← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 38

Sashe 6

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Khausar dake ɗan lumshe idanu Didi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo cike da kulawa tace.
“Aleeyu ku shiga ciki yarinyar ta gaji da zaman motar nan ”.
Kai ta gyaɗa Tare da cewa.
“Toh”.
Sai kuma ya damƙe hannun Khausar cikin nasa tare da ɗan janyota jikinsa suka nufi Side ɗin sa.

Gaba Innayi tayi tana mai cewa.
“Didi, Lalla Khadijah Lalla Hafsat Bismillah”.
Kai suka gyaɗa tare da bin bayanta suka nufi ɗaya daga cikin Side ɗin.
Akuma dai-dai lokacin Ummi ta fito daga Side ɗin fuskarta ɗauke da farin ciki da mamakin ganinsu tace.
“Masha Allah sannunku da zuwa, sai yanzu kuka iso, da naji ku shiru-shiru har nake cewa barin tafi wata ƙil zaku kai dare”.
Ta ida maganar tare da rungumar Didi itama Didi rungumeta tayi tana cewa.
“Masha Allah fatan mun sameku lafiya”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da riƙo hannun Lalla Hafsat tace.
“Alhamdullah. Bismillah mu shiga daga ciki”.
Cike da farin ciki suka bi bayanta...

Abban Jameel kuwa shi yayi wa Abualeey, Waziri, Galadima, Baffan Zakariyya, Dr Jameel Zakariyya jagora zuwa Side ɗin da suka fito ko wanne yana ɗauke da 3bedroom manya,-manya wanda aka shirya su da kaya na alfarma da kawa ɗaya daga cikin ɗakunan Dr Jameel, Zakariyya da Ibraahim ne aciki.
Sai kuma na biyun Abualeey ne da Waziri, Sai kuma Baffan Zakariyya, Galadima.
Acan Side ɗin su Ummi kuwa Didi da Rahama ta nunawa ɗakin farko inda zasu zauna kana bedroom ɗin gaba ta kai Lalla Khadijah, Lalla Hafsat,da Niyna.
Sai da ko wannensu yayi wanka kana suka canza kaya zuwa mai ɗan nauyi amma ba can ba saboda yanayin sanyin garin kafin suka gabatar da sallolin suka ɗan huta tare da taɓa hira sai kuma suka fito Falo Ummi da kanta tayi musu iso zuwa dining.
Didi na murmushi ta shaƙi sanyayyar Iskar garin da kuma wanda bishiyoyi da flowers ɗin gidan ke kaɗawa tace.
“Kai Alhamdulillah Masha Allah weather garin nan akwai daɗi ”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Aikam sai dai akwai sanyi”.
Sai kuma tayi serving ɗin su da lifiyayyan abinci iri iri na alfarma da suka musu.
Akuma dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka shigo bayan sun fito daga ɓangaren su Abualeey Haiydar na bin Falon da kallo yace.
“Ummi ina Addah Khausy?”.
Ɗan Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Tana side ɗin Moddibo”.
Cikin sassarfa ya juya da niyyar fita sai kuma yayi saurin juyawa ya kalli Didi cikin girmama ya ɗan rusunar da kanshi yace.
“Ayyah Didi kuyi haƙuri na manta bamu gaisa ba ina yininku fatan kunzo lafiya?”.
Dariya tayi tare da faɗin.
“A' lafiya lau anyi kewar ƴar uwa ko?”.
Dariya yayi tare da kama hannun Bashir da yake gaida su daga nan suka ficewa kai tsaye Side ɗin Moddibo suka nufa.

Acan Side ɗin Mazan ma haka ya kasance Abban Jameel da kansa yagabatar musu da abinci na alfarma da girmamawa sosai Abualeey suka jinjina mutunci da karramawarsu...

