← Book details So Dan Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

So Dan Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na Louis Vuitton da ta yi rolling kanta da shi a hankali take taku ai daga kan stairs in har ta ari sa sakkowa zaraf idanunta ya shiga na Maah dake zaune a Dining area da alama breakfast ta kammala jerawa shi ne ta zauna zaman jiran sakkowar Esherh'n. Laa Maah Tah wai kece da gaske? Esherh ta fa a cike da zumu i tana ari sawa har da an gudu-gudunta Dining Room ta a je mini bag nata Pink color a kan Kujerar Dining in tare da afalewa Maah in ta rungumota tana dariya. Dariya Maah ta yi tana shafa kanta ta ce. Wato dai ke har a kullum bakya girma ko? Yanzu Fisabilillah so kike ki karyani? Turo Lips in ta dake auke da Fenty Beauty Lip gloss ta yi jin abin da Maah in ta ce cike da shagwa a irin yadda ta saba ma ta ta ce. Waassh MaahMaah kinji ki da wani batu fa yanzu ni in har wani iba gareni da zan karya ki? Maah tana murmushi ta ce. Sosai kuwa dan na lura kwana biyun tashen cin abinci da yawa kike fama da shi. Dariyar da ya bayyana ha oranta farare tar da su Esherh ta saki jin kalaman Maah tasan da biyu ta yi dan ta tsaya taci abinci. Sai lokacin suka gaisa cike da auna irin na uwa da ya kuma cike da raha sannan Maah ta ara da fa Zauna muyi breakfast in kafin ki tafi dan nasan ba aramin abu ba ne a wurinki ki iya fita Company ba tare da kinci komai ba Maah ta fa a tana an kafe ta da ido har da wani aure fuska wai dan ma kar Esherh in ta ga fuska har ta ce a oshe take. Ba musu kuwa Esherh ta zauna suka ci abincin suna yi suna fira bata ci da yawa ba ta tashi ta yi ma Maah sallama sannan ta baro angaren nasu bayan Maah ta ha a ta da wani abincin a flask da shima musamman ta yi ma ta kamar yadda ta saba na Lunch sai da Esherh ta biya ta gaishe da kakan nata wato Mahaifin Maah in ta cikin raha kamar yadda suka saba sannan ta yi masa sallama ta bar angaren nasa daga nan ta ari sa wurin Security na musamman da Granny da kansa ya ware domin bata tsaro zuwa aiki kasancewar Ranar Monday ne tushen aiki wata farar JAGUAR XJL sabuwa fil aya daga cikin security in ya bu e ma ta ta shiga sannan ya rufe kana motocin guda uku a jere suka ari sa harabar Babban Gate na Estate in tare da fita daga ciki a nutse har suka hau titi kasancewar ta ba mai son gudu da mota ba shi ya sa motocin suke a jere kuma a hankali suke tafiyar. *Ethereal Kreations Joint EKJ* Shahararre ne kuma lamba cikin Company da a ke ji da su ta hanyar samar da kayayyaki na sakawa na mata da ma sauran kayan ado irinsu sar a abin hannu jaka da sauransu, ainihin Companyn mallakar Maah ne sai dai sakamakon abubuwa da suka yi ma ta yawa ya saka shekaru biyu ke nan da ta dam a akalar Companyn gaba aya a hannun iyarta Esherh domin Fashion Designer ta karanta kuma cikin ikon Allah a an wa an nan shekarun ba aramin aukaka da nasarori Companyn ya ara samu ba shi ya sa a koda yaushe Maah take alfahari da iyar nata dama kuma tun farko da sunan Esherh in ta bu e Companyn ma'anar EKJ in shi ne ESHERH KALTHOM JEDDY's sai dai ta oye hakan a ranta ta kuma saka wa sunan wani ma'anar daban saboda wani manufa nata shi ya sa Esherh tana kammala karatu ta yi gaggawar dam a ma ta ragamar Companyn yanzu Matsayin CEO Esherh keda a Companyn kuma tana iya kar bakin arin ta wurin ganin a kullum Companyn ya ci gaba da samun nasarori da aukaka domin ta wannan hanyar ne ka ai zata tabbatar wa da Maah in ta cewar lallai jaruma ce iyar nata kuma mai aunar farin cikinta. Esherh zaune take cikin hamsha in katafaren Office nata dake hawa na arshe kuma ya wadatu da komai na alfarma cike wasu takardu take before su shiga meeting da zasuyi da wani Companyn na fashion design daban a kan wata ar sa ani da ta shiga tsakaninsu na design in sabuwar sar a da za su fitar sai kuma wancan Company in suka auka suka dan arawa nasu design in suka kuma riga su fitarwa. Knocking ofar Office in a ka yi kusan sau uku a tare ha e kuma da danna doorbell dake wurin duka lokaci guda. Ba tare da ta ago daga abin da take yi ba kuma bata nuna damuwa a kan wannan abu da a yi ba dan ta bari ta ga wani mahaluki ne hakan ya sa ta bada umarnin shiga ta hanyar furta. Come on in. Kafin ta rufe baki sai ga Basma ta bayyana cikin