Sashe 20
Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya buɗe ƙofar ganin Khausar ce agaba yasa ya ɗan ja baya cikin sauri Khausar ta wuce cikin falon tare da cewa.
“Barka da safiya Dr”.
Fuskarsa ɗauke da ƙayataccen Murmushi yace.
“Barka dai Bestynmu”.
Sai kuma yayi saurin juyawa tare da rungume Moddibo cikin matsanancin farin ciki yace.
“Ka gama min komai Aminina kuma ɗan uwana ka bani abinda ban taɓa samun irinsa ba arayuwata ta duniya”.
Ya lumshe idanunsa yana tuna irin garar daya kwasa awajen Asma'u kana ya cigaba da faɗin.
“Dukk biye-biyen neman Matana ban taɓa samun gamsuwa, nutsuwa, da kwanciyar hankali ba kamar akan wannan ƙanwar taka kagama min komai”
Ɗan tsuke fuska Moddibo yayi kana yasa hannunsa na dama ya make ƙeyensa tare da rike ƙunnensa yace.
“Ka kuwa san abinda kake faɗa?,”.
Still fuska ɗauke da murmushi Dr Jameel ya gyaɗa masa kai tare da cewa.
“Na sani mana, nasan me nake faɗa kawai dai na rasa ta ya zan nuna farin cikina ne.
Ji nake kamar in kira Ummi in sa mata albarka saboda ta bani abu mafi daraja da daɗin samuwa arayuwar duniya”.
Zare idanu Moddibo yayi kana yace.
“Baka da hankali fa”.
Kai Dr Jameel ya gyaɗa yana lumshe idanunsa kana har zuwa lokacin fuskar na ɗauke da Murmushi yace.
“Sosai ma bani da hankali, Wallahi bani da ishesh-shen hankali saboda tun jiya da hankalina ya tafi cikin gajimare har yanzu bai dawo ba.
Ni kaɗai nasan irin daɗi da shaukin dana kasance”.
Da ɗan ƙarfi Moddibo ya matsa kunnensa wanda yasa Dr Jameel sakin ƙaramin ƙara.
Moddibo kuwa yana cigaba da matsa kunnensa yace.
“Shine ka azabtar min da ƙanwata da fitinar da baka kasheta ba na tsawon watanni ko?
shine yanzu dare ɗaya zaka sauke akanta ko?”.
Langwaɓar da kai Dr Jameel yayi tare da cewa.
“Ƙanwar taka ce tafi zuma daɗi baki ɗaya ta gigitani ta gigita min lissafi duk ta rikitani”.
Ƙeyensa Moddibo ya kuma makewa da karfi kana ya wuce cikin falon.
Da sauri Khausar da tuni tayi ciki, ta juya ta kallesu kana tace.
“Dr ina Asma'u take?”.
Da hannu ya nuna mata Corridor da bedroom ɗin su yake.
Da sassarfa ta wuce.
Moddibo kuwa zama yayi akan kujeran kana Dr Jameel ya zauna gefensa.
Asma'u kuwa cikin yanayin baccin daya fara ɗibarta ta fara jiyo sautin muryan Khausar cikin sauri ta yunƙura da niyyar tashi.
Da sauri Khausar ta tura ƙofa ta shiga Asma'u kuwa da wani irin sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta zauna tare da sakin ƙara tana yarfe hannunta.
Cikin sauri Khausar ta matsa ta zauna kusa da ita kana ta riƙe hannunta tare da cewa.
”Allah sarki Asmeeyn Ummi an girma”.
Harara Asma'u ta galla mata da kumburarrun idanunta tace.
“Wani an girma?,An dai zalinceni!, Kawai ai wannan zalincine ba girma ba”.
Murmushi Khausar tayi wanda ya bayyanar da hoƙoranta tace.
“Kema kiji abinda ake ji, kiji abinda ko wacce ƴa mace take ji fatan mu dai Ubangiji Allah yayiwa iyayenmu albarka ya kuma saka musu da mafi kyawun sakamako da tarbiyyan da suka bamu Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya a gidajen aurenmu”.
Cikin shesh-sheƙa Asma'u tace.
“Ameen ya Allah amma Ni dai wallahi tare zamu tafi”.
Zare idanu Khausar tayi tare da cewa.
“Tare zamu tafi?,Na isa? A,a ni kam ba isa in ɗauke wa Dr Mata ba”.