Haiydar da Bashir kuwa tun daga kan step ɗin Side ɗin Moddibo suke ƙwalawa Khausar kira suna cewa.
“Addah Khausy! Addah Khausy!!, Addah, Khausy!!!”.
A kuma dai-dai lokacin Khausar da Moddibo ne tsaye Dining hannunsa na cikin nata cikin taushi ya ranƙofa kanta tare da sassauta murya yace.
“Me zaki ci?”.
Kanta ta langwaɓar tare da tsirawa jerin abincin dake dining ɗin ido lumshe idanunta tayi tare da fara buɗe womers ɗin cikin yanayin jin sanyi ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Ga nan tuwo miyan kuka kasa min kaɗan zanci ”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Masha Allah zauna toh bari na zuba miki”.
Da dan sauri ta juya jin Bashir da Haiydar na cewa Addah Khausy Addah Khausy hannunta dake cikin nasa ta janye ta juya cikin sassarfa ta nufi ƙofan anufinta tayi gudu.
Da wani irin sauri Moddibo ya riƙo tsintsiyar hannunta yace.
“Kiyi haƙuri Minha na tuba dan Allah kada kiyi gudu”.
Ɗan ware idanunta tayi tare da faɗin.
“Su Bashir da Haiydar ne fa”.
Kafin ta ƙarasa suka ƙara so cikin falon tare da rungumeta shima Bashir cikin sauri ya rungumeta ta gefen Haiydar.
Murmushi Moddibo yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji yana kallonsu da tattausan murmushi bisa kekkyawar fuskarsa.

Khausar kuwa kallon Bashir tayi tare da cewa.
„Bashir ina Asma'u?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ba tazo ba wai ita kunya Amarya baza ta zo ba”.
Dariya mai tauri ta sanya tare da faɗin.
“Don Allah yanzu baza tazo ba haka zata min kenan?”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Wallahi fa taƙi zuwa tun safe taƙi zuwa ayi shara da ita wai Ummi tayi haƙuri”.
Dariya Khausar ta sanya tace.
“Lallai dai kam”.
Haiydar kuma hannunshi yasa cikin nata.
Cikin mamaki ta kamo hannun tare da kallon faratunsa hararansa tayi tare da cewa.
“Me haka zaka wani tare farce kamar mace?”.
Cikin lingwaɓar da kai yace.
“Na gaza koyan yanke wa nefa, Mommy kuma tace in dai bazan koyaba bazata yanke minba”.
Murmushi tayi tare dasa hannunta ɗaya ta dungure ƙeyarsa tare da cewa.
“Shine daga isowata zaka haɗani da aikin yankewa”
Ta ƙareshe mgnar tana jawosu suka zauna bisa kujerun Dinnin table ɗin.
Moddibo kuwa a kujerar dake fuskantar Khausar ɗin ya zauna, yana maiyi mata wani arin amintaccen kallo ya fahimci akwai tsananin shaƙuwa da so tsakaninta da Haiydar duk da yawan faɗan da suke a da.
Anan sukaci abinci tare.
Kana sukayi ta hira kiran sallan Magrib ne yasa duk mazan sunka tafi masallaci.
Kana basu dawoba saida sukayi sallan Isha sannan suka dawo nan kuma suka sake dasa sabon hira.
Hakama Abban Jameel dasu Abualeey.
Suma su Didi da Ummi haka ta kasance a wurinsu.

Misalin sha ɗaya su Lamiɗo suka yiwa su Abualeey saida safe kana suka tafi.
Su kuma duk sukayi shirin bacci suka kwanta.

Ummi dake tare da Malam Ahmad ta nufi sashen Khausar tana faɗin.
“Bari in je in jawo su Haiydar dan na lura su yau in zasu samu a nan zasu kwana”.
Kai ya jinjina mata tare da jingina jikin motarsu ya tsaya jiran fitowarta.

Ummi na shiga ta kalli Haiydar dake zaune gefen Khausar tace.
“Ku tasa mu tafi”.
Da sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.
“Toh Ummi bari in ɗauko mayafina mu tafi”.
Juyawa Ummi tayi jin Moddibo na cewa.
“Ina zaki je?".
Idanunta ta narkar kana tace.
“Zanje gida mana”.
Yana tsuke fuska yace.
“Da Izinin wa?".
Murmushi Ummi tayi tare da kallon Haiydar da Bashir tace.
“Haiydar kuzo mu tafi dare yayi mu barsu su huta”.
Saurin kallon Ummi Khausar tayi tace.
“Ayyah Ummi dan Allah ku jirani ya za'a kuma ace bazan jeba don Allah kayi haƙuri”.
“Da Izinin wa?”.
Ya maimaita tambayar yana mai tsuke fuska.
Kamar za tayi kuka tace.
“Da Izinin ka mana”.
Kai tsaye yace.
“Toh ban bada Izini ba”.
Ummi kam hannun Haiydar da Bashir taja suka fice.

