← Book details Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 36

Sashe 36

Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yara ne su guda hudu suke wasa a falon uku daga ciki kamar yan uku domin girman su 蓷aya hatta da kayan jikin su kawai dai biyu a ciki mata ne 蓷aya kuma namiji gaba dayan su baza su wuce shekara biyar ba sai kuma yarinya karama a zaune a kujera batafi shekara biyu ba

Mace daya daga cikin yan ukun ce ta dau remote ta chanza Chennal da sauri na mijin ya sauka a kujerar yana karbar remote din bayan ya kai mata duka

Kuka tasa awajan ,daga ciki naji ana magana wata mata ce ta fito tana fa蓷in "gaskiya Khalifa bakajin magana sau nawa ina fadama banason saurin duka kuma ba na fadama Zuhra yayar ka ceba dan gidan ku ko dan kaga tsayin ku daya to ta baka wata uku

Sai da ta gama fa蓷an ta juyo sunnan na gane wace jamsy ce ta zama babbar mace da alama hutu da kwanciyar hankali sun zauna

Da gudu Khalifa yayi waje yana sa kuka akan fa蓷an da tayi masa kai ta girgiza tana fa蓷in zaka dawo ne kasame ni

Part din farko ya shiga yana kiran " mamy虏 wacce ya kira da mamy ce ta fito tana fa蓷in dan gidan mamy mai kuma ya faru ne irin wannan kiran haka Rufy ce ta zama wata hamshakiya kamar ba ita ba tayi 茩iba abinta

"Ummi ce ta ce wai Zuhra ta girme ni kuma dai dady yace nine babban Yaya
Dariya Rufy tayi domin kuwa tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki dama kullum sai anyi wannan maganar
"Eh kai ne babban yaya amma dai ka daina dukan su babban yaya baya duka kaji ,yanzu jeka wajan Didi kace Ina gaishe ta kaji twins sun fara kuka

Fita yayi daga part din ya nufi 蓷ayan ita kuma ta shiga 蓷aki wajan twins da suka fara kuka nono ta shiga basu

Da daddare kamar yadda aka saba waje 蓷aya ake cin abinci duk gidan har mazajan su yaran a ha蓷a musu sai kowa kuma ya zuba abinda yayi mai anayi ana hira da yake akwai wajan shan iska babba agidan dan haka da daddare duk nan suke zama cin abinci

Su Ibrahim yanzu an zama manyan magidan ta ga kuma uwa uba kudi an samu alhamdulilah rayuwa lafiya kalau ake yin ta kowa yana farin ciki tare da matar sa da kuma 拼a拼an Sa

Bayan an gama akai sallama kowa ya nufi part 蓷insa Zuhra ce 拼ar Rufy tace "mamy wajan finah 拼ar gidan Farida take nufi Ni dai zan kwana
Khalifa ne ya kallo ta to nima anan zan kwana

Ibrahim ne ya kalle shi yana girgiza kai kafin yace
"Ai babban yaya baya kwana cikin mata yanzu abinda za'ai kai da husna (yar gidan jamsy ta biyu) zaku kwana tare shike nan kaga an raba ko
Kai ya daga mai alamar ya yadda

Daga nan kowa ya wuce part din sa bayan anyi sallama da juna

Rufy ce zaune bakin gado tana shirya twins cikin kayan baccin su Ibrahim ya shigo

"Baby ayi maza maza a gama shirya su azo a shirya baban su shima
Dariya Rufy tayi tana fa蓷in "kai hubby yanzu da yaran ka uku ka girma ai

"Chabb lallai yariyar nan to aini ko Zuhra na aurar karshe kenan to wallahi bazan girma ba wajan matata
Dariya tayi tana kantar da twins sannan ta matsa kusa da shi tana fa蓷in

Nima mijina bana son ka girma awaje na nafison kayi ta zama a yaron ka kaji Ni kuma zan kula da kai yadda ya kamata

Bangaran Farida sai da ta yiwa finah da Zuhra addu'ar bacci sannan ta baro dakin su ta shiga nata lokacin hafiz yana zaune
"Au abban finah ai na zata kayi bacci yadda na dade dinnan

"Bacci fa kika ce ai jira nake kizo ki bani abin da蓷in nan naki ya 茩ara sa maganar yana tsare ta da ido

"Kai wasa kake dai ko yanda na zama jagwal dinnan salon kawai ka tsokano min nakuda ban shirya ba

"Haba dai karki karaya kadan zanyi insha Allahu ba abinda zai faru kuma ma ai dama idan ana harka nakudar tazo haihuwar tafi sauki
Daga haka ya samu yayi nasarar hade bakin su waje 蓷aya

Jamsy ce zaune bakin mudubi sai shafa hura take masu kamshin gaske gaba 蓷aya dakin ya dau kanshin Abdullahi dake danna waya ganin jan ran da take mai yayi yawa ya sa ya aje wayar cikin sanda yazo inda take sai ji kawai tayi yayi sama da ita yana
"Haba dan Allah sweetie sai jamin rai kike gaba 蓷aya kamshin humrar ki ta gama cika ni

ALHAMDULILAH

Anan na kawo karshen wannan littafin nawa ina fatan kun fahimci abinda nake so a fahimta aciki
Dan Allah wanda nayiwa ba dai dai ba ya yafe min dan Adam ajizi ne Ako da yaushe mu masu laifi ne

Inawa kowa fatan alkairi ,wadan da suka juri bibiya ta Ina GODIYA SOSAI ALLAH ya bar zumunci ya ha蓷a kowannnen mu da alkairin watan da yake tunkaro mu ameen
Chapter 36 · 0% Book details