hankali Nas Ummi ta fara girma kullum ta Allah kyawunta karuwa yake yi. Ba mutumin dake ganinta a waje ba lokaci-lokaci hatta Alhaji Kabir da matarsa Sa'adatu dake ganinta kullum suna mamakin kyawu irin na Ummi Wani abin ban mamaki shi ne tun ranar da aka haifi Ummi kullum a hannun Abdulmalik take wuni yana yi mata wasa. Gashi dai shi ba mace ba amma kullum yana makale da jaririyar dan haka har sa'ar da Ummi ta kai shekaru goma a duniya, duk inda zasu tare suke da Abdulmalik a lokacin nan shi yana da shekaru ashirin a duniya Amma duk da haka kusan tsayin sa daya da Ummi Wani sa'in sai Abdulmalik ya dauki Ummi a mota su yi ta yawo kantuna-kantuna inda ake sayar da kayan lashe-lashe da makulashe idan sun je sai Abdulmalik ya juyo ya kalli Ummi cikin fara'a a tausashe ya ce "Ummi, dauki duk abin da ki ke so" Cikin farin ciki da kauna irin ta dan uwa sai ta dubeshi ta ce "Abdulmalik kana shagwaba ni!" A duk lokacin da ta ce haka sai Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta dada narkewa da begenta domin tun ranar da aka haifi Ummi Abdulmalik ya fara sonta tun ma bai san mene ne kauna ba. Don haka sannu a hankali shekaru na shudewa har wannan son ya juye zuwa kauna. To sai dai kuma abin da Abdulmalik ya kasa fahimta shi ne a duk tsawon zamanin nan Ummi a matsayin dan uwanta na jini ta daukeshi domin bata taba sanin cewa ba uwarsu daya ba ubansu daya ba. Abdulmalik ya riga ya fi kowa sanin cewa Ummi ba yar uwarsa ba ce ta jini Domin shi ne ma ya yi sanadiyyar haihuwarta a gidan, to amma daidai da rana daya bai taba nuna mata alamu ba A bangaren iyayen Abdulmalik kuwa sun dade suna kallon irin alakar mai karfi dake kulluwa tsakanin yaran guda biyu, koda yake ga zuciyar Alhaji Kabir bai taba daukar alakar yaran a bakin komai ba face kawai sabo da kuma yan uwantaka. . To amma ranar wata laraba da yamma sai matarsa Sa'adatu ta dubeshi ta ce. "Alhaji, wai kuwa kana lura da al'amarin yaran nan?" Maigidanta Kabir ya dubeta cikin mamaki. "Kamar ya ya ina lura dasu? Wannan ai dole ne domin kuwa yayana ne." Sa'adatu ta dubeshi cikin yar damuwa ta ce. "Ba abin da nake nufi kenan ba." "To me ki ke nufi?" Sa'adatu ta gyara zama ta ce. "Wato ni gani na ke yi kamar Abdulmalik kaunarta ya ke yi." Alhaji Kabir ya dubeta baki bude cikin mamaki ya ce. "Yau ga ikon Allah, to daman mutum ba dole ne ya kaunaci dan uwansa ba." Sa'adatu ta girgiza kai. "Abin ya wuce da haka ina tsammanin begenta ya ke yi." Alhaji Kabir ya kura wa matarsa idanu na tsawon lokaci, sannan sai ya yi kasa-kasa da murya ya ce. "Kada fa ki manta cewa, har yanzun nan Ummi ba ta san cewa ba mune iyayenta ba." Sa'adatu ta yi murmushi. "Idan ita ba ta sani ba, ai shi Abdulmalik ya san ba yar uwarsa ba ce ta jini. Kuma abin da ya sa ka ji na fada ma haka shi ne, yanzu da ka leka cikin dakinsa za ka ga duk ya zagaye shi da hotunan Ummi, kowannensu ya rubuta (My love) Alhaji Kabir ya dada duban matarsa na tsawon lokaci, akwai alamun tunani a fuskarsa, can sai ya yi ajiyar zuciya ya ce. "To, sai mu bar wa Allah komai, ya yi ikonsa, Allah zaba musu abin da ya fi alkairi." . A bangaren Abdulmalik, sannu a hankali har Ummi ta kai shekaru goma sha bakwai. Kullum wutar begenta sai dada ruruwa cikin zuciyarsa take yi, ita ko in ka dauke soyayya irin ta yan uwantaka bata dauke shi a bakin komai ba. Amma duk da haka nan dai kullum suna tare basa rabuwa. Wata rana da yamma Ummi ta shiga dakin Abdulmalik ta ci kwalliya, fes,fes, hakan shi ya sa zuciyar Abdulmalik harbawa. A ranar ne to Abdulmalik ya ji kamar ya amayar mata da boyayyen sirrin zuciyarsa, to amma sai ya tuna kashedin da mahaifinsa ya yiwa duk wani mutum dake gidan inda yake cewa. "Kada wani daga cikinku ya sake ko da da wasa ya fadawa Ummi cewa mu ba iyayenta ba ne." Wannan shi ya sa Abdulmalik hadiye maitarsa. Zuciyarsa na harbawa ya dago kai ya dubeta cikin yabawa da abin da ya gani ya ce. "Kai, amma fa kin kara kyau Ummi." Ummi ta dube shi cikin dariya ta ce "Na gode yaya Abdul." Ta dan yi shiru tana kallon jeren hotunanta ko ina a cikin dakin sannan ta dubi Abdulmalik ta ce. "Duk duniya babu yan uwan dake kaunar juna kamar mu, dubi fa Yaya Abdulmalik duk ka bi ka wani shagwaba hotunana kamar wata budurwarka. Wannan ko budurwa ce ai ba karamin kaunarta kake yi ba." Abdulmalik ya sunkuyar da kai da dan murmushi, wata zuciya na cewa da shi, fada mata kawai cewa ita fa ba yar uwarka ba ce ta jini. To amma sai gargadin mahaifinsa