office in kai da gani kasan a wani irin fusace take sai dai ganin yadda ko arzi in Esherh in ta a go ta kalle ta bata samu ba bare ta sama gwarin gwiwar zubar mata sa buhu-buhu da wando na rashin mutunci da kuma warning da ta zo ta yi ma ta a kan mijinta hakan kuma da Esherh'n ta yi ba aramin ara fusa ta ta yi ba. A fusace ta ari sa tare da buga desk in gaban Esherh da hakan ya sa wasu daga cikin takardun dake wurin suka yi sama wasu kuma suka zube. A hankali ta a go manyan fararen idanunta tare da ware su saman fuskar Basma dake uban huci sannan cikin nutsuwa ba tare da wani reaction ba ta sake lumshe idon nata sannan ta ware su a kan Sakatariyar ta da ta biyo bayan Basman a ru e cikin son fidda kai tun kafin Esherh ta furta komai Sakatariyar ta riga ta da fa Am so sorry ma'am nayi duk iya arina a kan hanata shigowa amma ta i har sai da ta riba ce ni sannan ta shigo.... Okay You can wait outside. Esherh ta katse da fa in hakan tana mayar da hankali wurin aukar takardun da suka barbaje a asa, godiya Sakatariyar ta yi ma ta sannan ta fita taja musu ofa. Ci gaba Esherh ta yi da abin da take yi kamar ba zata kula Basma da ta gama kai wa iya wuya ba sai dai ta kasa ta uka komai tun daga duban farko da Esherh'n ta yi ma ta. Zaki iya zama naji dalilin zuwanki idan kina bu atar hakan a ka sin hakan kuma nan ba filin shirme da shiririta ba ne zaki iya jira a waje har zuwa lokacin da kika shirya fa an abin da ya kawoki. Esherh ta fara maganar ba tare da kalla inda Basma in take ba ta kuma are tana mai agowa tare yi mata wani duba tana jingina bayanta jikin Kujerar da take kai. Ke Esherh ba ro on ki nazo ba da har zakiyimin wannan kalamai zuwa nayi domin yi miki kashedi da babbar murya a kan ki rabu da mijina ko fita a harkarsa inda kuma ba haka ba hhhh to fa duk abin da ya biyo baya ki kuka da kanki! Basma ta fa a a tsawace tare da fizge handbag inta da ta aje ta juya da nufin barin Office Who are you and your fucking husband? Tambayar rainin hankalin da Esherh ta yi ma ta shi ya sa ta tsayawa cak! Sai kuma a wani irin fusace ta juya domin bata amsa daidai da tambayarta sai dai ganin Esherh tsaye dab da ita da batasan lokacin da hakan ya faru ba shi ne ya sa ba shiri gabanta ya yi mummunar bugawa sai ta kasa fa in abin da ta yi niyya. Daga mijin naki har ke idiot dake ban auke ku a bakin komai ba kuma wannan ya zama karo na farko kuma na arshe da zaki ara zuwarmin office da shashanci irin wannan domin na rantse kika ara to fa shafawa idanuna toka zan yi sannan na ha a ki da security su lallasa min ke idiot! Esherh ta are maganar tana fidda hannuwanta dake zube cikin trouser pocket nata sannan ta ari sa gaban madaidaicin Fridge zake office in ta bu e tare da ciro Holandiya sannan ta koma saman Sofa na office in ta zauna afa aya kan aya sannan ta fara kur ar abin ta hankali kwance. Zaki iya tafiya idan baki da sauran abin fa Esherh ta katse Basma da ta shiga Duniyar mamaki da kuma tsoro da fa in hakan bayan ta sauke bottle in a bakinta. Jiki a sanyaye kuma da an gudu-gudu Basma ta bar Office in cike da takaicin wannan cin mutunci da Esherh ta yi ma ta. Bayan fitar Basm girgiza kai kurum Esherh ta yi tana mamakin rashin ha uri da kuma kishin hauka na wasu matan, ita Allah ya gani ma Omer in ma baya gabanta sam sai dai wannan zuwan da Basma ta yi dama tsokiburutsunta sun saka taji wasan ya fara yi ma ta armashi zata so wasan ya ci gaba domin ganin yadda Basma zata yi. Mintuna ka an da faruwar hakan suka shiga meeting in ainihin lamarin shi ne ma'aikaciyar wancan Kamfanin ta kasance tsohuwar ma'aikaciya ce a kamfanin su Esherh in kuma tana daga cikin wa an da suka fitar da wannan design sai dai an koreta daga kamfanin ne sakamakon kamata hannu bibbiyu da a ka yi da karya dokar kamfani ta hanyar bada sirrinsu ga wani kamfanin daban shi ya sa a ka koreta ita kuma da ta tashi sai ta shiga wancan Kamfanin da ta sama dama shi ne ta basu design na kamfanin su Esherh a matsayin ita ta ira su kuma da basu san ainihin gaskiya ba sai suka fitar da sabuwar sar a da irin wannan design Shiru Esherh ta yi lokacin da suka kawo nan kowa ya san gaskiyar da ma'aikaciyar da kanta ta fa a ganin asirinta ya tonu. e wa shugabar ayan kamfanin da a
Chapter 6 · 0% Book details