← Book details Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 36

Sashe 21

Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To haka dai suka 茩ara sa wannan yinin suna tattana yadda za'a samu mafita sai dai a kwai abubuwa da yawa da Rufy take ganin baza ta iya ba
Da yamma tayi tare suka shiga kitchen sukayi tuwan semo da miyar ku蓳ewa,sannan matar hafiz tasa aka dafa shayi yasha kayan 茩amshi sabida garin da sanyi sanyi

***********Wunin yau gaba 蓷aya sai a hankula yayi aikin sabida tunanin da ya addabi 茩wa茩walwar sa zuciyar shi ce ta tanbaye shi "A ina jamsy tasan cewa Rufy ba budurwa bace?

Girgiza kai yayi alamar bai sani ba dan shi dai yasan bai gaya mata ba iyaka yace auren ha蓷i akai musu ba tare da suna san juna ba shike nan to amma a ina ta samo wannan maganar tabbas akwai wata a 茩asa
Da sauri ya tashi tsaye wajan jamsy zashi ya jiyo inda taji wannan labarin

Wayar ta ce tayi 茩ara dai dai sanda ta fito daga wanka 茩aran kiran ne yasa ta 茩ara so da sauri sabida mutum 蓷aya ne yake da wanann ringtone din da sauri ta 蓷aga

"Kizo mu hadu inda muka hadu jiya yanzu ina jiran ki
Iya abinda yace kenan ya kashe wayar

Da sauri ta fara shiryawa sabida karta 蓳atamai lokaci
Bayan ta gama ne ta fara yiwa wanda ke kwance kan gadon magana

"Alhaji nifa na shirya ka sallameni zan wuce ana jirana

Ku蓷i wanda ta kira da alhajin ya dakko ya bata zasu kai dubu hamsin ta kar蓳a tayi gaba dan burin ta taje taji kiran me Ibrahim yake mata

Lokacin ta ta 茩ara so harya tashi zai tafi dan ya gaji da jira gashi yana da aiki a office ya fito

Bako sallama haka ta zauna a wajan tana fa蓷in
"Sorry baby na barka kana jirana wanka nake ne lokacin

Okay kawai ya iya ce mata ya tsaya yana 茩are mata kallo jamsy ba mummuna bace sai dai tayi kama da wa蓷an da idon su ya bude ga bakinta yayi kamar tana san wani abu,ganin kamar zan shiga zargi kuma yasan ba kyau hakan yasa ya kawar da wannan tunanin ya fara mata magana

"Dama akan maganar da mukayi jiya ne tabbas nayi tunani abinda kika fa蓷a gaskiya ne sai dai kuma wani abu da ya bani mamaki taya akwai kikasan Rufaida ba budurwa bace waya fa蓷a miki ?
Ya jefa mata tanbayar yana tsare ta da ido

"A'a...ba kaine ba ka fa蓷amin lokacin da muka hadu da kai
Ta fa蓷a cike da alamun rashin gaskiya tare da ita

"Ni kuma jamsy gaskiya ki sake tunani dan banyi wannan maganar da ke ba kwata kwata sai dai idan wani wajan kika jiyo

Shiru tayi tana tunani
"Nashiga uku surutu na zai jawomin ya gano koni wacce amma bazan bar hakan ta faru ba dole na san mafita

"Kinyi shiru kin barni ina magana ni ka蓷ai a ina kikaji wannan maganar?
Ya sake jefa mata tanbaya

"Tunani nake sai dai kuma baby na kasa tunawa sai nake ganin kamar kaine ka fa蓷amin idan ba haka ba a ina zanji

"Kinga a rayuwa ta banason munafirci idan har kinaso ala茩a ta da ke ta dore to tabbas ki fito ki fa蓷amin gaskiyar inda kikaji wannan maganar
Daga haka ya tashi yabar wajan

Zama tayi ta zuba tagumi garin neman hanyar shiga tana neman ta fita yanzu me zata ce mai idan ya kuma tanbaya tabbas ya zama dole tasan abinyi kafin lokacin