Ɗan hararanta Asma'u tayi kana tace.
“Idan ke baki isa ba Yah Moddibo ya isa?”.
Sai kuma ta fara yunkurin miƙewa tana cewa.
“Ina Yah Moddibo?”.
Ganin yanda take ciccije bakinta yasa Khausar faɗin.
“Ki zauna mana bakya jin zafi ne”.
Tana goge hawayen fuskarta tace.
“Ai nasha magunguna na fara jin yana raguwa sosai yanzu”.
Kai Khausar ta gyada tare da cewa.
“Toh yanzu ina zaki je”.
Tana cije gefen lip inta na ƙasa tace
“Zanje wajen Yah Moddibo”.
Dariya Khausar ta sanya tare da faɗin.
“Iyeee wai ke bakya jin kunya ne?”
Hararanta Asma'u tayi kana tace
“Eh ɗin bana ji,Ke lokacin da aka miki kunya kika ji?,Ina gaban su Ummi kika je kika rinka Zuba taɓara son ranki”.
Dariya Khausar ta sake fashewa dashi ganin yanda Asma'u ke wani ciccije baki alamar har yanzu bata gama warware ba tace.
“Eh amma ai agaban mata nayi ba Maza ba”.
Shiru Asma'u tayi kana ta fara ƙoƙarin miƙewa har ta mike ta fara tafiya miƙewa Khausar tayi tabi bayanta tare da riƙe hannunta ahaka suka fito falon kallonsu Moddibo yayi ganin yanda Asma'u ke tafiyar yasa ya sunkuyar da kansa ƙasa ya kalli gefe tare da cewa.
“Asmeeyn Ummi kin fito?,”.
Cikin da shashshiyar muryanta tace.
“Eh Yah Moddibo ”.
Akuma dai-dai lokacin suka ƙarasa cikin falon zama sukayi akan 2sitter ahankali Asma'u ta zame ta kwanta kana ta ɗaura kanta akan cinyar Khausar.
Ahankali Khausar ta gyara zamanta kana ta tallafo kanta.
Moddibo kuwa ba tare da ta kuma sallonta yace.
“Asmeey zaki danne Baby fa”.
Murmushi Asma'u tayi duk da yanayin da take ciki saboda ya bata dariya ta lura Yah Moddibo yana masifar tattalin cikin nan juyawa Asma'u tayi ta kalli tudun cikin Khausar hannunta na dama tasa kan kitchen tare da cewa.
“Baby kayi haƙuri nima yau ina buƙatar cinyar Mamynka”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Yama isa tun kafin ya fito,ai tare ya ganmu ma”.
Ahankali Moddibo ya shafa sajensa yace.
“Adai barshi kar ta kura mishi”.
Dr Jameel dake Murmushi ya kalli Moddibo yace.
“Iyeee komai yaya dai yau zai bari ayi tattalin Umminsa”.
Murmushi suka baki ɗaya kafin Moddibo ya kalli Asma'u yace.
“Ya jikin?”.
Asanyaye tace.
“Da sauƙi Yah Moddibo ”.
Kallonsa ya mayar kan Dr Jameel tare da cewa.
“Ya baki magunguna ko? Kuma kinci abinci?”
Kai ta girgiza tana ɗan lumshe Idanunta tace.
“A'a banci ba”.
Shiru yayi kafin yace.
“Toh yanzu me zaki ci insa akawo Miki daga gida?.
Cikin sauƙe numfashi Khausar tace.
“A'a bari in shiga kitchen in girka mata”.
Da sauri Moddibo ya girgiza kai tare da faɗin.
“A'a bana so”.
Kai ta langwaɓar tare da cewa.
“Yah Mu'allim zan iya mana agida ma ina shiga inyi girki ”
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Toh shikenan”.
Asma'u kuwa miƙewa tayi tare da cewa.
“Toh mu tafi kitchen ɗin tare”
Kai Khausar ta girgiza tare da cewa.
“A'a ke kam ki wuce bedroom ki kwanta naga kamar bacci kike ji”.
“A'a muje dai”.
Cewar Asma'u tana lumshe Idanunta.
Numfashi Khausar ta fesar tare da kallon yanda take lumshe idanu tace
.“A'a ke dai kije kiyi baccin”.
Ahankali tace.
“Toh”.