Sai da suka sauƙe Haiydar agida kafin suka wuce.

Haiydar na shiga Falon Momy ya shiga da sauri ya zauna gabanta kan lallausan Darduma da take bisa alamu shafi da witri tayi.
yayin da ta jingina kanta jikin kushin cike da matsanancin farin ciki yace.
“Momy".
Cikin tsira nasa ido ta gyara zamanta tare da cewa.
“Na'am”.
Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa tare da faɗin.
“Kin ga yanda Addah Khausy ta dawo kuwa Momy?”.
Kai Momy ta girgiza kana tace.
“A'a ya ta dawo?”.
Zama ya gyara yace.
“Wallahi idan kika ganta zakice Balarabiya ce Masha Allah Subhanallah, tayi wani irin fari mai masifar kyau farinta har wani ƙelli takeyi”.
Ɗan ware idanu Momy tayi tare da faɗin.
“Allah ko?”.
Kai ya gyaɗa yace.
“Wallahi fa”.
Daga nan suka cigaba da hira.

Acan ɓangaren su Moddibo kuwa cikin tura baki Khausar tace.
“Haka kawai ahanani zuwa gidan mu yanzu Fisabilillahi muna ƙasa ɗaya gari ɗaya ace bazan ga Momyna ba?”.
Kansa ya ɗaura bisa kafaɗarsa yace.
“Na isa? Ai ban isa in hana ki ganin Momyn kiba? waya isa ya raba uwa da ɗa? ban isa in ra Baki da Momy ba.
Kawai dai nima bana so ara bani da ɗana akusa dani ne shiyasa”.
Cunno baki tayi tana kallonsa cike da shagwaɓa hanci ya lakace mata kana ya cigaba da cewa.
“Kuma ina so ki huta nasan in kunje hira zaku tayi baza ki huta ba kiyi haƙuri ki kwanta kiyi bacci ki huta gobe da kaina zan kai ki muje mu gaida Momy”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Da sassafe”.
Kai ya gyaɗa cikin tabbatar wa yace.
“In sha Allah in dai mun karya”.
Lallausan murmushi ta sakar mishi tare da riƙe tafin hannunsa tace.
“Toh shikenan”.
Bedroom suka wuce sosai tsarin ɗakin yayi kyau komai yayi yanda ake buƙata kana agyare tsaf-tsaf sai tashin ƙamshin roomfteshner yake, zama tayi kan gadon tare da jingina kanta da jikin gadon.
Moddibo kuwa gefenta ya zauna yana ɗan matsa mata ƙafafun yace.
“Kinga tafiyar nan da akayi mai ɗan tsawo sai nake ga kamar ƙafarki ta kumbura”.
Idanunta dake lumshe ta ɗan buɗe ta kalli ƙafan sai kuma ta gyaɗa masa kai tace.
“Eh dama Ni haka nake in dai na ɗanyi tafiya mai tsawo amota Normal haka yake min, zuwa safiya zaka ga ya watse”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Kuma ahaka kike so ki tafi kije ki zauna ba kiyi bacci ba”.
Ya ƙare maganar yana jan yatsun ƙafar tata tare da ɗan mammatsa mata su, sassayan numfashi ta fesar tare da muskutawa, da sauri ya ɗan tallabota tare da gyara mata kwanciyar saboda ganin duk ta sake alamun bacci mai nauyi takeji.
Ahaka ya cigaba dayi mata massage suna hira jefi-jefi har bacci ya ɗauketa.
janyota jikinsa yayi ya haɗa hannunsa waje ɗaya ya tofa musu addu'a ajikinsa ya fara shafawa kana ya shafa mata.
Chapter 6 · 0% Book details