***********
Sanda suka dawo gida sosai yadda hafiz da matar shi suka tari juna ya burge Rufy da Ibrahim sabida sun nuna iya wannan yinin sunyi kewar junan su

Wannan shine karon farko da Rufy ta ta蓳a kar蓳ar jakar Ibrahim bayan ya dawo, shima sabida matar hafiz ta mata nuni da hakan ne
Dan haka ta kar蓳e tana fa蓷in sannu da zuwa sai yaga abin wani iri sabida bai saba ba,hanyar 蓷akin shi tayi cike da fargaba domin wannan shine karon farko da zata shigar mai 蓷aki

Bayan ta dawo ne ta tarar matar hafiz ta zubawa mijin ta abinci sannan ta sa hannu sun fara ci suna hira

Zubawa Ibrahim Rufy tayi dan wannan shine karo na farko da ta fara zubamai abinci tashi ta so yi zata bar wajan matar hafiz tace

"A'a ina kuma zaki ke da kike ta cewa yunwa kike ji kisa hannu kici idan kun gama sai ku rakamu mu tafi karmu ta kure ango da amaryar sa
Ta 茩ara sa maganar tana dariya 茩asa 茩asa

"Da gaskiyar ki sweetie Dan da ganin abokin nan nawa kinsan lamarin sa ba sauki
Hafiz ya fa蓷a yana mai dariyar shakiyan ci

Gaba daya kunya ce ta rufe Rufy jin maganar da sukeyi duk sai tayi wata irin kunya ta kamata gashi hannun ta cikin kwano 蓷aya da Ibrahim duk sai ta jita a takure

"A'a amarya ya dai naji kinyi shiru ko duk cikin salon korar mune
Matar hafiz ta fa蓷a tana dariya

Rasa abin fa蓷a yasa Rufy cewa
"A'a kuyi zaman ku ba komai

To bayan sun gama cikin abincin ne Ibrahim ya tashi zai rakasu amma matar hafiz tace Rufy ta tawo suje tare mana daga nan ta ga gari
"Yawwa Ibrahim gobe zanje siyayya kaga zai muje tare da amarya sabida nasan itama baza ta rasa abinda zata siya ba koya kika ce
Ta fa蓷a tana kallon Rufy da kanta yake a 茩asa

"A'a gaskiya dai ko ba komai ai ta zaga garin Lagos ba kullum ace tana gida ba
Hafiz ya fa蓷a shima

"To shike nan Allah ya kaimu gobe sai kuje tare
Cewar Ibrahim dai dai lokacin da suka fito waje

Haka suka tafi suna hira duk da ba baki Rufy take sawa ba iya ka tayi murmushi kawai sabida gaba daya idan hafiz da matar shi sukayi wata maganar kunya suke sata ji su kuwa ko a jikin su harkar su kawai suke

Bayan sun rasasu sun dawo ne suna cikin tafi ba hira suke ba amma kasan cewar sun jero daga nesa sai kazata hira suke Chocolate din da ya ta蓳a siya mata ya gano irin ta dana haka yace jirani ina zuwa daga haka ya tsallaka titin wajan

Tun bayan rabuwar su da su hafiz jamsy ta hango su ita kuma suna tare da wani sabon Alhaji da suka hadu sosai ganin Ibrahim da Rufy ya bata mamaki kuma ya 蓳ata mata rai domin ba haka taso ganin su ba

Ganin ya barta awajan ne yasa ta tsaida su suma dan ganin ina zashi wajan mai Chocolate din da taga yaje ne ya bata mamaki kenan yasan abinda Rufy take so
"Kardai har sunma fara soyayya,ta tanbayi kanta
Da sauri ta girgiza kai tana fa蓷in ina hakan bazai taba yiwuwa ba wallahi ni kadai ce matar da ta dace Ibrahim yaso

馃崈馃崈 SECONDARY SCHOOL馃崈馃崈

(Love & romantic story)

