← Book details Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Tsohon Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

samu damar tattaunawa sosai" Ta dan yi shiru tana nazarin fuskarsa ganin cewa har yanzu a rude yake sai ta ce. "In kuma har yanzu ba ka gamsu ba bari in fito fili in fada ma abin da zamu tattauna. So nake na saye ka!" Anas ya ji gabansa ya fadi ya dubi Mabaruka a rude. Mabaruka ta dubi Anas ta fashe da dariya ta ce "Me ye na ga ka hada fuska kana jin ba zan iya sayen naka bane?" Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni "Nas wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin" Na dubeshi cikin kaguwa "Haba Baba ya ya sai da labarin ya dauko dadi za ka katse ni anan?" Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani daya ya jefa a baki kana ya dube ni ya ce. "Nas kenan, har kullum ba ka fahimtata in ban da abin ka ai sauran zararrukan labarin da ke gaba sun fi wannan ma dadi nesa ba kusa ba. Ka yi min afuwa Nas zan koma da kai can baya shekaru ashirin da takwas da suka wuce kada ka damu sannu a hankali zan dawo da kai kan tsohon zaren labarin da na gama yanzun nan na hada maka bakinsu in kulle guri guda" Na gyara zama sannan na ce dashi. "To Baba Sidi, ina sauraronka" Abin da yake bani mamaki ga lamarin Sidi mai jaka shi ne irin yadda yake bada labarin ko sarkewa ba yayi. . SIDI MAI JAKA ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya dubeni cikin murmushi, sannan sai ya tura tsinke ya tsikari wani dankareren tubani ya tura a baki. "Nas duk duniya babu abin da na fi so kamar tubani" "Haka ne" Na ce dashi. Sidi mai jaka ya dubeni. "Me yiwuwa ka yi mamakin irin yadda nake ta zubo maka labari bana ko tsayawa" Na gyada kai. "Kwarai kuwa" Na ce dashi "Domin a wancan karon da na zo duk kusan mintuna goma sai ka tsaya" Sidi mai jaka ya fashe da dariya. Sannan ya sunkuyar da kai ya ce. TSOHON ALKAWARIN da ka cika min ne ya sa nake ta kwararo labarin nan ba wakafi balle aya" Na dubeshi cikin mamaki. "Wane tsohon alkawari kuma?" Sidi Mai jaka ya dubi kwanon dake gabansa ya ce. "Tubanin da ka yi min alkawari shekaru biyu da suka wuce shi nake nufi da tsohon alkawari. Domin ba duka mutum bane a wannan zamanin kan iya cika alkawari" Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan sai ya dubeni ya ce. "Nas, ina son ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita shekaru ashirin da takwas da suka wuce a lokacin ma ba a haifi Mabaruka ba" Na dago da kai cikin kaduwa. "Shekaru ashirin da takwas?" Sidi mai jaka ya gyada kai. "Kwarai kuwa, domin shi ne zaren labarin mu na biyu." Ya dan yi shiru kana ya tsikari tubani ya jefa baki sannan ya dubeni. "Nas, shekaru ashirin da takwas da suka wuce, wasu ma'aurata guda biyu wadanda ke cikin tsananin shauki na kaunar junansu sun kasance zaune a wani fankadeden falo na alfarma wanda a takure zai iya cin mutune sittin ba tare da wani ya shaki numfashin dan uwansa ba. A zaune a daya daga cikin kujerun wani mutum ne dogo, baki, sanye da farar riga suwaita da shudin wanda na shadda, kansa babu hula, hakan shi ya bayyana matashin sankonsa a fili, da yawa daga cikin wadanda suka sanshi a lokacin, sun riga sun yi imani da cewa mutumin ba zai dade da gashi a kansa ba, domin gashi dai a lokacin bai fi shekara talatin da biyar ba a duniya, amma dogon sankon ya gama cinye rabin gashin kansa. Wannan dogon sanko dake kan mutumin bai hana matarsa Aliya mutuwar kaunarsa ba, duk kuwa da cewa a lokacin ma tana da cikin dan wata takwas Wannan mutum mai dogon sankon sunansa A. Faruk. Ba karamin mutum bane, domin a fagen kudi biloniya ne, mamallakin kamfanoni ashirin da takwas a nan kasar. Jita-jita kuma na cewa wai yana da kamfanunnuka sama da goma a kasar Amurka, da kuma wani katon asibiti a kasar Birtaniya. Lokacin da ya auri matarsa Aliya tana yar shekaru ashirin daidai. In ban da yawan maganganu n yan uwa da babu abin da zai sa ya yi aure a lokacin. Domin tun yana dan saurayi kafin ya yi arziki ya taba neman wata yarinya Murja, wani direban mota ya kasa shi, tun daga wannan bai kara sha'awar ya nemi wata mace ba a duniya sai da ya hadu da Aliya. Da farko sa'ar da aka yi bikinsu da Aliya bai taba tsammanin auren zai sami wata kyakkyawar nasara ba. To amma kwanaki uku kacal da yin auren sai ya fuskanci ashe Aliya mace ce ta gari mai iya kissa da soyayyar janyo hankalin maza. Wannan ita ta sa a yanzu A. Faruk yake mutuwar kaunar matarsa Aliya. Duk inda zashi koda kasashen ketare ne tare suke tafiya, to amma yanzu da yake cikinta ya tsufa sun fi wata uku a gida Najeriya suna