Hannunta Khausar ta riƙe suka wuce bedroom ɗin kwanciya Asma'u tayi kana Khausar ta zauna gefenta tace.
“Amma kinyi amfani da Ruwan ɗumi sosai?”.
Kai Asma'u ta gyada tare da cewa.
“Eh ya sassani kuma ya ban magunguna sannan yamin allurai kuma ya shafa min wani ma a wurin Alhamdulillah naji sauƙi sosai yanzu ɗazun fa ko numfashi nayi zafi nake ji kamar raina ake zarewa”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe kana tace.
“Toh ba komai yanzu dai bari na miki abinda zaki ɗan ci mai zan dafa Miki?”.
Idanunta ta juya tare da taune lips ɗin ta tace.
“Nikam ma bana jin yunwa”.
Cike da kulawa Khausar ta dafa kafaɗarta tace.
“A'a ki dai fadi me kike so adafa miki?”.
Rau-rau tayi da idanuna tare da cewa.
“Nifa bana jin kwaɗayin komai”.
Shiru Khausar tayi na tsawon minti ɗaya alamar tunani kafin ta mike tace.
“Bari dai naje kitchen in ga abinda zan Miki.
Ko dai in gasa Miki nama?
Dan nasan ki”.
Tana gyara kwanciyarta tace.
“Eh”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da wucewa kitchen.
Kallon Moddibo Dr Jameel yayi kana yace.
“Yanzu kusan 1month fa kenan da Khausar taje anti nytel ya kamata ace gobe ko jibi ku samu ta sake zuwa”.
Cike da gamsuwa Moddibo ya gyara zamansa yace.
“Eh nima dama gobe ko jibi nake so muje,dama tun bayan 2weeks ma naso muje toh ya kama bikin nanne da muka tafi amma in sha Allah gobe ma zan kawo ta”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh Allah ya kaimu”.
“Ameen”.
Ya amsa kana suka cigaba da hira...
A gefen Khausar kuwa cikin sauri sauri ta gasawa Asma'u nama mai ɗan romo-romo sai tashin ƙamshi yake kana ta dafa Cous-cous da yaji Carrot da grean beans daya ƙawata kyawunsa gashi yayi wasar-wasar abin sha'awa sai kuma tayi miyar hanta da yayi kyau sosai bayan ta gama ta zuba a Warmer kasancewar duka ayyukane masu sauƙin yi ta ɗauki na Moddibo da Dr Jameel ta kai musu Falo kana ta koma ta ɗauki nasu ta wuce bedroom ɗin Asma'u.
Tana shiga ta samu Asma'u na bacci jin alamun tana jin yunwa yasa ta zauna a tsakiyar ɗakin kana ta zuba a plate ta fara ci.
Tana cikin ci ta ɗago kanta ta kalli Asma'u jin alamun Asma'u tayi motsi.
Asma'u kuwa cikin baccinta taji kamar sautin ƙaran cokali tare da yunwar daya murɗeta ne ta mike ta zauna.
Dan ɗan murmusu tayi sai kuma ta miƙe ta zauna.
Khausar dake kallonta tace.
“Ya dai”.
Cike da farin ciki ta shafa cinyoyinta kana tace.
“Zafin ya tafi fa”.
Ajiyar zuciya Khausar tayi tare da kai spoon ɗin bakinta tace.
“Haba dai”.
Cikin tabbatarwa ta gyada mata kai sai kuma ta sakin sanyayyar ajiyar zuciya tace.
“Wlh kuwa”.
Ta ƙare maganar tana gyara zamanta.
“Masha Allah magunguna sun kama aikinsu”.
Cewar Khausar na Murmushi.
Asma'u kam cikin jin daɗi tace.
“Wlh kam".
Warmer Khausar ta janyo tana ƙara musu abincin tace.
“Toh saƙƙo muci abinci”.
Kai ta gyada kana ahankali ta saƙƙo ta zauna suka fara cin abinci bayan sun gana Khausar tace.
“Akwai magungunan da zaki sha yanzu ne?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“A'a sai bayan Azahar zan sake shan wasu”.
Tana tattara plate ɗin waje ɗaya tace.
“Toh shikenan”. Daga nan sukaci gaba da hira.
Wunin ranan dai haka Khausar ta yini agidan Asma'u koda Moddibo yace su tafi cewa tayi yayi haƙuri sai bayan Sallar Isha'i yazo ɗaukar ta.