Shalele ce馃拑

_____________Daga inda take tsaye taga Ibrahim ya mi茩a wa Rufaida ladar hannun sa sosai yaji zuciyar ta ta mata zafi dan haka ta ciro waya ta kira shi

Jin 茩arar shigowar kirane yasa shi ciro wayar daga aljihu ganin wadda ke kiran hakan yasa yaja tsaki ya katse kiran nata sannan ya mai da wayar aljihu
Duk abinda ke faruwa jamsy na kallo har tsakin da yayi mata sosai abin ya bata mamaki to me hakan yake nufi Ibrahim ya fara soyayya da Rufy kome

Lokacin da suka koma gida Rufy zata shiga daga tunawa da ledar da ya bata yasa ta koma da baya tana fa蓷in gashi ka manta baka kar蓳a ba
Ta fa蓷a tana mi茩amai ledar hannun ta

"Naki ne dan kuma bakyaso sai ki zubar
Daga haka ya shige 蓷akin sa

Da kallo Rufy ta bishi wannan mutum kwai ba茩in halin tsiya
Ta fa蓷a tana rakashi da harara

Sai da ta gama duk abinda zatai ta kwanta kenan sai duk abinda ya faru 蓷azu ya fara dawo mata yadda suka ci abinci kwano 蓷aya duk da ita batafi lauma hudu tayi ba amma duk sai taji wani abu da ban
Ganin wannan tunani zai 茩arfi a zuciyar tane yasa ta dakko ledar da ya bata ba tare da ya fa蓷a mata meye aciki ba
Dubawa tayi Chocolate ce kuma wadda take so sosai wani irin farin ciki ne taji ya kawo mata ziyara domin batayi zato ba sosai kyautar tashi ta burge ta

Fuska ta narkar alamar shagwa蓳a tana fa蓷in
"Ai bansan ita ka siyomin ba nake cewa mai ba茩in hali Please sorry
Duk wannan maganar tana yinta ne kamar yana gaban ta,ganin abin nata yana neman yin yawa ne yasa ta mari fuskar ta tana fa蓷in Rufy ki dawo hankalin ki mana wannan haukan fa

To wash gari kamar yadda Farida matar hafiz ta fa蓷a hakan ne ya kasan ce domin kuwa lokaci da hafiz zai fita tare suka tawo ya kawo ta gidan Ibrahim,lokacin ita Rufy tama manta sunyi wannan maganar dan tayi zatan wasa takeyi

Lokacin da Ibrahim ya fito da shirin fita ne ya samu hafiz da matar shi zaune suna hira sai Rufy dake gefe tana sa baki lokaci lokaci

"Yawwa ango muma fa zuwa anjima zamu shiga kasu ni da sister dan haka a cika mana aljihu koya kika ce 拼ar uwa
Ta 茩arasa maganar tana kallon Rufy da kanta yake sunkuye

Ita dai Rufy bata ce komai ba tana jinsu sunayi

"A'a gaskiya nifa banason yawo kuma dai kinsan bata son sanyi
Ibrahim ya fa蓷a duk dan kar Rufy ta fita

"A'a dan Allah karka mana haka tun jiya muka fa蓷a yanzu dai abinda zamuyi zamu dawo da wuri ko sis Dan Allah kiyi magana mana
Ta fa蓷a tana ta蓳a Rufy da kanta yake 茩asa

"Dan Allah ya..ya.. ka barmu muje
Wannan maganar ta yita ne cike da 茩in 茩inar dole ga farga ba ha蓷i da tsoro

Tsaya wa yayi yana kallon ta ganin tace mai yaya To a gidan uban wa ya zama ya'yan ta ko dai kalan dangi take ne

Hafiz da ya gaji da tsaiwa ne yace "dan Allah ka sallame ta mu tafi kafi kowa sanin muna da aiki yau din nan

Jin hafiz yasa baki ne yasa shi ciro kudi daga aljihu dubu sittin ne dan haka ya mi茩a musu yana fa蓷in
"Nasan dai duk abinda zaku siya sun isheku
Chapter 21 · 0% Book details