renon cikin. Aliya ta muskuta akan kujerar ta shafa cikinta ta ce. "Kwanta Mabaruka yar gata." A. Faruk ya ajiye jaridar dake hannunsa kana ya shafi dogon sankonsa ya dubi matarsa Aliya cikin murmushi. "Aliya, ke fa wallahi ba kya rabuwa da rigima in ban da abin ki wa ya ce dake mace za ki haifa da har ki ke sanya mata suna Mabaruka?" Aliya ta harareshi, sannan ta mike da kyar, ta nufo inda yake, tana zuwa sai ta kwanta akan cinyarsa a rigingine kana ta shafo cikin nata ta dubeshi ta ce a tausashe. "Ni na san mace ma zan haifa in Allah ya yarda." Faruk ya fashe da dariya ya dubeta. "To yanzu da har ki ka sa mata suna Mabaruka idan kika haifi namiji kuma me za ki sa masa? Kamata ya yi ki zabi sunaye biyu, na mace da na namiji, ina ganin zai fi kyau idan namiji ne mu sa masa suna Mabaruki." Aliya ta fashe da dariya. "Kai (darling) don Allah ka daina sa ni dariya, kar ka sa cikina ya yi ciwo." Faruk ya dubeta. "A'a, to ke kin ga laifina? Tun da dai kin ce idan mace ce za ki sa mata Mabaruka ni kuwa idan namiji ne sai in sa masa Mabaruki." Aliya ta kamo wuyansa cikin dariya ta matso da fuskarsa kusa da tata, ta dora bakinta akan kunnensa ta ce. "Kai a tunaninka idan na haifi mace da wa za ta yi kama?" Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya, sannanTSOHON ALKAWARI-5 . Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya sannan ya tuna da dogon sankonsa, gami da tababben hancinsa wanda sau da yawa, shi yake hana shi ganin madubi, sai ya dubeta da murmushi ya ce. "Ina fatan ko mace, ko namiji za ki haifa Allah ya sa ya yi kama da ke Aliya. Aliya ta rungumo shi cikin farin ciki domin ita kanta ta san kyakkyawa ce. Anan, sai Sidi Mai Jaka ya yi shiru, sannan ya sa hannu ya goge gumin da ke sartu akan goshinsa. Me yiwuwa zafi ne, babu mamaki kuma zazzafan yajin tubanin ne ya sashi gumi. Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce. "Nas, wani sa'in matasan mata sukan bani mamaki, da zarar sun sami ciki sai kaga suna ta zaben, wai sun fi son su haifi mace, ko namiji ko kuma mai kama da su, ko kyakkyawa...hak a dai za ka ji suna ta kawo tsarabobi iri daban-daban kai ka ce su ke da ikon halitta. Ni a ganina Nas, gara a bar wa Allah zabi domin shi ne gwani akan komai ko kuwa me ka gani?" Na gyada kai cikin sauri. "Haka ne. Ci gaba baba." Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa kana ya girgizaq kai cikin takaici, domin duk yawan tubanin nan dake ciki ya nhadidiyesu kamar zakara wadanda suka rage basu fi kwaya goma ba. Sidi Mai jaka ya canki na goman karshen ya jefa baki kana ya ci ga. "Nas, wata guda da yan kwanaki, da faruwar wannan hira da na baka labari dazu tsakanin ma'auratan biyu, sai Aliya ta haihu. Ta wani bangaren haihuwar ta zo musu kamar yadda suka zata tun farko to sai dai kuma ta wani bangaren haihuwar ta zo musu a murde, musamman ma Aliya. Lokacin da Aliya ta haihu bata san inda hankalinta yake ba, sai bayan kusan sa'a guda da haihuwar ne sannan likita ta zo gabanta da murmushi ta ce. "Ina taya ki murna kin haifi mace." Aliya ta yi matukar farin ciki da jin cewa mace ta haifa, amma sa'ar da likitan ta miko mata jaririyar da ta haifa sai duniyar jin dadin Aliya ta birkice lokaci guda. Aliya ta dubi jaririyar cikin kaduwa, ko kusa ko alama jaririyar bata yi kama da ita ba, gashi dai lafiyayyace sosai to amma irin tabebben hancin mahaifinta ya mamaye kusan rabin fuskarta, bugu da karin bakin ciki ga Aliya kuma jaririyar ba ta da kafafu domin duk a shanye suke sili-sili kamar maburgi. "Wannan...kafaf un nata ba za su gyaru ba?" Aliya ta tambayi likitan muryata na rawa. Likitan ta girgiza kai cikin jimami. "Babu wani likita a duniya da ya isa ya gyara kafafun nan nata. Ki godewa Allah da ya kawota duniya cikin koshin lafiya, ba kya ganin idan ki ka dauke shanyayyun kafafun lafiyarta kalau." A daidai lokacin da likitar ta yi shiru sai jaririyar ta bude idanu. Aliya ta dubeta tayi kamar za ta fashe da kuka Ga mamakinta sai jaririyar ta dubeta ta washe baki cikin murmushi Aliya ta rungume yar jaririyarta cikin kuka ya ce. "Ina son ki Mabaruka, ina son ki haka nan domin haka Allah ya so ya gan ki." Shekaru ashirin suka shude kamar wasa, a cikin shekaru ashirin din nan babu irin gatan duniyar da Mabaruka bata gani ba. Anan Najeriya ta yi makarantar firamare dinta, amma duk sauran karatunta a Burtaniya ta yi. Duk da kasancewar Mabaruka gurguwa kuma mummuna, iyayenta basu ki nuna mata tsananin soyayya ba. Wani Ikon Allah kuma tun daga kan Mabaruka, Aliya ba ta sake haihuwa ba, wannan shi ya kara
Chapter 5 · 0% Book details